islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Falalar Wanda Ya Tabbatar Da Tauhidi


12260
Surantawa
Tauhidi shine babban ginshiqin da sammai da kassai suka tsayu akan shi, kuma ta dalilin shi ne aka halicci mutum da aljan, kuma aka aiko manzanni, kuma gwargwadon yadda mutum ya samar da tauhii da kyutata niyya ga Allah da nisantar shirkar zahiri da ta lungu, gwargwadon yadda zai sami amintuwa, da shiriya anan duniya da lahira.
P>Manufofin huxubar

Bayanin muhimmancin tauhidi da falalarsa.

Bayani kan cewa tauhidi shi ne sinadarin tsirar bawa ranar tashin qiyama, da kuma yafe masa laifukansa.

Bayani kan cewa tauhidi sababin juyar da bala’i da fitina ne.

Bayani kan muhimmancin sanin tauhidi, da kuma shirka da nau’ikanta.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ina yi muku wasiyya, da ni kaina, da tsoron Allah a voye, da kuma a fili. Sannan ku sani cewa, zuciyar mumini ba ta gyaruwa, sai da wani abu mai girma, kuma babu wanda zai kuvuta daga duniya, sai da tabbatar da shi. Allah ya yi bayanin sa a cikin littafinsa, kuma Manzon Allah (ﷺ) ya yi bayanin sa a cikin sunnarsa, bayani mai warkarwa, mai gamsarwa, shi ne kaxaita Allah mai girma, da bautata masa shi kaxai, babu mai tarayya da shi, da kuma tsantsanta aiki gare shi.

Tauhidi shi ne tushe mai girma, wanda sama da qasa suka tsaya a kansa. Ubangiji ya ce,

( لَوْ كَانَ فِيهِمَا آَلِهَةٌ إِلَّا اللَّهُ لَفَسَدَتَا فَسُبْحَانَ اللَّهِ رَبِّ الْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَ 22)[الأنبياء: 22]

(Da a ce akwai abubuwan bauta a cikinsu (sama da qasa), ba Allah ba, da sun vaci. Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin al-arshi, daga abin da suke siffantawa).

Saboda da shi ne aka halicci bil Adama da iskokai, kuma aka aiko manzanni, tsira da aminci su tabbata a gare su. Allah ya ce:

وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ56) [الذاريات: 56]) (Ban halicci aljannu da bil Adama ba, sai don su bauta mini).

Ma’ana, don su kaxaita ni.

Kuma saboda shi ne, har yau, aka halicci aljanna da wuta. Duk wanda ya tabbatar da shi, sannan ya mutu, zai shiga aljanna; duk wanda bai tabbatar da shi ba, ba zai shiga aljanna ba.

Daga Uthman, Allah ya yarda da shi, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Duk wanda ya mutu, alhali yana sanin cewa babu abin bautawa bisa cancanta, sai Allah, zai shiga aljanna.” [Muslim ya rawaito shi].Kuma saboda shi ne jihadi ya tsayu.

Tauhidi yana da falaloli masu yawa. Daga cikinsu: Lallai yana kankare laifuka, kuma yana hana ma’abocinsa ya dawwama a wuta. An rawaito daga Ubadah, Allah ya yarda da shi, daga Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Duk wanda ya shaida babu abin bauta bisa cancanta, sai Allah, halin kasancewarsa shi kaxai, babu mai tarayya da shi, kuma lallai Muhammad bawansa ne, Manzonsa ne, kuma Isa bawan Allah ne, Manzonsa ne, kuma kalmarsa ce da ya jefa wa Maryam, kuma ruhi ne daga gare shi. Kuma aljanna tabbas ce, kuma wuta tabbas ce, Allah zai shigar da shi aljanna, bisa abin da ya kasance na aiki.” [Bukhari ya ruwaito shi]

Kuma yana daga cikin falalarsa, da shi ne bawa yake kusantuwa zuwa ga Ubangijisa. Allah Ta’ala ya ce:

(إِنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللَّهِ الْإِسْلَامُ19) [آل عمران: 19]

(Haqiqa addini a wajen Allah, shi ne musulunci).

