Manufofin huxubar
Haxa Zukata da Allah Maxaukakin Sarki.
Fito da wasu daga cikin hanyoyin da mai wa’azi zai kama zukatan masu sauraro da su.
Bayanin yadda ake shiryar da mutane ta hanyar hikima da kyakkyawan wa’azi da tausasawa.
Bayanin wasu daga cikin hanyoyin da Manzon Allah (S.A.W) yake bi wajen kira zuwa ga Allah.
Tsoratarwa daga korar mutane daga fahimtar addini.
Huxuba Ta Farko
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.
Ya ku ‘yan uwana musulmi masu sauraro : a yau zamu yi magana ne akan tsokar da ta fi mahimmanci a jikin xan adam, tsokar da idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuwa ta vace to dukkan jiki ya vace.
Kasancewar zuciya tana da mahimmanci a babba a wajen gyaruwar xan adam, sai ta zama kamar sarki a jikin jiki, sauran gavovi talakawanta, don haka wajibi ne akan mai wa’azi da kira zuwa ga addinin Allah ya damu da sanin hanyoyin da zai isar da kiransa da saqonsa gareka, don wa’azinsa ya isa ga mutane, su amfani da shi. Ga wasu daga cikin waxannan hanyoyin :
Abu na farko : Wajibi ne akan mai da’awa ya haxa zukatan mutane da Allah, ya koya musu tsarkake Allah, da dogaro gare shi, da son shi, da fata, da tsoro duk ga Allah Maxaukakin Sarki, saboda idan zuciya ta tsarkaka, ta koma zuwa ga Allah, to zai mata sauqi ta kamanta umarnin Allah, ta hanu daga abin da ya hana.
Hakanan wajibi ne akan mai da’awa ya zama yana qara wa kansa ilimi, ya karanta Al’qur’ani ya hardace da abin da zai iya daga cikinsa, ya karanci Sunnah ya fahimce ta daidai gwargwado.
Kamar yadda yake kan da’awa ya zama mai sauqi da haquri da mutane, Allah Maxaukakin Sarki yana cewa Annabinsa :
( فَبِمَا رَحْمَةٍ مِنَ اللَّهِ لِنْتَ لَهُمْ وَلَوْ كُنْتَ فَظًّا غَلِيظَ الْقَلْبِ لَانْفَضُّوا مِنْ حَوْلِكَ فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاسْتَغْفِرْ لَهُمْ وَشَاوِرْهُمْ فِي الْأَمْرِ) [آل عمران: 159]
Ma’ana : “Saboda Rahamar Allah ka tausasa musu, domin da ka zama mai tsanani da kaushin zuciya da sun watse daga wajenka, ka yi musu afuwa ka shawarce su a cikin al’amarin…”. (Ali Imran : 159 )
Sannan An karvo daga A’isha – Allah ya yarda da ita – ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Sauqi da tausasawa ba sa shiga cikin komai face sai sun qawata wannan abun, haka nan ba a rasa tausasawa a cikin komai face sai ya yi muni” Muslim da Ahmad da Abu Dawud suka rawaito shi. Yana daga cikin sauqaqawa yin abubuwan da za su zo :
Kada ya matsanta wa mutane da tsawaita wa a wajen sallah ko huxuba.
Kada ya matsanta wa mutane da yawan karatu, da tsawaita shi, da yin karatun da bai dace da buqatunsu ba.
Mai wa’azi ya zama tare da mutane a koda yaushe, kada ya zama mai girman kai a garesu, kada ya nisance su, kada ya zama idan sun neme shi basa samunsa, idan suna buqatarsa sai su rasa shi, saboda kusantarsu da qaunarsu shi ne zai jawo masa matsayi a zukata, da soyayya a cikin zuciya, idan ya yi magana su ji, su yi aiki da ita, idan ya nemi su yi wani abu su aikata, idan ya fuskantar da su zuwa ga wani abu, su yarda su yi abin da ya ce. Saboda haka mai wa’azi ya zama yana tare da mutane yana cikin muhimman abubuwa.
