islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Haqqin musulmi akan musumi dan-uwansa


12453
Surantawa
Yanuwantaka don Allah niima ce babba daga Allah, kuma wata irin falala ce da Allah ke kwararota da kyautarta ga bayinsa muminai masu gaskiya. Yanuwantaka abin sha ne me tsarki da Allah ke shayar dashi ga muminai tsarkaka. Haqiqa musulunci ya zaqu wajen qarfafa dankon zumunci tsakanin musulmi da dau-uwansa, don haka ne ma ya sharanta wasu alamura da zasu qarfafa wannan alaqa, kamar yada sallama, da gaida marasa lafiya, da dai sauran haqqoqin musulmi akan musulmi dan uwansa.

Manufofin huxubar

Bayanin haqiqanin ‘yan uwantaka a musulunci.

Bayanin wajabcin taimakon juna a musulunci.

Bayanin falalar ‘yan uwantaka a musulunci da nuna cewa ta fi ‘yanuwantakar Jini.

Tsoratarwa daga rarrabuwa da xaixaicewa a tsakanin musulmi.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Ya ‘yan uwana musulmi : Haqiqa addinin musulunci addini ne mai girma, kuma addinine mai tsari, ya tsara wa mabiyansa kyakkyawan tsari, tsarin da ya haxa kiyaye haqqoqin da wajibai, kuma babu wani aiki na qwarai da yake tafiya a banza a cikin wannan tsari, tsari ne da ya ba duk wani mai haqqi haqqinsa, daga cikin irin waxannan haqqoqi da wannan tsari ya zo da shi akwai haqqin musulmi a kan xan uwansa musulmi.

Yaku yan uwa Musulmi : Haqiqa Manzon Allah (ﷺ) ya tabbatar da cewa Musulmi yana da haqqi a kan xan uwansa musulmi, in da yake cewa, “Haqqin musulmi a kan musulmi shida ne. Aka ce mene ne su ya Manzon Allah?” Sai Manzon Allah ya ce, su ne, “idan ya gamu da shi ya yi masa sallama, idan ya gayyace shi ya amsa, idan ya neme shi ya yi masa nasiha, ya yi masa, idan ya yi atishawa ya gode wa Allah ya gaishe shi, idan baya da lafiya ya je ya duba shi, idan ya mutu ya raka shi” Muslim ne ya rawaito shi.

A cikin wannan hadisi mai girma zamu ga Manzon Allah (ﷺ) ya faxi wasu haqqoqi da musulmi yake da shi akan xan uwansa musulmi. Aiki da waxannan haqqoqi - babu ko shakka – zai kawo soyayya da qauna da zaman lafiya a tsakanin musulmi, wanda hakan ya kan zama sababin mutum ya shiga Aljannah. Saboda ya zo a cikin hadisin da Imam Muslim ya rawaito, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Na rantse da wanda raina yake hannunsa, ba zaku shiga Aljannah ba, har sai kun yi imani, kuma ba zaku yi imani ba, har sai kun so junanku. Ashe bana nuna muku abin da idan kuka aikata shi zaku so junanku ba? Ku yaxa sallama a tsakaninku”.

Yana cikin haqqin musulmi a kan musulmi kada ya yi masa hassada, kada ya qullace shi, saboda shi mumini qirjinsa a wanke yake, zuciyarsa mai tsarki ce, yana kwana ba tare da qullin wani ko hassada a zuciyarsa ba, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa a cikin hadisin da Bukhari da Muslim suka rawaito daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, : “Kada ku yi gaba da juna, kada ku ba juna baya, kada ku yi gasa da juna, ku zama bayin Allah ‘yan uwan juna”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

Yana daga cikin haqqin musulmi a kan xan uwansa musulmi ya taimaka masa daidai gwargwadon ikonsa wajen biyan buqatunsa na duniya, ya sauwaqa masa idan ya shiga tsanani, ya suturta shi yayin da yake buqatar sutura. An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wanda ya yaye wa wani mumini baqin ciki daga cikin baqin cikin duniya, Allah zai yaye masa wani baqin ciki daga cikin baqin cikin lahira. Wanda duk ya sauwaqa wa wanda yake cikin matsi, Allah zai sauwaqa masa duniya da lahira, wanda duk ya suturta musulmi, Allah zai suturta shi duniya da lahira. Allah yana cikin taimakon bawa matuqar bawa yana taimakon xan uwansa” Muslim ne ya rawaito.

