islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Tarbar watan ramalana


9800
Surantawa
Watan ramalana wata ne mai girma, cikinsa ne ake bude kifofin aljannu, kuma ake rufe kofofin wuta, wani irin wata ne da Allah ya fifita shi akan sauran watanni, cikinsa ne Allah yake wa mutane falala iri-iri domin ya bude musu kofofin fata da sa ran yanta su daga wuta.Allah yakan yanta wasu daga cikin bayinsa daga wuta , a kowane dare daga cikin dararen sa. Don haka ya dace ga kowane musulmi yayi kyakkyawan tanadi ga wannan wata mai alfarma kafin zuwansa, domin shi bakone mai daraja, baya zuwa sai so daya a shekara.

Manufofin huxubar

Kwaxaitar da mutane a kan su yi shirya zukatansu don tarbar watan Ramadan.

Kwaxaitarwa a bisa ribatar kwanakinsa masu falala.

Bayani a kan wasu daga falalolin azumi da hukunce-hukuncensa da fa’idojinsa.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma

Bayan haka:

Allah Ta’ala Yana cewa:

( شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآَنُ هُدًى لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَنْ كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ 185 ) [البقرة: 185]

.

(Watan Ramadan wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa a matsayin shiriya ga mutane da bayyanannun ayoyi daga shiriya, da mai rarrabewa tsakanin gaskiya da qarya, duk wanda azumi ya riske shi a halin zaman gida to ya azumce shi, wnda kuwa ya kasance mara lafiya ko a bisa tafiya, to ya rama a wasu kwanakin na daban, Allah yana nufin sauqi ne da ku ba ya nufin qunci da ku ba, sannan kuma domin ku cika adadin (kwanakin azumin), kuma ku girmama Allah a bisa shiriyar ku da ya yi, kuma tsammaninku za ku gode).

Ya wanda fakuwarsa ta tsawaita ga barin mu! Kwanakin sulhu sun gabato. Ya wanda asararsa ta dawwama! Haqiqa kwanakin kasuwanci mai riba sun gabato. Ya wanda bai ci riba ba a cikin wannan wata! To a cikin wane wata ne zai ci riba? Duk wanda bai kusanci Ubangijinsa a cikin wannan watan ba, to har abada ma ba zai kusance shi ba.

Ya ku mutane! Ku ji tsoron Allah Ta’ala, kuma ku gode masa a bisa ni’imomin da ya yi muku na lokutan alheir, da abin da ya ba ku na falaloli da karamomi. Ku girmama waxannan lokuta, ku ba su matsayinsu da aikta biyayya da ayyuka masu kusantarwa zuwa ga Allah, da nisantar savo da abubuwa masu jefa mutun a cikin hallaka. Domin ba a samar da waxannan lokuta ba sai domin kankare munanan ayyukanku, da qara inganta kyawawan ayyukanku, gami kuma da xaukaka darajojinku.

Ya ku bayin Allah! Haqiqa kun fuskanci wani wata mai girma, da yanayi mai cike da riba mai girma ga wanda Allah Ya datar da shi ga aikata aiki na qwarai. Kun fuskanci wtan Ramadana, wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa. Wata ne da ake ninka kyawawan ayyuka a cikinsa. Kuma ake girmama munanan ayyuka a cikinsa. Allah Ya sanya azumtar yininsa farilla ce daga rukunan musulunci, kuma tsayawa a dararensa nafila ce don kammala farillanku. Duk wanda ya azumce shi don ba da gaskiya da neman ladan Allah, Allah zai gafarta abin da ya gabata daga zunubansa. Wanda kuma ya tsaya darensa, yana mai imani da neman lada, Allah zai gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa. Wanda ya yi Umara a cikinsa, kamar wanda ya yi hajji ne. A ciki ne ake buxe qofofin aljanna, ayyukan biyayya kan yawaita daga ma’abota imani. Ana kulle qofofin wuta, sai savo ya yi qaranci daga ma’abota imani. Ana xaure shaixanu, ba za su sami damar isowa zuwa ga masu imani ba, irin yadda suke isa zuwa gare su a wasu lokutan.

