islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Girmamawar da musulunci yayi wa ya mace


10456
Surantawa
Haqiqa ya mace a lokacin Jahiliyya ta zama kamar wani kaya na sayar wa da bai da qima har saida musulunci yazo ya karrama ta irin karamcin da babu irin shi.ya tsamar da ita daga duhun zaluncin jahiliyya. Ya dawo mata da hakkokinta,ya daidaita ta da da-namiji a da dama daga cikin wajibban addini, da cikin lada da uquba. Don haka bata sami karamci ba da girmamawa kwatankwacin wanda ta samu a addinin musulunci
huxuba ta

Manufofin huxubar

Bayanin halin da mace take ciki kafin zuwan musulunci.

Bayanin yadda musulunci ya xaukaka darajar ‘ya mace.

Bayanin cewa musulunci ya daidaita mace da namiji a wasu vangarori.

Fito da wuraren da musulunci ya girmama ‘ya mace a cikinsu.

Ba da amsa ga masu cewa Musulunci ya tauye wa mata haqqi.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka : ‘Yan uwa musulmi : Huxubarmu a yau tana magana ne a kan wani maudu’i da ya shagaltar da duniya gaba xaya, kuma a dalilinsa aka jingina wa musulunci da musulmai ci baya da qauyanci, , aka tuhunci musulunci da qare – qaraki da yawa, masu sharri da varna suka xauki wannan maudu'i qofa ce ta vatar da mutane da yaudararsu da kange su daga hanyar Allah, wannan maudu’i shi ne bayanin matsayin ‘ya mace a addinin musulunci.

Babu yadda zamu san irin girmamawa da musulunci ya yi wa ‘ya mace sai mun koma baya, mun san matsayinta a lokacin jahiliyya kafin zuwan musuluncin.

Haqiqa ‘ya mace a lokacin Jahiliyya ta zama kamar wani kaya na sayar wa da bai da qima da daraja, har ya kai idan an haifa wa mutum ‘ya mace yana baqin ciki, yana qin ta, ba ma ya son ya haxa ido da mutane saboda kunya da damuwa, daga nan sai ya shiga tunanin xayan abubuwa biyu : kodai ya riqe ta a wulaqance, ya yi haquri da duk irin wulaqancin da mutane za su yi masa, ko kuma ya yi mata mummunan kisa, ya binneta da ranta, kamar yadda Allah ya bada labari inda yake cewa :

(وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُمْ بِالْأُنْثَى ظَلَّ وَجْهُهُ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌ58 يَتَوَارَى مِنَ الْقَوْمِ مِنْ سُوءِ مَا بُشِّرَ بِهِ أَيُمْسِكُهُ عَلَى هُونٍ أَمْ يَدُسُّهُ فِي التُّرَابِ أَلَا سَاءَ مَا يَحْكُمُونَ59) [النحل: ٥٨ - ٥٩].

Ma’ana : “Idan an yi wa xayansu bushara da ‘ya mace, sai fuskarsa ta yi baqiq qirin yana mai fushi, yana voye wa mutane saboda munin abin da aka yi masa bushara da shi, (ya riqa tunani cewa) zai riqe ta ne a wulaqance ko kuwa ya turvuxeta ne a cikin qasa, ku saurara abin da suke hukunta wa ya yi muni”. (Annahal : 58 – 59).

Don haka Allah ya bada labarin cewa zai bi wa wannan da aka zalunta haqqinta daga wanda ya zalunce ta bada wani haqqi ba, Allah ya ce,

(وَإِذَا الْمَوْءُودَةُ سُئِلَتْ8 بِأَيِّ ذَنْبٍ قُتِلَتْ9) [التكوير:8-9]

Ma’ana : “Idan aka tambayi wadda aka binne da ranta. Da wane laifi ne aka kashe ta” (At – Takwir : 8 – 9).

Idan kuwa ba su kashe ta ba, sai su wulaqantar da ita idan ta girma, ba sa bata gado, suna sanya ta cikin kayan da ake gada, Imamul Bukhari – Allah ya yi masa rahama – ya rawaito daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Sun kasance idan mutum ya mutu, waliyyansa suke da haqqi a kan matarsa, idan sun ga dama wasu cikinsu su aure ta, ko su aurar da ita, idan kuma sun ga dama ba za su aurar da ita ba, suna ganin su suka fi cancanta da riqe ta fiye da danginta”, sai aya ta sauka da cewa :

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا لَا يَحِلُّ لَكُمْ أَنْ تَرِثُوا النِّسَاءَ كَرْهًا19) [النساء:19].

Ma’ana : “Ya ku waxanda kuka yi imani ba ya halatta ku gaji mata a kan dole”.

Hakanan a lokacin jahiliyya mutum yana iya auren mata da yawa ba adadi, ya munana musu mu’amala. Da musulunci ya zo zai ya haramta haxa mata fiye da huxu a lokaci guda, ya kuma sanya sharaxin haxawar shi ne idan zai yi adalci tsakaninsu, Allah ya ce,

(وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَى فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ مَثْنَى وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ3) [النساء: ٣].

Ma’ana : “Ku auri abin da ya yi muku daxi na mata, bibiyu, ko uku – uku ko hurhuxu, idan kuna jin tsoron ba za ku yi adalci ba to ku auri xaya, ko (ku wadatu) da abin da damarku ta mallaka”. (Annisa’i : 3).

Idan kuwa mutum ya mutu to shekara guda matarsa zata yi, tana masa takaba, babu fita. Hakanan namiji yana iya sakin matarsa ba tare da wani adadi ba, in ya sake ta, sai ya qyale ta sai ta kusa gama idda sai ya dawo da ita, sai kuma ya qara sakinta, sai ta kusa gama idda sai ya sake dawo da ita, haka zai ta yi. Har sai da Allah ya qayyade adadin saki biyu da mutum zai iya mayar da matansa a cikinsu.