Hakanan yana cikin haqqin musulmi akan musulmi taimakonsa a cikin kowane hali da yanayi, ya taimake shi idan yana zalunci, kamar yadda zai taimake shi idan ana zaluntar shi. An karvo daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ka taimaki xan uwanka, ana zaluntarsa ko shi yana zalunci. Sai wani mutum ya ce, “Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ana zaluntarshi, amma yaya zan taimake shi idan yana zalunci?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ka riqe hannunsa” (ka hana shi zalunci).

Yana cikin haqqin musulmi ne akan xan uwansa musulmi ya voye aibinsa, ya yi masa afuwa da rangwame yayin da ya yi masa wani abu maras daxi, yin haka yana daga cikin manya – manyan haqqin musulmi akan xan uwansa musulmi, saboda xan uwanka ba mala’ika ba ne, ba Annabi ba ne, mutum ne don haka ka suturta shi.

Malamai suna cewa : Mutane kala biyu ne. Kala na farko su ne waxanda suka shahara a cikin mutane da nagarta da nisantar savo, to irin waxannan idan suka faxa cikin kuskure ana son musulmi su yi musu afuwa, su suturta su, kada su bibiyi al'aurarsu, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa a cikin hadisin da Imam Ahmad ya rawaito daga Abi Barzatal Assalami ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, : “ Yaku taron waxanda suka yi imani da harshensu, amma imanin bai shiga zuciyarsu ba. Kada ku yi gulmar musulmi, kada ku bibiyi alurarsu, duk wanda ya bi al’aurar musulmi, shi ma Allah zai bi al’aurarshi, duk kuwa wanda Allah ya bibiyi al'aurarsa to zai kunyata shi a cikin gidanshi” .

Kala na biya daga cikin mutane, su ne, waxanda suke bayyana savonsu a fili, ba sa jin kunyar Allah, ba sa jin kunyar mutane, to irin waxannan fasiqai ne, ba a suturta su.

‘Yan uwana masu sauraro : Son juna saboda Allah ba qarami abu ne a musulunci, yana daga cikin abubuwan da suke nuna cikar imanin mutum, kuma yana iya zama sababi daga cikin sababan da suke kai mutum Aljannah.

Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Abubuwa guda uku, wanda yake da su ya xanxani zaqin imani, ya zama ya fi son Allah da Manzonsa akan waxanda ba su ba, sannan ya so mutum don Allah, ba don wani abu ba, sannan ya qi komawa kafirci kamar yadda yake qin a sanya shi a wuta”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wani mutum ya tafi wani gari don ya ziyarci wani xan uwansa, sai Allah ya sanya masa Mala’ika a kan hanyarsa yana jiransa. Lokacin da wannan mutumin ya iso wajen Mala’ikan, sai ya ce da shi, “ina zaka je?” Sai ya ce, “Zan ziyarci wani xan uwana ne a wannan gari”. Sai Mala’ikan ya ce, “Shin akwai wata ni’ima ce wadda kake renonta a wajensa?” sai ya ce, “A’a, ni dai kawai ina son shi ne saboda Allah”. Sai Mala’ikan nan ya ce da shi, “Ni Allah ne ya aiko ni wajenka, ya ce, yana sonka kamar yadda kake son shi”.

Wannan ita ce haqiqanin 'yan uwantaka ta gaskiya, kuma wannan ita ce haqiqaninta, haqiqa 'yan uwantaka saboda Allah ba ta ginuwa akan komai sai akan igiyar aqida da igiyar imani da igiyar soyayya saboda Allah, waxannan igiyoyi ba sa tsinkewa har abada.

