islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Jan- Kunne Kan Bokaye Da Matsafa


10319
Surantawa
Yana daga cikin abin da aka jarrabi mutane da yawa da shi a yau, maza da mata, manya da qanana, sai wanda Allah ya kuvutar da su,shine zuwa wajen matsafa da bokaye da ‘yan duba da ‘yan tsibbu, don neman taimako a wajensu, don sanin abin da zai zo nan gaba, wanda wannan ba karamar halaka bace mai tabarwa duniya da lahira.

Manufofin huxubar

Haxa zukatan Muslumai da Ubangijinsu.

Bayanin hukuncin tsafi da bokanci a musulunci.

Jan-kunne game da zuwa wajen bokaye da matsafa da ‘yan duba.

Bayan irin haxarinsu a cikin al’umma.

Umarni da ruqo da sababai na shari’a.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Yana daga cikin abin da aka jarrabi mutane da yawa da shi a yau, maza da mata, manya da qanana, sai wanda Allah ya kuvutar da su, ko, zuwa wajen matsafa da bokaye da ‘yan duba da ‘yan tsibbu, don neman taimako a wajensu, don sanin abin da zai zo nan gaba. Su kuwa waxannan bokaye da ‘yan tsibbu, sai su riqa yin qarya ga mutane, suna cin dukiyoyinsu a banza, kuma suna kare su daga bin tafarkin Allah. Allah ya kiyashe mu! Za ka ga wani gwamna ko basarake, zuciyarsa tana rataye da wani boka ko xan tsibbu, ba abin da zai iya aikatawa, sai abin da ya nuna masa ya aikata, ko da wannan abin ya sava wa addinin Allah. Yana ji a cikin zuciyarsa cewa ya samu mulki ne ta hanyar wannan bokan, kuma bokan zai iya qwace mulkin sanda ya so. Ya manta da fa (وَقُلِ اعْمَلُوا فَسَيَرَى اللَّهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالْمُؤْمِنُونَ وَسَتُرَدُّونَ إِلَى عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ105) [التوبة: 105]

(Ka ce, «Ya Ubangiji! Kai ne mamallakin mulki, kana bayar da mulki ga wanda ka so, kuma kana kwace mulki daga hannun wanda ka so, ka xaukaka wanda ka so, kuma kana qasqantar da wanda ka so, alheri gabaxaya yana hannunka. Lallai kai mai iko ne a kan komai).

Ka ga wani kuma xan kasuwa ne, ba zai saya, ko ya sayar ba, sai da shawarar bokansa, ko xan tsibbunsa, wanda zuciyarsa take rataye da shi. Ka ga yana aikata abin da bokansa ya gaya masa, komai muni da qazantar da take cikin haka. Ko kuma, a’a, mace ce da take so ta mallake mijinta, ya zamo ba shi da katavus, ballantana ya yi wani abu bisa zavinsa, sai ta je wajen lalatacce, qazamin xan tsibbu, tana neman ya taimake ta bisa muradinta. Wannan fa shi ne halinmu, sai wanda Allah ya kare.

Haqiqa Allah ya bayyana cewa, koyan tsafi da tsibbu, kafirci ne. Allah ya ce,

(وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ102) [البقرة: ١٠٢].

(Ba sa koya wa kowa, har sai sun ce da shi, “Mu fa fitina ne, kada ka kafirta).

Kuma Allah ya ce,

(وَلَا يُفْلِحُ السَّاحِرُ حَيْثُ أَتَى69) [طه: ٦٩].

(Kuma mai sihiri ba zai rabauta ba, ko ta ina ya zo).

Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa.” Sai aka ce, “Waxanne ne, ya Ma’aikin Allah?” Sai ya ce, “Haxa Allah da wani, da tsafi, da kisan kan da Allah ya haramta, sai da gaskiya, da cin dukiyar maraya, da cin riba, da tserewa daga fagen yaqi, da yin qazafi ga tsararrun mata, gafalallu, muminai.” [Bukhari da Muslim].

