islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Haqqin Shuwagabanni Da Talakawa


12360
Surantawa
Haqiqa addinin musulunci addini ne cikakke, don haka ya tanadi duk wani abu da mutane ke bu'kata a rayuwarsu, daga ciki akwai shugabanci. Don haka ne ma ya shimfida yadda mu'amala ya kamata ta kasance tsakanin shuwagabanni da talakawansu, da haqqoqin da suka rataya akan kowanne daga cikinsu.

Manufofin huxubar

Bayyana cewa shari’ar musulunci cikakkiya ce a cikin tsarinta.

Bayyana cewa shari’ar musulunci ta wajabta samun shugaba a cikin al’umma.

Sanar da shugabanni haqqoqin talakawa da suke kansu.

Sanar da talakawa haqqoqin shugabanni a kansu.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

‘Yan uwana Musulmi, Allah Maxaukakin Sarki yana cewa a cikin littafinsa mai tsarki :

( الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا ) [المائدة: 3]

Ma’ana : “A yau na cika muku addininku, kuma na cika muku ni’imata gareku, na yardar muku musulunci ya zama addini gareku”. (Al-Ima’ida : 3 )

Haqiqa addinin musulunci addini ne cikakke ta kowanne vangare, don haka musulmi ba sa buqatar wani addini wanda ba shi ba, basu buqatar wata shari’a wadda ba ita ba, saboda cikar shari’ar musulunci, ta qunshi dukkan abin da yake maslaha ne ga al’umma, ta bawa dukkan mutane haqqoqinsu, talakawa da masu arziqi, masu mulki da waxanda ake mulka, namiji da mace, kai har ma da dabbobi, Allah Maxaukakin Sarki ya ba duk wani mai haqqi haqqinsa.

To daga cikin abin da musulunci ya ba shi kulawa, al’amarin shugabanci da jagoranci, musulunci bai bar mutane su zauna kara zube ba, a’a ya yi umarni da naxa shugaba koda a halin tafiya ne, saboda amfanin samun shugaba a cikin al’umma amfani ne bayananne baya buqatar wani dogon bayani, don rayuwar mutane ba za ta tsayu ta gyaru ba sai idan akwai shugabanci a cikinsu, don haka Allah maxaukakin sarki da Manzon Allah (ﷺ) suka nuna mahimmancin bin shugaba da samun shugabancin a cikin mutane, Allah Maxaukakin Sarki ya ce :

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ ) [النساء: 59]

Ma’ana : “Yaku waxanda kuka yi imani ku bi Allah, ku bi Manzon Allah, (sannan ku bi) ma’abota al’amari daga cikinku” (Al – Nisa’i 59).

Kuma Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Duk wanda ya yi min xa’a to ya yi wa Allah, wanda kuma ya sava min to ya sava wa Allah. Haka duk wanda ya bi shugaba to ya bi ni, wanda kuma ya sava wa shugaba to ya sava min. shugaba garkuwa ce da ake yaqi a bayanta, ake kariya da ita, don haka idan shugaba ya yi umarni da tsoron Allah, ya yi adalci, to yana da lada, in kuwa ya aikata savanin haka to wannan laifi yana kansa” Bukhari ne ya rawaito.

An karvo daga Ummu Salama, matar Annabi (ﷺ), daga Annabi (ﷺ) ya ce, : “Haqiqa za a naxa muku shugabanni a bayana, waxanda zaku ga abu mai kyau a tare da su, kuma ku ga marasa kyau, wanda ya qi maras kyau xin ya kuvuta, haka ma wanda ya yi inkari, sai dai wanda ya yarda ya bi (to wannan mai laifi ne). Sai sahabbai suka ce “ba za mu yaqe su ya Manzon Allah? Sai ya ce, “a’a, matuqar dai suna yin sallah”. Muslim ne ya rawaito shi.

Ya ‘yan uwa : Waxannan kaxan kenan daga cikin dalilan da suke nuna mahimmancin samar da shugabanci a musulunci, saboda haka ma musulunci ya tsara haqqoqin shugaba akan talakawansa, ya kuma tsara haqqin talaka a kan shugabansa.

Yana cikin haqqin talakawa akan shugabansu ya samar musu da kotunan da za su riqa yanke hukunci tsakanin mutane da sasanta su, ya samar da kwamitocin da za su riqa sasanta mutane, suna umarni da kyakkyawan aiki suna hana mummuna. Kamar yadda yake wajibi ne akan shugaba ya tsaida haddi akan duk wanda ya qetare iyaka, ya zalunci bayin Allah, ya tava rayukansu ko jininsu ko dukiyoyinsu, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : “Haddi xaya da za a yi aiki da shi a bayan qasa, ya fi a yi wa mutanen qasa ruwa na kwana arba’in”. Ibnu Majah ne ya rawaito shi, Sheikh Albani ya ce Hadisi ne mai kyau.