Daga cikin abin da mai da’awa yake kama zukatan mutane da shi, ya zama abin koyi a wurinsu, kada ya aikata abin da ya hana su, ya yi kuma abin da ya umarce su da shi , Allah Maxaukakin Sarki yana cewa :
( أَتَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبِرِّ وَتَنْسَوْنَ أَنْفُسَكُمْ وَأَنْتُمْ تَتْلُونَ الْكِتَابَ أَفَلَا تَعْقِلُونَ 44 ) [البقرة: 44]
Ma’ana : “Kuna umartan mutane da alheri amma kuna manta wa da kawunanku, alhali kuna karanta littafi, ashe ba za ku zama masu hankali ba”. (Baqara : 44 )
Haka kuma ana son mai wa’azi da da’awa ya zama mai kyauta da bayarwa gwargwadon ikonsa, Saboda Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mutum ne mai yawan kyauta, ya kasance lokacin da ya fi kyauta shi ne cikin watan Ramadan, lokacin da Mala’ika Jibrilu yake haxuwa da shi ya yi masa karatun Alqur’ani, kamar yadda Imamul Bukhari ya rawaito
Yaku ‘yan uwa musulmi : Yana cikin babban muhimmin abin da ake kama zukata da shi, hikima wajen wa’azi da karantarwa. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa Annabinsa :
( ادْعُ إِلَى سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ وَجَادِلْهُمْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنْ ضَلَّ عَنْ سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ 125 ) [النحل: 125]
Ma’ana : “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau, ka yi jayayya da su ta (hanyar) da ta fi kyau, haqiqa Ubangijinka ya san wanda ya vace ga barin hanyarsa, kuma shi ne ya san shiryayyu”. (Annahal : 125)
Ibnu Kasir – Allah ya jiqansa da rahama - ya ce : “Allah Maxaukakin Sarki yana mai umartar Annabinsa Muhammad (S.A.W) da cewa ya kira mutane zuwa ga Allah da hikima. Ibnu Jarir ya ce, (Hikima) ita ce abin da Allah ya saukar masa na Alqur’ani da Sunnah, wa’azi kyakkyawa kuwa shi ne abin da yake cikin (Alqur’ani) na tsawatarwa da (faxin) abubuwan da suka sami mutanen da (suka savawa Allah), ka tunatar da su don su kiyayi azabar Allah Maxaukakin Sarki. Faxin Allah “Ka yi jayayya da su ta (hanyar) da ta fi kyau) tana nufin wanda ya buqaci jayayya da tattaunawa da kai a cikinsu to ka yi jayayyar da tattaunawar da shi ta fuskar da ta fi kyau, da tausasawa, da kyakkyawar magana, kamar faxin Allah “Kada ku yi jayayya da ma’abota littafi sai ta (hanyar) da ta fi kyau, sai dai idan waxanda suka yi zalunci ne daga cikinsu” (Anan zamu ga Allah ya umarci Annabinsa) da tausasawa, kamar yadda ya umarci Musa da Haruna – Amincin Allah ya tabbata a gare su – da tausasawa lokacin da ya aike su zuwa ga Fir’auna, Allah ya ce, “Ku faxa masa magana mai taushi ko ya wa’azantu ko kuma ya ji tsoron Allah”. Faxin Allah “haqiqa Ubangijinka ya san wanda ya vace ga barin hanyarsa” ma’ana ya san wanda yake xan wuta a cikinsu, ya san xan Aljannah, ya kuma rubuta hakan a wajensa, ya gama da shi, don haka ka kira su zuwa ga Allah, kada ka damu da wanda ya vace daga cikinsu, shiriyarsu ba a wajenka take ba, kaxai kai mai isarwa ne, hisabi kuwa yana wajenmu “Kai ba ka shiryar da wanda ka so” “Shiriyarsu ba a kanka ta ke ba, sai dai Allah yana shiryar da wanda ya so”.
Yana cikin hikima wajen yin wa’azi voye sunan wanda ya yi aikin da ba daidai ba yayin yi masa wa’azi a cikin jama’a, kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) yake yi, yana cewa “Me yasa wasu mutane suke kaza da kaza”.
Don haka wajibi ne a kanka – mai wa’azi – ka lura da waxannan hanyoyi masu kyau, har wa’azinka ya kai zuwa ga wanda kake kira, ya yi amfani duniya da lahira.
Allah Maxaukakin Sarki ya yi mana albarka cikin abin da muka ji, na Alqur’ani da Hadisi, Haqiqa shi Allah mai iko ne akan dukkan komai.
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.A.W) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:
Ya kai xan uwana mai da’awa : Saurara ka ji wasu daga cikin hanyoyin da Manzon Allah (S.A.W) yake bi wajen da’awarsa don ka yi koyi da shi
An karvo daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, wasu mutane guda uku sun je gidajen matan Annabi (S.A.W) suna tambayar yaya ibadan Annabi (S.A.W) take, da aka faxa musu, kai ka ce sun ganta kaxan, don haka sai suka ce, ina mu ina ibadar Annabi (S.A.W) alhali an gafarta masa abin da ya gabata na zunubi da abin da zai zo, saboda haka sai xayansu ya ce, Ni dai zan yi ta sallah da daddare har abada. Xayan kuma ya ce, “Ni kuma zan yi ta yin azumi ba zan huta ba” Xayan kuma ya ce, “Ni kuma zan nisanci mata, ba zan yi aure ba har abada”. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya je wajensu ya ce, “Ku ne kuka ce kaza da kaza, To Wallahi ni na fi ku tsoron Allah, na fi ku kiyaye dokokinsa, amma duk da haka ina azumi kuma ina hutawa, ina yin sallar (dare) kuma ina yin barci, ina kuma tarawa da mata, duk wanda ba ya son sunnata to ba ya tare da ni”.(Bukhari)
Misali na biyu : An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya yi wani abu, ya kuma ya yi rangwame a kan yin sa, amma sai wasu mutane suka qyamaci wannan abun, sai labari ya zo wa Annabi (S.A.W) sai ya yi huxuba ya godewa Allah ya ce, “Me ya samu wasu mutane suke qyamatar abin da na yi!?, to na rantse da Allah ni na fi su sanin Allah, na fi su tsananin tsoronsa”. Bukhari ya rawaito shi.