Kuma da shi ne cikakken aminci yake samuwa, da kuma cikakken shiriya ga bawa, a duniya da lahira. Ubangiji ya ce,

(الَّذِينَ آَمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ أُولَئِكَ لَهُمُ الْأَمْنُ وَهُمْ مُهْتَدُونَ82) [الأنعام: 82]

(Waxanda suka ba da gaskiya, kuma ba su cuxanya ban-gaskiyarsu da zalunci ba, irin waxannan suna da cikakken aminci, kuma su ne shiryayyu).

Kuma Allah ya ce,

(لَا يَحْزُنُهُمُ الْفَزَعُ الْأَكْبَرُ وَتَتَلَقَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ هَذَا يَوْمُكُمُ الَّذِي كُنْتُمْ تُوعَدُونَ 103)[الأنبياء: 103]

(Firgici mafi girma, ba ya baqanta musu zuciya, kuma mala’iku suna tarbar su, suna cewa, “Wannan shi ne yininku, wanda kuka kasance ana alqarwanta muku).

Kuma yana daga cikin falalar tauhidi, shi ne, gwargwadon yadda ka tabbatar da tauhidi, ka tsantsanta ibada ga Allah, kuma ka nesanci shirka ta fili da ta voye, gwargwadon yadda za ka samu aminci da shiriya. Don haka, za ka ga mumini, wanda ya kaxaita Allah, ya fi mutane samun aminci a duniya, kuma ya fi mutane samun aminci a lahira. Kamar yadda kuma, tauhidi sanadi ne na juyar da bala’i da fitintinu. Ubangiji yana cewa,

(إِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنْتُمْ لَهَا وَارِدُونَ98) [الأنبياء: 98]

(Lallai ku, da kuma abin da kuke bautawa, koma-bayan Allah, makamashin jahannama ne….” har a zuwa faxinsa, “Haqiqa waxanda kalmar yabo ta rigaya gare su, daga gare mu, su waxanda ake nesantawa ne daga gare ta).

Ga Annabin Allah, Ibrahim, badaxin Allah, Allah ya raba shi da wuta, a lokacin da aka jefa shi a cikin wuta. Ubangiji ya ce,

( قُلْنَا يَا نَارُ كُونِي بَرْدًا وَسَلَامًا عَلَى إِبْرَاهِيمَ69وَأَرَادُوا بِهِ كَيْدًا فَجَعَلْنَاهُمُ الْأَخْسَرِينَ 70 وَنَجَّيْنَاهُ وَلُوطًا إِلَى الْأَرْضِ الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا لِلْعَالَمِينَ 71 ) [الأنبياء: ٦٩ – ٧١].

(Muka ce, “Ya ke wuta! Ki zama sanyi da aminci a kan Ibrahim. Kuma suka nufi kaidi a gare shi, sai muka tseratar da shi, da Annabi Luxu, zuwa qasa wadda muka sanya albarka a cikinta ga talikai).

Ya ku bayin Allah! Lallai mafiya shiriya cikin mutane, kuma mafiya samun aminci a cikinsu, su ne annabawa da manzanni, saboda tabbatar da tauhidi da suka yi, da kuma tsantsanta bautarsu ga Allah. Ga Annabi Dawud, Allah Ta’ala ya siffanta shi da komawa zuwa gare shi. Ya ce,

(اصْبِرْ عَلَى مَا يَقُولُونَ وَاذْكُرْ عَبْدَنَا دَاوُودَ ذَا الْأَيْدِ إِنَّهُ أَوَّابٌ17) [ص: 17]

(Ka yi haquri a kan abin da suke faxa, kuma ka ambaci bawanmu Annabi Dawud, ma’aboci qarfi. Lallai shi mai yawan komawa ne zuwa ga Allah).