Hakanan haqqi ne akan shugaba ya sadar da haqqoqi ga masu su, ya samar da ‘yan sanda, waxanda za su ba da tsaro ga mutane da dukiyoyinsu, saboda rayuwa ba ta yiwu wa sai da tsaro, kamar yadda wajibi ne akan shugaba ya gina makarantu da wuraren ibada, ya samar da qwararrun malamai waxanda za su koyar da al’umma addini kamar yadda Manzon Allah ya zo da shi. Ya taimaka wa masu bincike, ya taimaka a wajen buga littattafan addini da sauran irin waxannan ayyuka.

Hakanan wajibi ne akan shugaba ya zama mai adalci tsakaninsa da talakawansa, saboda adalci shi ne tushen rayuwa, kuma da adalci ne al'amura suke daidaita duniya da lahira.

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya yana cewa : "Al'amurar mutane na duniya suna daidaita ne da adalcin da yake haxe da nau'uka na zalunci fiye da yadda al'amura za su miqe da zalunci a cikin haqqoqi, ko da kuwa ba su tarayya a zunubi ba, don haka aka ce, Allah yana tsayar da daula mai adalci ko da kuwa kafira ce, ba ya kuma tsayar da daular azzaluma ko da kuwa musulma ce, hakanan ana cewa : Duniya tana dauwama da adalci da kafirci, amma bata dauwama da zalunci da musulunci. Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : "Babu wani zunubi da ya fi sanya azaba da wuri fiye da zalunci da yanke zumunci" Azzalumi ana buge shi a duniya koda kuwa an masa gafara da rahama a lahira, saboda adalci tsari ne a cikin komai da komai, idan aka tsayar da al'amarin duniya akan adalci sai komai ya tsaya, koda kuwa ma'abocin duniyar nan ba shi da rabo a lahira, idan kuwa ba tsayar da al'amurar duniya akan adalci ba, to lamarin ba zai tsaya ba, ko da kuwa ma'abocinsa yana da imanin da zai ishe shi a lahira" (Duba : Maj’mu’ul Fatawa 28/ 146).

Haka nan shugaba ya zama qarfi wajen zartar da abin da yake gaskiya ne a cikin talakawansa, ya nisanci zalunci, da qarya da cin amana, da ha’inci, da sauran munanan halaye.

Waxannan su ne kaxan daga cikin haqqoqin talakawa a kan shugabaninsu, don haka wajibi ne akan shugabanni su kiyaye waxannan haqqoqi, saboda al’amuran talakawansu amana ce a wuyansu, Allah zai tambaye su abin da ya basu kiwo na daga bayinsa. Ku ji tsoron Allah yaku shuwagabanni, ku kamanta, ku nemi taimakon Allah ta hanyar sallah da haquri, Allah yana tare da masu haquri, kuma kyakkyawan karshe yana ga masu tsoron Allah.

Allah Maxaukakin Sarki ya yi mana albarka cikin abin da muka ji na Alqur’ani da Hadisi, haqiqa shi mai iko ne akan komai.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (ﷺ) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Yaku ‘yan uwana musulmi : Babu ko shakka shugabanni suna da haqqoqi masu girma a kanmu, wanda da samuwar su ne al’amura za su miqe, su daidaita, komai ya tafi yadda ake so, daga cikin irin waxannan haqqoqi akwai ji da biyayya a cikin abin ba savon Allah da Manzonsa ba ne.

Ji da biyayya ga shuwagabanni – ya ‘yan uwa – wajibi ne ko da kuwa waxannan shuwagabannin suna zalunci da son kai, yin tawaye da fito – na – fito da su baya halatta, saboda Manzon Allah (ﷺ) ya hana. Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : “Za a samu son kai, da wasu abubuwan da kuke qi”. Sai sahabbai suka ce, “To me kake umartar mu da shi ya Rasulallahi?” sai Manzon Allah ya ce, “Ku sauqe nauyin da yake kanku, ku kuma ku roqi Allah haqqinku”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

Imam Annawawiy – Allah ya yi masa rahama – ya ce, “Wannan hadisi yana daga cikin mu’ujizar Annabta, wannan hadisi ya maimaitu da yawa, kuma abin da hadisin ya bada labari shi ma an same shi da yawa. Sannan a cikin hadisin akwai kwaxaitarwa a kan ji da biyayya (ga shugaba) koda kuwa wanda yake kai azzalumi ne mai shirme, sai a bashi haqqinsa na biyayya, ba za a yi masa tawaye ba, baza a jire shi ba, za a koma a qasqantar da kai ga Allah a kan ya yaye cutarsa, ya ije sharrinsa, ya gyara shi”. Duba littafin (Sharhin Sahihi Muslim J 12 sh 543, Bugun Darul Khari.

An karvo daga Abu Zarri – Allah ya yarda da shi – ya ce, Badaxayina (wato Manzon Allah) ya yi min wasiyya in ji kuma in yi biyayya, koda wanda aka shugabantar min bawa ne mai yankakken gavvai. Muslim ne ya rawaito shi.

An karvo daga Ummul Husaini – Allah ya yarda da ita -, ta ji Manzon Allah (ﷺ) yana huxuba a hajjin ban – kwana yana cewa : "Koda an xora muku bawa, yana jagorantarku da Littafin Allah to ku saurare shi kuma ku yi masa xa'a". Muslim ne ya rawaito.