An karvo daga A’isha (RA) ta ce, wasu mutane sun tambayi Manzon Allah (ﷺ) a kan bokaye. Sai ya ce, “Su ba komai ba ne.” Sai suka ce, “Ya Ma’aikin Allah! Suna ba mu labari wani lokaci, na wani abu, sai ya zamo gaskiya.” Sai ya ce, “Wannan kalma ce ta gaskiya, wadda aljani yake wabto ta, sai ya raxa wa mai jivintarsa, sai su kuma bokaye su gauraya qarya guda xari da ita.” [Bukhari ya rawaito shi].

Kuma Manzon Allah (ﷺ) ya yi bara’a daga wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci, ko aka yi masa bokanci, kamar yadda Imran ibn Husain ya rawaito. Ya ce, “Wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ba ya tare da mu; ko ya yi bokanci, ko aka yi masa bokanci, ko ya yi tsafi, ko aka yi masa tsafi. Duk wanda ya je wajen boka, ya gaskata shi da abin da yake faxa, haqiqa ya kafirta daga abin da aka saukar wa Muhammad.” [Bazzar ya rawaito shi, da salsala ingantacciyya].

Hukuncin mai tsafi da xan tsibbu, shi ne a fille musu kai da takobi, kamar yadda wasu daga cikin sahabban Manzon Allah (ﷺ) suka yi.

Ya ku musulmai! Ku sani, illar da waxannan fasiqai, bokaye da ‘yan tsibbu suke yi a cikin al’umma, tana da yawa. Daga ciki akwai abubuwa kamar haka:

Na farko, zare imani ga waxanda suke zuwa wajensu, waxanda suke gaskata su cikin abin da suka faxa, kamar yadda hadisi ya gabata a kan haka.

Na biyu, yawaita kisa da yaxa shi a cikin al’umma. Duk abin da muke gani, ko muke ji na vatan wane ko wance, ko ganin qaburbura a tone, ko ganin wasu sassan xan Adam, ana sayar da su, duk wannan sakamakon aikin ‘matsafa ne da bokaye, waxanda suke umartar mabiyansu da waxannan abubuwa.

Na uku, yaxa neman mata da fajirci a tsakanin mutane. Sau da yawa boka yakan sadu da mace, kafin ya yi mata aikin da ta zo nema. Ta sanadiyyar haka, ya lalata wa mijinta ita, kuma ya buxe mata qofar varna da fasadi a bayan qasa.

Na huxu, cin dukiyar mutane a banza. Saboda duk wani abu da boka ko xan tsibbu yake karva, a maimakon aikinsa da tsafinsa, varna ne, kuma datti ne. Abdullahi ibn Mas’ud ya rawaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya haramta kuxin kare da sadakin karuwa da ladan boka. [Bukhari ya fitar da shi].

Na biyar, vatar da mutane, da xora su a kan tafarkin fasiqanci, ta hanyar hana su bautar Allah: Wasu a hana su sallah, ko gabaxaya, ko wani yanki nata; wasu wankan janaba; wasu a hana su alheri, a umarce su da suk wani munkari.

Na shida, suna jawo azabar Allah da fushinsa ga al’ummah. Zainab bint Jahsh, Allah ya yarda da ita, ta ce, “Ya Ma’aikin Allah! Yanzu za a halakar da mu, a cikinmu akwai mutanen qwarai?” Ya ce, “Idan datti ya yi yawa!”[Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]. Shin akwai dattin da ya fi na matsafa?

Na bakwai, asarar duniya da lahira. Allah ya ce,

(وَلَا يُفْلِحُ السَّاحِرُ حَيْثُ أَتَى69) [طه: 69]

Ma’ana: “Matsafi ba zai tava rabauta ba, ta ko ina ya vullo.”.