Ku sani, ya bayin Allah, tauhidi ya kasu zuwa gida uku: Tauhidin kaxaita Allah da aikinsa; tauhidin kaxaita Allah da aikin bayi, wato ibada; da tauhidin kaxaita Allah cikin sunayensa da siffofinsa. Haqiqa Allah ya haxa waxannan nau’ika guda uku, a cikin faxinsa,

رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا فَاعْبُدْهُ وَاصْطَبِرْ لِعِبَادَتِهِ هَلْ تَعْلَمُ لَهُ سَمِيًّا 65[مريم: 65]

(Ubangijin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu, ka bauta masa, ka jure wa ibadarsa. Shin ka san wani a matsayin takwara gare shi?).

Kuma tabbatar da tauhidi da rabe-rabensa guda uku, ya zo da dama a cikin Alqur’ani mai girma. Daga ciki, akwai faxinsa,

(قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ 1 اللَّهُ الصَّمَدُ 2 لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ 3 وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ 4) [الإخلاص: ١ – ٤].

(Ka ce, “Shi Allah, shi kaxai ne. Allah wanda ake buqatuwa zuwa gare shi, bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani da ya zama tamka gare shi).

Kuma Allah ya ce,

(اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَأَنْزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجَ بِهِ مِنَ الثَّمَرَاتِ رِزْقًا لَكُمْ وَسَخَّرَ لَكُمُ الْفُلْكَ لِتَجْرِيَ فِي الْبَحْرِ بِأَمْرِهِ وَسَخَّرَ لَكُمُ الْأَنْهَارَ 32وَسَخَّرَ لَكُمُ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ دَائِبَيْنِ وَسَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ33وَآَتَاكُمْ مِنْ كُلِّ مَا سَأَلْتُمُوهُ وَإِنْ تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللَّهِ لَا تُحْصُوهَا إِنَّ الْإِنْسَانَ لَظَلُومٌ كَفَّارٌ34 ) [إبراهيم: ٣٢ – ٣٤].

(Allah wanda ya halicci sama da qasa, kuma ya saukar da ruwa daga sama, sannan ya fitar da ‘ya’yan itatuwa da shi, don arziki gare ku, kuma ya hore jiragen ruwa, don su gudana a cikin teku, da izininsa, ya kuma hore muku qoramu. Kuma ya hore muku rana da wata masu gudu ba qaqqautawa, kuma ya hore muku dare da yini. Kuma ya ba ku daga duk abin da kuka roqe shi. Kuma idan za ku lissafa na’imar Allah to ba za ku iya qididdige ta ba. Lallai xan Adam mai yawan zaluntar kansa ne, mai yawan butulci).

Kuma Allah ya ce,

( لَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ وَهُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ 11 ) [الشورى: ١١].

(Babu wani abu da yake kamarsa, kuma shi mai ji ne, mai gani ne).

An karvo daga Abu Huraira, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ubangiji ya ce, “Ka ciyar, zan ciyar da kai.” Kuma ya ce, "Hannun Allah a cike yake, ciyarwa ba ta tauye shi, mai yaye dare da rana. Ya ce, “Ku ba ni labari kan abin da Allah ya ciyar, tunda ya halicci sama da qasa. Lallai haka bai tauye abin da yake hannunsa ba. Kuma al-arshinsa ya kasance a kan ruwa, sikeli yana hannunsa, yana saukar da shi, yana xaga shi.” [Bukhari ya ruwaito shi].

Allah ya yi albarka gare ni, tare da ku, cikin Alqur’ani mai girma, kuma Allah ya amfanar da ni, da ku, da abin da yake cikinsa, na ayoyi da tunatarwa mai azanci. Shi majivincin haka ne, kuma mai iko a kan haka.

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, kuma tsira da aminci su tabbata ga mafi xaukakar Annabawa da Manzanni, Annabinmu, Muhammad, da iyalensa da sahabbansa gabaxaya.

Bayan haka, ya ‘yan uwa! Lallai tauhidi yana da abubuwan da suke warware shi masu yawa, wajibi ne a kan mutum ya yi taka-tsantsan da su, saboda aukawa cikinsu, yana warware tauhidi, kuma sanadi ne na shigar mutum wuta. Daga ciki, akwai shirka da rabe-rabenta. Babbar shirka tana warware tauhidi gabaxaya. Qaramar shirka kuma tana warware cikar tauhidi.