An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Mutane bakwai Allah zai musu inuwa a cikin inuwarsa, ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa, shugaba mai adalci, da matashin da ya tashi a cikin ibadar Allah, da mutumin da zuciyarsa take rataye da masallaci, da mutane biyun da suka yi soyayya saboda Allah, sun haxu saboda shi, sun rabu a kanshi (wato har rabuwa ta zo suna kan soyayyarsu saboda Allah) da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi, sai ya ce mata, ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka, ya voye ta har hannun dama bai san me hannun hagu ya bayar ba, da mutumin da ya ambari Allah shi kaxai, idanuwansa suka zubar da hawaye". Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

Da wannan hadisi zamu gane cewa 'yan uwantaka saboda Allah ni'ima ce babba daga wajen Allah, wani marmaron ruwa ne da Allah yake kwarara shi ga muminai masu gaskiya, kamar yadda 'yan uwantaka take wani ruwa ne mai tsarki da Allah yake shayar da bayinsa tsarkaka muminai. Allah Maxaukakin Sarki ya ce,

(إنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ فَأَصْلِحُوا بَيْنَ أَخَوَيْكُمْ وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ10) [الحجرات: 10]

“Kaxai muminai ‘yan uwan junane, ku daidaita tsakanin ‘yan uwanku. Ku ji tsoron Allah don ku samu rahama” (Al – hujrat : 10).

Allah ya yi mana Albarka cikin abin da muka ji na Alqur’ani mai girma, ya amfanar da mu da abin da yake cikinsa na ayoyi da zikiri mai girma, haqiqa Allah mai iko ne akan komai.

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (ﷺ) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Ya ‘yan uwa masu girma : Haqiqanin 'yan uwantakar musulunci ita ce take haxa abin da yake rabe, take haxe abin da ya sava, ita ce igiyar da take sanya taron al'ummar musulmi su zama kamar jiki xaya, ta mayar da su kamar gini, sashensa yana qarfafa shashe, irin wannan ‘yan uwantaka ita ce irin wadda take tsakanin Sahabban Manzon Allah (ﷺ), tsakanin mutanen Makka da Madina, har ya kasance mutum yana raba dukiyarsa ya ba xan uwansa rabi, ya saki matarsa don xan uwansa ya aura.

An karvo daga Anas – Allah ya yarda da shi – ya ce, Abdur-Rahman xan Auf ya zo wajenmu (a Madina) sai Annabi (ﷺ) ya haxa 'yan uwantaka tsakaninsa da Sa'ad xan Rabe'u, wanda yake yana da dukiya mai yawa. Sai ya ce wa Abdur-Rahman "Mutanen Madina sun san cewa ni ina cikin masu dukiya mai yawa, don haka sai raba dukiyata rabi, na baka, kuma ina da mata biyu, ka kalli wanda ta fi qayatar da kai, sai in sake ta, idan ta yi idda ka aura. Sai Abdur-Rahman ya ce, "Allah ya yi maka albarka a cikin dukiyarka da iyalanka, ku nuna min kasuwa". Ba a yi wasu kwanaki ba, sai ga Abdur-Rahman ya zo wajen Manzon Allah (ﷺ) da alamar turare a jikinsa, sai Manzon Allah ya ce masa, "Me ya faru ne?" sai ya ce, "Na auri wata mata daga cikin mutanen Madina". Sai Manzon Allah ya ce, "Me ka bata sadaki?" sai ya ce, "Mauni na zinare ko azurfa" sai Manzon Allah ya ce, "Yi walima, koda da akuya ne".

Allahu Akbar! Wannan ita ce 'yan uwantakar musulunci, ku duba ku ga yadda ta mayar da waxannan mazaje, dukiyarsu da iyalansu sun zama masu sauqi a wajensu don neman yardar Allah. Ko akwai wanda zai wa'azantu!?.

Ya 'yan uwa musulmi : Haqiqa hassada da qulli a zuciya suna cikin mafi haxarin cututtukan zuciya, waxanda suke rusa 'yan uwantaka, saboda hasada ita ce xan uwa ya ga xan uwansa a cikin ni'ima, sai ya qullace shi, ya yi masa hassada ya yi burin wannan ni'ima ta gushe daga xan uwanshi, ya manta da cewa Allah Maxaukakin Sarki shi ne wanda ya bashi wannan arziqin, don haka wanke zuciya daga hassada da qulli babbar lamari ne, kuma dalili ne daga cikin dalilan da shigar da mutum Aljanna.