Bukhari ya rawaito hadisi daga Abu Huraira, ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah ya ce, Allah ya ce, “Duk wani aikin xan-adam na shi ne, ban da azumi, domin shi nawa ne, kuma ni ne nake sakawa a kansa. Kuma azumi garkuwa ne, idan ranar azumin xayanku ta kasance, kada ya yi batsa, kada ya yi hayaniya, idan wani ya zage shi ko ya neme shi da faxa, to ya ce, ni ina azumi. Na rantse da wanda ran Muhammadu ke hannunsa, haqiqa rihin bakin mai azumi ya fi qamshi a wajen Allah fiye da qamshin almiski. Mai azumi yana da farin ciki biyu, da yake yinsu. Idan ya yi buxa-baki zai yi farin ciki da shan ruwansa, idan kuma ya gamu da Ubangijinsa, zai yi farin ciki da azuminsa”.

Ya ku mutane! Ku yi azumi domin ganin jinjirin watan azumi, kuma kada ku gabace shi da azumin rana xaya ko biyu. Domin Annabi (ﷺ) ya yi hani a kan haka, sai dai fa wanda ake bin sa azumin Ramadan da ya shuxe to ya rama shi. Ko kuma ya kasance bisa wata al’ada ta azumi, to kamar wanda yake azumin Litinin ko Alhamis, ko azumin fararen kwanaki (Ranakun 13, 14, 15 na kowa ne wata) sai suka kuvuce masa, to wannan babu laifi idan ya azumce su kafin Ramadan da kwana xaya ko biyu.

Kada ku azumci ranar da ake kokwanton ta. Wato ran ashirin da ga Sha’aban, idan a wannan daren an sami abin da zai hana ganin jinjirin wata na hadari ko duhu ko makamantansu. Ya zo a cikin Sahihil Bukhari, daga hadisin Abdullahi xan Amru (R.A), cewa Annabi (ﷺ) ya ce, “Kada ku yi azumi har sai kun gan shi, idan an muku lullumi, to ku cika lissafin talatin.”

Hakanan ya ruwaito daga Abu Huraira daga Annabi S.A.W, ya ce “Idan ya vuya a gare ku, to ku cika lissafin Sha’aban talatin.” Kuma Ammar bin Yasir ya ce: ” Duk wanda ya azumci ranar da ake kokwanto a cikinta to, haqiqa ya savi Baban Qasim (ﷺ)”

Duk wanda ya ga jinjirin wata to, ya sanar da shugaba, kada ya voye. Idan aka sanar a rediyo cewa an ga wata, to ku yi azumi. Idan kuma aka sanar cewa an ga watan Shawwal to ku sauke. Domin sanarwar shuwagabanni kamar hukunci ne a kan hakan.

Ya ku bayin Allah! Abu ne sananne ga kowane musulmi cewa, azumin Ramadan xaya ne daga cikin rukunan musulunci da Allah ya wajabta shi a bisa bayinsa. Saboda haka duk wanda ya musa wajabcinsa to shi kafiri ne. Domin ya qaryata Allah da Manzonsa da haxuwar Musulmi. Allah Ta’ala ya ce:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ 183 ) [البقرة: 183]

(Ya ku waxanda suka yi imani, an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabatawa waxanda suka gabace ku, lalle za ku samu taqawa).

Kuma ya ce:

( شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآَنُ هُدًى لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَنْ كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ) [البقرة: 185] .

(Watan Ramadana wanda a cikinsa aka saukar da Alqur’ani domin shiriya ga mutane da bayyanannun ayoyi daga shiriya, kuma mai rarrabewa tsakanin qarya da gaskiya, duk wanda ya zama mazaunin gida a kwanakin watan to ya azumce shi…).

Don haka azumi wajibi ne a kan kowane musulmi, baligi, mai hankali, mai iko, mazaunin gida, namiji ne ko macen da ba ta jinin haila, ko na biqi (a lokacin) azumin. Ba ya wajaba a kan kafiri, amma da zarar ya musulunta a tsakiyar rana to ya kame bakinsa a ragowar yininsa, amma ba zai rama wannan ranar ba.

Azumi ba ya wajaba a kan yaron da bai balaga ba, sai dai idan azumin ba ya ba shi wahala, za a iya umartarsa da ya yi, don ya saba domin sahabbai (R.A) suna horar da yaransu a kan yin azumi, har ya kasance yaro yana kuka saboda yunwa sai su ba shi abin wasa ya shagala da shi har sai lokacin faxuwar rana ya yi.