Haka nan, roqon wanin Allah buqatar da Allah kaxai yake da ikon yin ta, kamar mutum ya nemi aljani ko waliyyi ko shehi, ya yaye masa cuta, ko ya jawo masa amfani, wannan shirka ce mai girma, wadda take warware tauhidi baki xaya. Haqiqa Manzon Allah (ﷺ) ya nuna cewa, adu’a ibada ce, kamar yadda ya ce, “Adu’a ita ce ibada.” [Tirmizi da Ahmad suka rawaito] Hakanan, yana daga shirka babba, abin da mutane suke yi a yau, na xawafi da duqufa a kan qaburan bayin Allah na qwarai, da kuma neman biyan buqata daga gare su, koma-bayan Allah. Allah Ta’ala ya ce,

) وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنْ يَدْعُو مِنْ دُونِ اللَّهِ مَنْ لَا يَسْتَجِيبُ لَهُ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ وَهُمْ عَنْ دُعَائِهِمْ غَافِلُونَ([الأحقاف: 5]

(Wanene ya fi vata, sama da wanda yake roqon wani koma-bayan Allah, wanda ba zai amsa masa ba, har tashin qiyama, su sun shagala ga barin addu’arsu su?).

Daga ciki, akwai zuwa wajen bokaye, da ‘yan tsibbu, da ‘yan duba, da kuma gaskata su cikin abin da suke faxi na da’awar sanin gaibu. Ubangiji Ta’ala ya ce,

) وَإِنْ يَمْسَسْكَ اللَّهُ بِضُرٍّ فَلَا كَاشِفَ لَهُ إِلَّا هُوَ وَإِنْ يَمْسَسْكَ بِخَيْرٍ فَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ 17 ( [الأنعام: ١٧].

(Idan Allah ya shafe ka da cuta, babu mai yaye ta, sai shi, idan kuma ya shafe ka da alheri, to shi mai iko ne a kan komai).

Daga ciki, akwai shirka ta nufin wanin Allah, kamar mutum ya nufi duniya, ko son a sani, ko a gani, da aikinsa. Allah Ta’ala ya ce,

) مَنْ كَانَ يُرِيدُ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيْهِمْ أَعْمَالَهُمْ فِيهَا وَهُمْ فِيهَا لَا يُبْخَسُونَ15 أُولَئِكَ الَّذِينَ لَيْسَ لَهُمْ فِي الْآَخِرَةِ إِلَّا النَّارُ وَحَبِطَ مَا صَنَعُوا فِيهَا وَبَاطِلٌ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ16 ([هود: ١٥ – ١٦].

(Duk wanda yake nufin rayuwar duniya da adonta, za mu cika musu ayyukansu a cikinta, su ba za a tauye su a cikinta ba. Irin waxannan ba su da komai a lahira, sai wuta, abin da suka aikata a cikinta ya rushe, kuma abin da suka kasance suna aikatawa lalatacce ne).

Daga ciki, akwai shirka ta biyayya. Ita ce biyayya ga abin halitta wajen halatta abin da Allah ya haramta. Allah Ta’ala ya ce,

) اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ 31 ) [التوبة: ٣١].

(Sun riqi malamansu, da masu bautarsu, iyayen giji, koma-bayan Allah).

Kamar yadda Annabi (ﷺ) ya fassara wa Adiy xan Hatim, lokacin da ya tambaye shi. Ya ce, “Ba ma bauta musu!” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya nuna masa cewa, bautar ita ce, yi musu biyayya a kan savon Allah, da janja hukuncin Allah. Ya ce, “Ba suna haramta abin da Allah ya halatta ba, sai kuma ku xauke su a matsayin haram, kuma suna halatta abin da Allah ya haramta, sai ku xauke shi a matsayin halal?” Sai ya ce, “Na’am!” Sai ya ce, “Wannan ita ce bauta musu.” [Tirmizi da Xabarani suka rawaito shi].