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya – Allah ya ji qansa da rahama – yana cewa, “Wannan ya sa mashahurin mazhabar Ahlil – sunnah rashin yarda da fito – na – fito da shuwagabanni, da yaqarsu da takobi, ko da kuwa waxannan shuwagabannin suna da zalunci, kamar yadda hadisai ingantattu masu yawa daga Annabi (ﷺ) suka nuna, saboda varna da fitinar da zata samu wajen yaqarsu tafi wadda ake samu a dalilin zalincinsu, wanda ba bu yaqi a cikinsa, babu fitina. Sannan ba a kawar da fitina qarama da babba, don haka a tarihi ba a tava samun waxanda suka yi fito – na – fito da mai mulki ba face sai ya zama varnar da suka haifar ta fi wadda suka kawar. Haka kuma Allah Maxaukakin Sarki bai yi umarni a yaqi duk wani azzalumi ba, kamar yadda bai ce a fara yaqar duk wani wanda qetare iyaka ba, abin da ya ce, shi ne :

( وَإِنْ طَائِفَتَانِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ اقْتَتَلُوا فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا فَإِنْ بَغَتْ إِحْدَاهُمَا عَلَى الْأُخْرَى فَقَاتِلُوا الَّتِي تَبْغِي حَتَّى تَفِيءَ إِلَى أَمْرِ اللَّهِ فَإِنْ فَاءَتْ فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا بِالْعَدْلِ وَأَقْسِطُوا إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِينَ 9 ) [الحجرات: 9]

“Idan jama’u biyu daga cikin muminai suka yi faxa da junansu to ku yi musu sulhu, idan xayansu ta qetare iyaka akan xayar, to ku yaqi wadda ta qetare iyakar har sai ta koma zuwa ga umarnin Allah (na yarda da sukhu) idan ta dawo zuwa ga umarnin Allah, to ku yi musu sulhu da adalci”. Anan zamu ga Allah bai yi umarni da fara yaqar jama’ar da suka qetare iyaka ba har sai bayan da suka qi yarda da umarnin Allah, to yaya kuma Allah zai yi umarni a fara yaqar shuwagabanni!?” (Duba : Minhajus sunnah J 3 sh 391).

Don haka – yaku ‘yan uwa – abin da wasu matasa suke yi na fito – na – fito da shuwagabanni da yaqarsu abu ne da ya ci karo da dalilai na shari’a masu yawa, waxanda suka yi umarni da rashin yin haka, da haquri da kawar da kai daga abin irin waxannan shugabanni suke yi, matuqar dai suna sallah.

Yana daga cikin haqqin shugaba a kan talakawansa su yi masa addu’a, saboda hakan yana daga cikin manya – manyan abubuwan da suke kusantar wa ga Allah, mafi girman xa’a gare shi, sannan yana cikin nasiha ga Allah da bayinsa. Kuma aqida ce daga cikin aqidun Ahlis-sunnah wal Jama’a, kamar yadda Imam Sabuni da Isma’iliy da Xahawiu suka faxa. Duba (Alma’alum min wajibil alaqa bainal Hakim Wal Mahkum Na ibnu Baz Sh 21).

Hakanan yana cikin haqqin shugabanni yi musu nasiha da daidaita su, wannan haqqi ne da yake kan wuyan malamai da masu da’awa, sannan ya dace a wajen yi wa shugabanni nasiha a lura da lokutan da suka dace, da maganganun da suka dace, a tunatar da su kyakkyawan aiki, a hana su mummunan aiki, cikin ladabi da sauqaqawa, da rangwantawa. A kiyaye da matsayinsu da darajarsu, hakan zai sa a karva a kuma samu abin da ake nema”.

Ibnul Jauziy – Allah ya yi masa rahama – yana cewa : “Abin da yake halatacce ne wajen umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummuna ga masu mulki shi ne wa’azi da tausasa wa, amma kausasa magana kamar cewa, “Yakai azzalumi, ya wanda ba ya tsoron Allah. Idan irin wannan zai kawo fitinar da sharrinta zai kai zuwa ga wani to baya halatta, in kuwa abin ba zai shafi wani ba sai shi kansa mai wa’azin to ya hallata a wurin jumhurun malamai”. Duba (Al-adabush shar’iyya 1/196).

Yana daga cikin haqqoqinsu taimakonsa da basu goyon baya, saboda wajibi ne a kan musulmi su taimaka wa masu mulkinsu cikin duk abin da zai kawo ci gaba da alheri a dukkan vangarori na cikin gida da waje, da zartar da dokoki da hukunce – hukuncen shari’a, da umarni da aiki mai kyau da hana mummuna, abin da ya shafi kowa – da kowa da abin da ya shafi masu mulkin.

Wannan kaxan kenan daga cikin haqqoqin shugabanni a kan talakawansu, don haka ku ji tsoron Allah – ‘Yaku bayin Allah – ku bi Allah da Manzonsa ba. Zaku rabauta duniya da lahira.