Azumi ba ya wajaba a kan wanda ba shi da hankali, kamar mahaukaci, ko wawa, ko makamantansu, ko babba wanda yake sambatu, to wannan azumi bai hau kansa ba. Haka nan ba ciyarwa ko tsarki ko salla a kansa, domin ba shi da cikakken hankali, kamar yaro yake kafin ya fara tantance abubuwa. Azumi ba ya wajaba a kan wanda ya kasa kamar mai shekaru da yawa, wato tsoho, ko kuma marar lafiyar da ba a tsammanin warkewarsa, sai dai zai ciyar da miskinai a madadin azumin. Ga kowane miskini rubu’in Sa’i (mudu xaya). Amma an fi so idan ya haxa da mahaxin abincin, kamar nama da mai (ko kayan miyarsa).

Ya ku Musulmai, shi ko mara lafiya da ake sa-ran warkewarsa, idan azumin ba ya wahalar da shi, kuma ba ya cutar da shi, to ya wajaba ya yi azumin, domin ba shi da uzuri. Idan kuwa azumin yana wahalar da shi amma ba ya cutar da shi, to zai sha, kuma an karhanta masa azumin. Idan kuma azumin yana cutar da shi to haramun ne ya yi azumin. Duk kuma sanda ya warke daga cutarsa to ya rama abin da ya sha. Idan ya mutu kafin ya warke babu komai a kansa.

Mace mai ciki wadda azumi yake yi mata wahala saboda rauninta ko nauyin cikinta, ya halatta ta sha, sannan ta rama idan ta samu sarari kafin ta haihu ko bayan ta samu tsarki daga jinin nifasi. Mai shayarwa ko nononta kan yi qaranci saboda yin azumin, kuma wannan qarancin zai cutar da shayarwar, to ya halatta ta sha sannan ta rama a lokutan da babu wahala ko tawaya (a nonon nata) a cikinsu. Amma matafiyi idan ya yi nufin dabara ne kawai don ya sha azumi, to shan azuminsa haramun ne a kansa, ya wajaba ya yi azumi.

Idan kuwa ba nufi ko dabarar shan azumi ba ne ya sa shi yin tafiyar, to yana da zavi, ko dai ya yi azumi ko kuma ya sha, sai ya rama adadin kwanakin da ya sha, amma an fi son ya aikata abin da ya fi yi masa sauqi.

Idan yin azumin ya yi daidai da rashin yin (a wajen wahala ko sauqi) to an fi son ya yi azumin domin shi ne aikin Annabi (ﷺ), kuma domin kuwa shi ya fi gaggawa a wajen sauke nauyin da ke kansa. Kuma galibi ya fi ramuwar sauqi. Idan kuwa azumin zai yi masa wahala saboda tafiyarsa, to an karhanta masa yin azumin. Idan kuwa wahalar ta tsananta, to haramun ne ya yi azumi, domin Annabi (ﷺ) ya fita a shekara buxe Makka, zuwa Makka a cikin Ramadana, sai ya yi azumi, sai aka ce masa haqiqa azumi ya wahalar da mutane, suna jiran abin da ka aikata. Take kawai sai ya yi umarni aka kawo masa kofin ruwa, bayan La’asar, sai ya xaga shi har sai da mutane suka gani, sannan ya sha, sai aka ce masa bayan haka, ai wasu mutane sun ci gaba da azumi, sai ya ce, "waxannan su ne masu savo".

Babu bambanci a tsakanin matafiyin da tafiyar ta bijiro masa don wata buqata, ko kuma matafiyin da tafiyar tasa mai maimaituwa ce a yawan lokuta. Irin waxannan sun haxar da ‘yan tasi, ko kuma direbobin manyan motoci, domin su duk sanda suka fita daga garinsu sun zama matafiya. Abin da ya halatta ga sauran matafiya ya halatta a gare su na daga Ramadana, da qasarun salla mai raka’a huxu, da haxawa a tsakanin sallar Azahar da La’asar, da tsakanin Magariba da Isha’i, a yayin buqatar hakan. Shan azumi shi ne mafifice a gare su, fiye da yin azumi. Idan shan shi ya fi sauqi a gare su, sai su rama shi a kwanakin sanyi. Domin masu mota suna da garin da suke zaune, da iyalin da suke komawa gare shi. Duk sanda suke a garinsu to suna zaman gida, duk kuwa sanda suka fita daga cikinsa, to matafiya ne, abin da matafiya suke da shi to su ma suna da shi, abin da ke kan matafiya yana kansu. Duk wanda ya yi tafiya a cikin yinin Ramadana yana azumi, mafifici ya cika azuminsa, idan ya wahala to ya sha sai ya rama. Tafiyar ba ta taqaita da wani lokaci ba. Duk wanda ya fita daga garinsa to shi matafiyi ne, har sai ya dawo garinsa, ko da ya zauna a lokaci mai tsawo a garin da ya je xin. Sai dai idan ya yi nufin ya samu damar shan azumi ta hanyar daxewar tasa. To a nan ya haramta ya sha azumi, kuma azumi ya wajaba a gare shi, domin farillolin Allah ba sa saraya domin dabarar mutum. Azumi ba ya wajaba a kan mace mai haila ko jinin biqi, kuma idan sun yi, to azumin nasu bai inganta ba. Sai dai idan sun yi tsarki kafin ketowar alfijir ko da da minti xaya ne, to a nan azumi ya wajaba a kansu kuma ya inganta in sun yi ko da ba su yi wanka ba sai bayan hudowar alfijir. Kuma ya lazimce su su rama kwanakin da suka sha.