Sheikhul Islam Ibn Taimiyya ya ce, “Zuzzurfan nazari ya tabbatar da cewa, ‘yan duba ba sa rabauta, duniya da lahira”. [Majmu’ul Fatawa].

Wannan kaxan kenan daga cikin illolin bokaye da ‘yan tsibbu a cikin al’umma. Saboda haka, ya zama wajibi a kan malamai da xalibai, su tsaya wajen bayanin illarsu a cikin al’umma, kuma ya zama wajibi a kan shugabanni, su tsayar musu da haddi, kamar yadda shari’a ta tanada, tun kafin ranar nadama ta zo.

Allah ya yi albarka gare ku, tare da ni, cikin Alqur’ani mai girma, ya kuma amfanar da ni, da ku, da abin da yake cikinsa na ayoyi da wa’azi, mai azanci. Lallai shi majivincin haka ne, kuma mai iko a kansa.

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabi (ﷺ).

Ya ku bayin Allah! Ya zama wajibi a kanmu gabaxaya, mu dogara ga Allah Ta’ala, shi ne mamallakin komai da komai. Duk abin da Allah ya bayar, ba mai hanawa, kuma duk abin da Allah ya hana, babu mai bayar da shi. Allah Ta’ala ya shar’anta mana roqon sa, da neman biyan buqatunmu a wajensa, kuma ya huwace mana hanyoyi da shari’a ta yarda da su, wanda za mu riqe su, don mu cimma burinmu. Daga cikinsu, akwai roqonsa, da neman biyan buqata a wajensa. Duk wanda ya roqi Allah da gaskiya da ikhlasi, lallai Allah ba zai tozarta aikinsa ba, Allah Ta’ala kusa yake, kuma mai amsa addu’a ne. Shi ne ya arzuta tsuntsu a sama, da kifi a cikin teku, kuma shi ne ya hore duk wani abu da muke gani a sararin duniya. Allah ya ce,

(اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَأَنْزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجَ بِهِ مِنَ الثَّمَرَاتِ رِزْقًا لَكُمْ وَسَخَّرَ لَكُمُ الْفُلْكَ لِتَجْرِيَ فِي الْبَحْرِ بِأَمْرِهِ وَسَخَّرَ لَكُمُ الْأَنْهَارَ32 وَسَخَّرَ لَكُمُ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ دَائِبَيْنِ وَسَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ33وَآَتَاكُمْ مِنْ كُلِّ مَا سَأَلْتُمُوهُ وَإِنْ تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللَّهِ لَا تُحْصُوهَا إِنَّ الْإِنْسَانَ لَظَلُومٌ كَفَّارٌ34) [إبراهيم: ٣٢ – ٣٤].

(Allah wanda ya halicci sama da qasa, kuma ya saukar da ruwa daga sama, sannan ya fitar da ‘ya’yan itatuwa da shi, don arziki gare ku, kuma ya hore jiragen ruwa, don su gudana a cikin teku, da izininsa, ya kuma hore muku qoramu. Kuma ya hore muku rana da wata masu gudu ba qaqqautawa, kuma ya hore muku dare da yini. Kuma ya ba ku daga duk abin da kuka roqe shi. Kuma idan za ku lissafa na’imar Allah to ba za ku iya qididdige ta ba. Lallai xan Adam mai yawan zaluntar kansa ne, mai yawan butulci).

Saboda haka, ya kai mai neman arziki, neme shi a wajen Allah, shi ne mai arzutawa, ma’abocin qarfi. Allah ya ce,

(فَابْتَغُوا عِنْدَ اللَّهِ الرِّزْقَ وَاعْبُدُوهُ وَاشْكُرُوا لَهُ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ17) [العنكبوت: 17]

(Ku nemi arziki a wajen Allah, kuma ku bauta masa, kuma ku gode masa, zuwa gare shi za ku koma).