Daga cikin akwai shirka ta soyayya wadda take tilasta girmamawa da rusunawa da qasqantar da kai, wanda ba su cancanta a yi su ba, sai ga Allah shi kaxai. Duk sanda bawa ya yi irin wannan soyayya ga wanin Ubangiji, to haqiqa ya yi shirka mai girma. Ubangiji yana cewa,

) وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَتَّخِذُ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَنْدَادًا يُحِبُّونَهُمْ كَحُبِّ اللَّهِ وَالَّذِينَ آَمَنُوا أَشَدُّ حُبًّا لِلَّهِ ( [البقرة: ١٦٥].

(Daga cikin mutane, akwai waxanda suke riqar kishiyoyi koma-bayan Allah, suna son su, kamar yadda suke son Allah. Su kuwa waxanda suka yi imani, sun fi tsananin soyayya ga Allah).

Ya ku bayin Allah! Ku sani cewa, Allah Tabaraka Wa Ta’ala, ba ya gafarta a yi shirka da shi. Ubangiji ya ce,

) يُرِيدُ اللَّهُ أَنْ يُخَفِّفَ عَنْكُمْ وَخُلِقَ الْإِنْسَانُ ضَعِيفًا ( [النساء: ٤٨].

(Lallai Allah ba ya gafarta a haxa wanin Allah da shi, amma yana gafarta abin da yake koma-bayan haka, ga wanda ya so).

Kuma ya ce,

)حُنَفَاءَ لِلَّهِ غَيْرَ مُشْرِكِينَ بِهِ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَكَأَنَّمَا خَرَّ مِنَ السَّمَاءِ فَتَخْطَفُهُ الطَّيْرُ أَوْ تَهْوِي بِهِ الرِّيحُ فِي مَكَانٍ سَحِيقٍ 31 ( [الحج: ٣١].

(Duk wanda ya haxa wani da Ubangiji, to kamar wanda ya faxo daga sama ne, sai tsuntsaye suka wabce she, ko iska ta yi wurgi da shi a wani waje mai nisa).

Kuma Ubangiji ya ce,

)إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَارٍ 72( [المائدة: ٧٢].

(Duk wanda ya haxa Allah da wani, haqiqa Allah ya haramta masa shiga aljanna, kuma makomarsa ita ce wuta, kuma azzalumai ba su da mataimaka).

Idan Allah ba ya yarda da shirka, sai dai tauhidi, kuma ba ya gafarta shirka, to lallai azabar masu yin shirka, mai girma ce. Azabarsu ita ce wuta, azabarsu ita ce wulaqanci a duniya da lahira. Waye a cikinmu - ya bayin Allah - ba ya son kuvuta a duniya da lahira? Waye a cikinmu, ba ya son ya shiga aljanna ba tare da hisabi ko azaba ba? Waye a cikinmu, ba ya son ya rayu, rayuwa mai daxi a duniya, kuma ya kuvuta ranar da dukiya da ‘ya’ya ba sa amfani?

Saboda haka, ku lazimta wa kanku tabbatar da tauhidi ga Allah, da tsantsanta bauta gare shi. Kuma ku koyi hakan, kuma ku kula da abin da malaman musulunci da jagororin sunna da jagororin wannan kira suka rubuta a kan waxannan manya-manyan mas’aloli na tauhidi. Domin, duba littattafan tauhidi, haske ne a cikin zukata, kuma shiriya ce ga rayuwa, kuma a cikin tauhidi nagarta take ga xaixaikun mutane da al’umma. Kada duniya ta shagaltar da kai ga barin wannan tushe mai girma, wanda ya tattare komai da komai, wanda saboda shi aka aiko Annabawa da Manzanni, kuma saboda shi aka halicci aljanna da wuta. Ku bai wa tauhidi haqqinsa, kuma ku gabato wajen koyon sa, tun daga wannan lokacin, tare da niyya ta gaskiya. Ku koyi tauhidi a dunqule, da kuma a rarrabe, don kada ku auka cikin abinn da mafi yawan mutane suka auka ciki na jahilci ko barin tauhidi.

Ina roqon Ubangiji, ya inganta mana niyyoyinmu, ya kuma inganta mana addininmu, ya kuma inganta mana duniyarmu. Lallai shi mai kyauta ne, mai karamci.