Ya ku musulmai! Haqiqa Annabi (ﷺ) ya kwaxaitar a bisa tsayuwar dare a wannan wata ya ce: “Duk wanda ya tsaya a Ramadana yana mai imani, da kuma neman lada, to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.” Haka nan sallar Asham ko Tarawihi, tana daga qiyamu Ramadana. Ya kamata ku tsai da waxannan salloli ku kyautata su, ku tsaya tare da limaminku har sai ya idar, domin duk wanda ya tsaya tare da limaminsa har ya qare, to za a rubuta masa ladan tsayuwar dare cikakke, ko da kuwa ya yi barci.

Ya wajaba, limamai su ji tsoron Allah a wannan Asham xin. Su kula da waxanda suke binsu sallah, su kyautata sallar gare su, su tsai da ita, da nutsuwa. Kada su yi sauri a cikinta sai su haramtawa kansu da waxanda suke binsu alheri, kuma kada su yi caccaken kurciya, ba sa nutsuwa a cikin ruku’inta, da sujjadarta, da zamanta da tsayuwa bayan ruku’i. Ya wajaba ga limamai, kada xayansu ya fita daga masallaci kafin mutane ko ya yawaita sallamomi ba tare da kyautata salla ba. Domin Allah Ta’ala yana cewa:

( لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ) [الملك: 2] .

“Domin ya jarraba ku wane ne ya fi kyautata aiki a cikinku.”

Bai ce, wane ne ya fi sarin gamawa, ko yawan aiki ba.

Haqiqa Annabinku wanda shi ne mafi kwaxayin mutane a bisa alheri, kuma abin koyi kyakkyawa ga wanda ya kasance yana qaunar rahamar Allah da ladan ranar lahira, ya kasance ba ya qari a bisa raka’a goma sha xaya, ba a Ramadana ba, ba kuma a wanisa ba. A cikin sahihi Muslim daga Ibn Abbas R.A, ya ce, Annbi (ﷺ) ya yi sallar asham da sahabbansa a Ramadana, sannan ya bar hakan, don tsoron kada a wajabta wa mutane, sai kuma su kasa.

Hadisi ya inganta daga Amirul Muminina Umar xan Khaxxab, cewa, shi ya umarci Ubayyu xan Ka’ab da Tamimud Dari, su yi salla da mutane raka’a goma sha biyu. wannan shi ne adadin da Annabi (ﷺ) yake sallata. kuma Khalifa shiryayye Umar xan Khaxxabi, ya bi shi a cikinsa. Shi ne mafifincin adadin da ake sallar Asham da shi. Idan wani zai qara a kan haka don kwaxayin lada ba wai don gujewa sunna ba, bayan ta bayyana a gare shi, ba za a yi masa inkari ba. Don an rawaito haka daga sashin magabata. Abin da kawai za a masa inkari akai shi ne, saurin da ya wuce iyaka, irin wanda wasu limamai suke yi, su jawo wa kansu da na bayansu asarar alheri.

Allah Ya datar da ni da ku zuwa cin moriyar waxannan lokuta ta hanyar ayyukan biyayya kuma ya kare mu daga aikata munkarin ayyukan da munana. Ya shiryar da mu tafarkinsa madaidaici, ya nisantar da mu tafarkin Jahimu, ya sanya mu dage masu azumtar Ramadana, kuma mu kasance daga waxanda suke tsayuwa dararensa, suna masu imani da neman lada, lallai Shi Mai yawan kyauta ne, Mai baiwa.

Abin da zan faxa ke nan, ina neman gafarar Allah ga kaina da ku da ragowar Musulmai daga dukkan zunubai.