Na Uku :An karvo daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Me yasa mu waxansu mutane suke xaga idanuwansu sama a cikin sallarsu!?” Sai Manzon Allah (S.A.W) ya tsananta ya ce, “Ko dai su hanu daga hakan, ko kuma a fizge ganin nasu”. Abu Dawud ne ya rawaito.
Na huxu : An karvo daga Mu’awiyya xan Hakam Assulamiy – Allah ya yarda da shi – ya ce, Ina cikin sallah tare da Manzon Allah (S.A.W) sai wani mutum ya yi atishawa, sai na ce masa “Yarhamukal Lahu” nan da nan sai mutane suka zare min idanuwa suna kallona, sai na ce, “Wayyo Kaicona!, meye ya same ku, kuke kallona” sai mutanen suka riqa dukan cinyoyinsu, da dai na ga suna nuna min in yi shiru, sai na yi shiru. Lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya gama sallah – kai! na fanshe shi da babana da babata – ban tava ganin malami da ya iya koyarwa kamarsa ba, Wallahi bai yi min tsawa ba, ko ya doke ni, ko ya zage ni, kaxai ya ce min “Wannan sallah ba dace a yi maganganu da mutane a cikinta ba, ita dai sallah tasbihi ce, da kabbara da karatun Alqur’ani”. Muslim da Ahmad da Abu Dawud suka rawaito shi.
Misali na biyar : shi ne hadisin da Anas xan Malik ya rawaito ya ce, Wani mutumin qauye ya yi fitsari a wani wuri a cikin masallaci, sai mutane suka yi masa tsawa, amma sai Manzon Allah (S.A.W) ya hana su. Da ya gama fitsarinsa, sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni da guga cike da ruwa aka zuba a kai” Bukhari ne ya rawaito.
Waxannan kaxan kenan daga cikin hanyoyin da Manzon Allah (S.A.W) yake bi wajen wa’azi da kiran mutane zuwa addinin Allah. Idan muka lura zamu ga a cikin waxancan hadisai irin yadda Manzon Allah (S.A.W) yake tausayawa mai kuskure, yake kuma fahimtar da shi, ba tare da tozartawa, ko zagi ko cin mutunci ba.
Yaku ‘yan uwa masu da’awa : Ku sani cewa akwai wasu kura – kurai da masu wa’azi da da’awa suke faxa wa cikinsu, waxanda suke sa mutane suna guje wa addini da gaskiya, ga wasu daga cikin irin waxannan kura – kurai don mu nisance su :
Daga cikinsu : akwai tsananta wa mutane da kausasa musu, mu duba mu ga yadda Manzon Allah (S.A.W) yake cewa wakilansa yayin da ya aika su zuwa kiran mutane, yakan ce musu, “Ku yi bushara, ku sauwaqa, ku koyar, kada ku kori mutane” Muslim ne ya rawaito.
Daga cikin irin waxannan kura – kuran akwai fatawa ba da ilimi ba, wanda wannan babbar musiba ce a addini. An karvo daga Jabir xan Abdullahi – Allah ya yarda da shi – ya ce, mun fita wata tafiya, sai dutse ya sami wani mutum daga cikinmu ya ji masa ciwo a ka, sai kuma ya yi mafarki (janaba ta same shi), ya tambayi abokan tafiyarsa, shin akwai wani rangwame na yin taimama (ma’ana ba sai na yi wanka ba, saboda ciwon da yake kaina), sai suka ce, “babu wani sauqi tun da dai zaka iya amfani da ruwa”, sai ya je ya yi wanka, ya mutu. Jabir ya ce, da muka dawo wajen Annabi (S.A.W)aka ba shi labarin abin da ya faru, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Sun kashe shi, Allah ya kashe su, ba za su tambaya yayin da ba su sani ba, ku sani maganin jahilci tambaya, kaxai ya ishe shi ya yi taimama, ya xaure ciwonsa, ya yi shafa a kan sauran jikinsa” Abu Dawud da Ibnu Majah suka rawaito shi.
Ku duba yaku ‘yan uwana irin yadda fatawa ba da ilimi ba ta jawo kisan rai, Allah Maxaukakin Sarki ya kare mu.
A qarshe ku sani yaku ‘yan uwana masu wa’azi, cewa wajibi ne ku kama zukatan mutane da hanyar kyakkyawan wa’azi, da shiryarwa tare da hikima, ku bi hanyar Manzon Allah (S.A.W) da Sahabbansa da waxanda suka bi yo bayansu, ku yi koyi da su iya iyawarku, ku nisanci korar mutane daga wannan addini mai girma, ko yaushe ku riqa tuna faxin Manzon Allah (S.A.W) cewa “Allah ya shiryi mutum xaya ta hanyarka, ya fi maka jajayen raquma”. Allah yana tare da ku, ba kuma sai tozarta ayyukanku ba.