Ya ke mai neman haihuwa! Kin manta da adu’ar Annabi Zakariyya, yayin da ya roqi Ubangijinsa? Ya ce,

( هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُ قَالَ رَبِّ هَبْ لِي مِنْ لَدُنْكَ ذُرِّيَّةً طَيِّبَةً إِنَّكَ سَمِيعُ الدُّعَاءِ 38 ) [آل عمران: 38]

(Ya Ubangiji! Ka ba ni zurriya ta gari daga gare ka, lallai kai mai jin adu’a ne).

Ya kai mai neman mulki, ko xaukaka, ko wani abu daban, neme shi wajen Allah, domin shi kusa yake, kuma yana amsa adu’ar bayi. Allah ya ce,

( وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذَا دَعَانِ فَلْيَسْتَجِيبُوا لِي وَلْيُؤْمِنُوا بِي لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ186 ) [البقرة: 186]

(Idan bayina suka tambaye ka game da ni, ka ce ni kusa nake, ina amsa adu’ar mai roqo, idan ya roqe ni. Su amsa kira na, kuma su yi imani da ni, ko sa shiriya).

Ya zama wajibi a kanmu, taron ‘yan uwa, mu yi taimakekeniya a tsakaninmu, don ceto al’umma daga sharrin waxannan fasiqai, fajirai. Kada mu ba su hayar gida ko xaki ko shago. Kuma kada mu taimake su cikin abin da suke yi na tsafi da tsibbu, kada mu rufa musu asiri. A’a, mu yi abin da yake wajibi a kanmu, na umarni da kyakkyawa, da hani daga mummuna. Allah yana cewa,

( وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ) [المائدة: ٢].

“Ku yi taimakekeniya a kan aikin nagarta da tsoron Allah, kada ku yi taimakekeniya a kan laifi da qetare iyaka”.

Sheikhul Islam Ibn Taimiyya yana cewa, “Haqiqa mun yi bayani da abin da muka ambata cewa, ladan da aka karva a kan haka - wato bokanci - da kyauta da sadaka, haram ne a kan mai bayarwa, da mai karva, kuma haramun ne ga masu gidaje da wakilai, su ba da hayar shaguna ko waninsu ga waxannan kafirai, don su yi irin wannan amfani da su, idan zatonsu ya yi rinjaye kan cewa, abin da za su yi da su kenan. Kuma wajibi ne a kan shugabanni, da duk wanda yake da iko, su yi aiki don kawar da haka, da kuma hana su zama shaguna, ko kan hanya, ko kuma shiga gidajen mutane. Idan kuwa shugaba bai aikata haka ba, to faxin Allah ya hau kansu, inda yake cewa,

Ma’ana» “Su, su kasance ba sa hana junasu kan mummunan aiki da suka aikata».

Da kuma faxarsa,

( لَوْلَا يَنْهَاهُمُ الرَّبَّانِيُّونَ وَالْأَحْبَارُ عَنْ قَوْلِهِمُ الْإِثْمَ وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَصْنَعُونَ 63 ) [المائدة: 63]

(Menene ya hana mutane na Allah da malamai ba za su hana su faxar laifi ba da cin rashawa. Tir da abin da suke aikatawa).

Kowa ya yadda da cewa, su waxannan tsinannun, suna faxar laifi, kuma suna abin da bai halatta ba. Kuma ya tabbata daga Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Idan mutane suka ga mummuna, ba su sauya shi ba, to Allah ya kusa ya game su da uquba daga gare shi.” Wane munkari ne ya fi aikin waxannan gurvatattu, sarin masu mulki, maqiya Manzanni, ‘ya’yan sabi’awa, masu bautar taurari.

Ku ji tsoron Allah, ya bayin Allah, kuma ku tuba gabaxaya, ku nemi gafararsa, ku dogara gare shi, shi kaxai cikin dukkan abubuwa, ku qyale waxannan abubuwa, ku nesance su, ku lazimci xa’ar Allah da Manzonsa, ku kare addininku da aqidarku, domin a yau, aiki ne babu hisabi, gobe kuma, hisabi ne babu aiki.