Godiya ta tabbata ga Allah, majivincin wanda ya ji tsoronsa. Duk wanda ya dogara a gare shi, to haqiqa zai isar masa. Wanda ya fake da shi, zai isar masa. Ina gode masa, ina shaidawa babu abin bautawa a gaskiya bisa cancanta sai Allah shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu, bawansa ne, kuma Manzonsa ne, kuma masoyinsa ne, kuma badaxayinsa ne. Allah Ya yi daxin tsira da albarka a gare shi, da alayensa, da sahabbansa da wanda ya yi kira da kiransa, ya shiryu da shiriyarsa.

Bayan haka: Ya ku bayin Allah! Akwai fa’idoji masu xinmbin yawa a cikin azumi. Daga cikinsu akwai:

Durqusar da zuciya. Domin yawan qoshi da abinci da biyan buqata na shawa’a yakan gadarwa zuciya girman kai da taqama da gafala.

killace zuciya don tunani da zikiri, domin biyan buqata ta sha’awa kan sanya zuciya ta qeqashe ta makance. Amma zama da yunwa na wani lokaci kan haskaka zuciya, ta zama mai taushi, gami da gusar da qeqashewarta, ta zama killatacciya da tunani da zikirin Ubangiji.

Mawadaci yakan tuna irin ni’imar da Allah ya yi masa, ta hanyar da haka, zai tuna wanda shi kwata-kwata ma ba ya da komai. Wannan zai janyo masa godewa ni’imar Allah da wadatar da ya yi masa. Kuma zai sanya shi ya jiqan xan uwansa mabuqaci, ya taimaka masa da abin da ya sauwaqa.

Azumi kan quntata magudanar jini, waxanda su ne magudanar shaixan a jikin xan’adam, domin shaixan yana gudana a jikin xan’adam a magudanar jini, sai azumi ya kwantar da wasi-wasin shaixan da karya tunzurin sha’awa da fushi.

Kusanci zuwa ga Allah ba ya cika ta hanyar barin abin da aka halatta, Sai bayan mutum ya bar abin da Allah ya haramta a kowane lokaci, kamar qarya da azalunci da ta’addanci a kan mutane da cin dukiyoyinsu da mutuncinsu. Don haka Annabi (ﷺ) ya ce, “Duk wanda bai bar faxin zur, da aiki da shi ba, to Allah ba ya buqatarr ya bar abincinsa da abin shansa.

Wani daga cikin magabata yana cewa: “idan ka yi azumi to jinka da ganinka da harshenka duk su yi azumi daga qarya da haram, ka bar cutar maqoci. Ya zama kana da nutsuwa a yinin azumin naka. Kada ka sanya ranar azuminka, da ranar da baka azumi, daidai wa daida, ta wajen rashin kamewa".

Magabata sun kasance idan suna azumi, sai su zauna a masallatai su ce; “Muna kare azuminmu ne ba za ma cin naman wani ba.”

Bayin Allah masu azumi suna kasu zuwa nau’i biyu.

Na Farko: Wanda ya bar abincinsa da abin shasa da sha’awarsa saboda Allah Ta’ala, yana fatan aljanna. To wannan yana ciniki ne da Allah, kuma ma’aikacinsa ne. Shi kuwa Allah, ba ya tavar da ladan wanda ya kyautata aiki. Wannan mai azumi za a ba shi abin da ya so a cikin aljanna na abinci da abin sha, da mata. Allah Ta’ala ya ce:

( كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا أَسْلَفْتُمْ فِي الْأَيَّامِ الْخَالِيَةِ 24 ) [الحاقة: 24]

(Ku ci ku sha, kuna masu farin ciki, saboda abin da abin da kuka gabatar a kwanakin da suka wuce).

Mujahid da waninsa sun ce, wannan aya a kan masu azumi ta sauka.

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Annabi (ﷺ), ya ce: “Lallai a cikin aljanna akwai wata qofa da ake ce mata Rayyan. Masu azumi ne kawai za su shiga ta cikinta, babu mai shiga cikinta banda su.” A wata ruwayar kuma, “Wanda ya shiga zai sha abin shan da ba zai yi qishi ba har abada.”