Hadisi ya tabbata a cikin littafin (Al – Musnad) na Imam Ahmad daga Anas ya ce, Muna zaune a wajen Annabi (ﷺ) sai ya ce, "Yanzu wani mutum xan Aljannah zai vullo muku" sai wani mutum daga cikin mutanen Madina ya vullo, gemunsa yana xigar da ruwan alwalarsa, ya rataye takalmansa a hannun hagun xin sa. Da aka wayi gari, sai Annabi (ﷺ) ya sake faxin abin da ya faxa, sai wannan mutumin ya vullo kamar yadda ya vullo a karo na farko. A rana ta uku sai Manzon Allah ya sake faxin maganarsa ta farko, sai wannan mutumin ya vullo kamar yadda ya vullo a karo na farko. Da Manzon Allah (ﷺ) ya tashi, sai Abdullahi xan Amru xan Asi ya bi wannan mutumin, ya ce masa, na xan nisanci babana ne, na yi rantsuwa ba zai shiga inda yake ba har tsawon kwana uku, don haka idan ka ga da dama ka bani wuri har zuwa kwana ukun to ka ba ni, sai mutumin nan ya ce, to. Anas (mai riwaya) ya ce, Sai Abdullahi ya bamu labari ya ce "ya kwana tare da wannan mutum kwana uku, bai ga yana tsayuwar dare ba, sai dai idan ya farka da daddare ya juya akan shinfixarsa, ya yi kabbara, ya juya har zuwa lokacin sallar asuba. Abdullahi ya ci gaba da cewa "sai dai ban ji yana faxin komai ba sai alheri" da kwana uku suka wuce, sai na kusa in raina ayyukansa, sai na ce masa "Bawan Allah, babu wani abu na fushi qaura tsakanina da mahaifina, kurum na ji Manzon Allah (ﷺ) har sau uku yana cewa "wani mutum xan aljannah sai vullo muku yanzu" sai in ga ka vullo, har sai uku, don haka na so in zo inda kake don in ga aikin da kake, in yi koyi da kai, amma sai ban ga kana wani aiki mai yawa ba, meye ya kaika abin da Manzon Allah ya faxa?. Sai mutumin nan ya ce, "wannan abin da ka gani shi ne kawai" da na juya sai ya kira ni, ya ce da ni, "wannan abin ka gani shi ne kawai, amma fa bana xauke da alush ga wani daga cikin musulmi, kuma bana yi wa wani hassada akan alherin da Allah ya bashi" Sai Abdullahi ya ce, "Wannan shi ne ya kai ka wannan matsayi, kuma shi ne abin bama iyawa".

Yaku al'ummar Musulmi : Irin wannan ‘yan uwantaka ita ce take gadar da qarfi ga musulmi, su rinjayi duk wani kafiri maqiyin wannan addini mai girma. Sai dai abin baqin ciki a yau musulmi sun zama kamar sharar da ruwa ya xauko, sun warwatse, sun rarrabe, maqiya sun dira a kansu, su wawashe dukiyoyinsu, sun ci mutuncinsu, duk wannan ba don komai ba, sai dai watsar da ‘yan uwantaka da juna, da rashin kiyaye haqqin juna. Babu ko shakka ba yadda za a yi al’umma ta dawo da qarfinta da kwarjininta sai ta raya ‘yan uwantaka a tsakaninta, musulmi ya kiyaye haqqin xan uwansa musulmi. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa :

(وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَا تَنَازَعُوا فَتَفْشَلُوا وَتَذْهَبَ رِيحُكُمْ وَاصْبِرُوا إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ 46)[الأنفال: 46]

Ma’ana : “ Ku bi Allah da Manzonsa, Kada ku yi jayayya da juna, sai ku valvalce, qarfinku ya tafi, ku yi haquri, haqiqa Allah yana tare da masu haquri” (Al-anfal : 46).

Saboda haka wajibi ne mu taimaki junanmu, mu zama bayin Allah ‘yan uwan juna, kamar yadda Allah da Manzonsa suka umarce mu, haqiqa Allah yana tare da jama’a. kuma qarfi yana cikin haxuwa, rauni kuwa yana cikin rarrabewa da tarwatsewa. Allah ya tsare mu daga rabewa da savawa.