Nau’i na biyu daga masu azumi, waxanda suke azumin gabarin duk wanda ba Allah. Sai xayansu ya kiyaye kansa da abin da kan ya qunsa, ya kiyaye cikinsa da abin da cikin ya tattara, ya riqa tuna mutuwa da ruvewa a qabari, ya nufi lahira da aikinsa, ya bar duk wani qale-qale na duniya. To wannan idin shi ne ranar gamuwa da Ubangijinsa, kuma farin cikinsa da gamuwa ne da shi:

( مَنْ كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ اللَّهِ فَإِنَّ أَجَلَ اللَّهِ لَآَتٍ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ 5 ) [العنكبوت: 5]

(Wanda ya kasance yana burin gamuwa da Allah to haqiqi ajalinsa (da Allah Ya sanya) mai zuwa ne, kuma shi mai ji ne mai gani).

Ya ku bayin Allah! Haqiqa wata azumi yana da kevance-kevancensa saboda Alqur’ani, kamar yadda Allah Ta’ala Ya faxa:

( شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآَنُ ) [البقرة: 185]

“Watan Ramadana wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa.”

Haka nan xan Abbas ya ce: “Haqiqa an saukar da shi jimilla guda daga Lauhil Mahfuz zuwa Baitul Izzah a daren Lailatul Qadari, shaidar haka, faxin Allah Ta’ala:

( إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ 1 ) [القدر: 1]

“Haqiqa mun saukar da shi a daren Lailatul Qadri”.

Zuhri ya kasance idan Ramadana ya shigo sai ya ce, “Ramadan wata ne kawai na karanta Alqur’ani da ciyar da abinci.”

Ibnul Hakam ya ce: “Maliku y kasance idan Ramadana ya shiga yana qauracewa karantun hadisi, da zama da xaliban ilimi. Ya mai da hankalinsa a kan karantun Alqur’ani daga Mus’hafi.”

Hakan nan ya ku bayin Allah, wannan watan horarwa ne a kan ciyarwa da yawan kyauta, domin ya zo a cikin Bukhari da Muslim daga xan Abbas Allah ya yarda da shi ya ce: Annabi (ﷺ), ya kasance mafi kyautar mutane da alheri. Kuma lokacin da ya fi kyauta shi ne da Ramadana, yayin da Jibrilu ya gamu da shi. Jibrilu ya kasance yana gamuwa da shi a kowane Ramadana. Sai ya yi karatun Alqur’ani tare da shi. Lallai Manzon Allah (ﷺ) ya fi sakakkiyar iska kyauta, yayin da Jibrilu yake gamuwa da shi.

Hikimar yawan kyautarsa a watan Ramadan ta haxa da:

Darajar lokacin da ninka ladan aiki a cikinsa, domin aiki yana qara daraja da darajar lokaci, ko guri ,ko don darajar ma’aikin da taqawarsa.

Haka nan akwai taimakawa masu azumi masu asham a cikinsu da maus zikiri a bisa xa'arsa. Sai mai taimaka musu ya cancanci ladansu, kamar yadda wanda ya shirya mayaqi yake da ladan yin yaqi, kuma wanda ya tsaya da kulawa da iyalinsa bayan tafiyarsa, yake da ladan yaqi.

Sannan haxa azumi da yana daga abin da ke wajabta aljanna. Ya zo a cikin Sahihi Muslim daga Abu Huraira, daga Annabi (ﷺ) cewa, “Waye a cikinku ya wayi gari yana azumi?” Sai Sayyidina Abubakar ya ce “Ni ne”. Ya ce waye a cikinku ya raka jana’iza? Abubakar ya ce, "Ni ne". Waye a cikinku ya yi sadaka? Ya ce, "Ni ne". Ya qara cewa wanene a cikinku ya gaida mara lafiya? Sai Abubakar ya ce, “Ni ne”. Sai Manzon ya ce, "Waxannan abubuwan ba su tava haxuwa ga mutum xaya ba face ya shiga aljanna.”

Daga ciki azumi ba makawa a samu wani tasgaro ko tawaya a cikinsa, ita ko sadaka tana xora abin da ya shiga cikinsa na tawaya da tasgaro don haka, zakkar Fid-da-kai, ta wajaba a qarshen Ramadana domin tsarkake mai azumi daga yasasshiyar magana da batsa.

Allah Ka karvi azuminmu da tsayuwar darenmu.

Allah ka gafartawa rayayyunmu da matattunmu, da qaraminmu da babbanmu, da namijinmu da macenmu, da mahalarcinmu da mafakinmu. Allah Ka yi salati da sallama a bisa Annabi Muhammadu, da alayensa da sahabbansa, ka yi sallama, sallama mai yawa.