Wannan shi ne irin yanayin da ‘ya mace take rayuwa a cikinsa a jahiliyya kafin zuwan musulunci, kuma haka halinta yake a wurin sauran al’ummu, har musulunci ya zo mace tana cikin irin wannan yanayi da hali, musulunci ya kuvutar da ita, ya karramata, ya kiyaye mata haqqoqinta, ya daidaita ta da xa namiji a wurare da yawa a cikin wajibai na addini, da barin haramun, da wajen bada lada da azaba, Allah ya ce, :

(مَنْ عَمِلَ صَالِحًا مِنْ ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَى وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُ حَيَاةً طَيِّبَةً وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُمْ بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ97) [النحل: 97]

Ma’ana “Wanda ya yi aiki na qwarai daga namiji ko mace yana mumini to zamu raya shi rayuwa mai daxi, kuma zamu saka musu da mafi kyau abin da suke aikatawa” (Annahal : 97).

Allah ya sake faxa a wani wurin ya ce, :

(إِنَّ الْمُسْلِمِينَ وَالْمُسْلِمَاتِ وَالْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَالْقَانِتِينَ وَالْقَانِتَاتِ وَالصَّادِقِينَ وَالصَّادِقَاتِ وَالصَّابِرِينَ وَالصَّابِرَاتِ وَالْخَاشِعِينَ وَالْخَاشِعَاتِ وَالْمُتَصَدِّقِينَ وَالْمُتَصَدِّقَاتِ وَالصَّائِمِينَ وَالصَّائِمَاتِ وَالْحَافِظِينَ فُرُوجَهُمْ وَالْحَافِظَاتِ وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُمْ مَغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا35) [الأحزاب: 35]

Ma’ana : “Haqiqa musulmai maza da musulmai mata, muminai maza da muminai mata, masu qasqantar da kai maza da masu qasqantar da kai mata, masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, masu haquri maza da masu haquri mata, masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, masu sadaka maza da masu sadaka mata, masu azumi maza da masu azumi mata, masu kiyaye farjinsu maza da masu kiyaye farjinsu mata, masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambaton Allah da yawa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma”. (Ahzab : 35).

Allah Maxaukakin Sarki ya fifita namiji ne akan mace a wasu wurare, saboda wasu dalilai da hikimomi da suka sanya hakan, kamar a wajen gado, da shaida da diyya da zaman gida da wajen saki, saboda xa namiji yana da tsarin halittar da ‘ya mace ba ta da shi, yana xaukar nauyin a rayuwa wanda mace ba ta xaukan wannnan nauyin, kamar yadda Allah ya ce, :

(الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْضٍ وَبِمَا أَنْفَقُوا مِنْ أَمْوَالِهِمْ34) [النساء: ٣٤]

Ma’ana : «Maza sune a tsaye akan mata saboda abin da Allah ya fifita sashensu akan sashe da kuma abin da suka ciyar daga dukiyoyinsu» (Annisa’i 34). Ya sake cewa :

(وَلِلرِّجَالِ عَلَيْهِنَّ دَرَجَةٌ228) [البقرة: ٢٢٨].

Ma’ana : «Maza suna da daraja akan mata» (Baqara : 228). Haka ma Allah ya sanya wa ‘ya mace rabo a cikin gado, ya ce, :

(لِلرِّجَالِ نَصِيبٌ مِمَّا تَرَكَ الْوَالِدَانِ وَالْأَقْرَبُونَ وَلِلنِّسَاءِ نَصِيبٌ مِمَّا تَرَكَ الْوَالِدَانِ وَالْأَقْرَبُونَ مِمَّا قَلَّ مِنْهُ أَوْ كَثُرَ نَصِيبًا مَفْرُوضًا7) [النساء: 7]

Ma’ana : “Maza suna da rabo cikin abin da iyaye da makusanta suka bari, haka ma mata suna rabo cikin abin da iyaye biyu da makusanta suka bari, daga cikin abu mai yawa ko kaxan, rabo ne yankakke”. (Annisa’i 7). Sannan Allah ya ba ‘ya mace damar mallaka da sadaka da damar ‘yanta wa kamar yadda namiji yake da irin wannan damar, Allah ya ce a cikin ayar da ta gabata «Da masu sadaka maza da masu sadaka mata» ya sanya mata haqqin zamar miji, ba za a yi mata aure ba yardar ta ba. Musulunci ya kareta daga wulaqanta wa, ya hana waxanda suke so su cutar da ita, waxanda suke so su ji daxi da ita ba hanyar shari’a ba. Haka mace take rayuwa a qarqarshin inuwar musulunci da girmamawarsa, ko dai ta zama mata, ko ‘yar uwa tana aikinta a rayuwa wanda Allah ya xora mata. Wannan shi ne matsayin mace a musulunci, addinin rahama da jin qai da kamala.

To abin tambaya a nan ina ne addinin musulunci ya wulaqanta ‘ya mace, ko ya rage mata qima da daraja? Yanzu duk waxannan abubuwan da suka gabata ba girmamawa ba ce da xaukakawa ba? Don haka waxanda suke maimaita maganar maqiya Allah masu cewa musulunci ya zalunci mace su ji tsoron Allah.

Yaku ‘yan uwa musulmi : Ku duba matsayin mace a wajen waxancan al’ummu da suke kushe musulunci da cewa ya zalunci ‘ya mace, ya qwace mata haqqi, ku saurara ku ji matsayinta a wurinsu, ku auna ku gani shin akwai wata girmamawa?.

Matsayin Mace a wurinsu a yau, ya fi matsayinta a jahiliyya muni, sun maida ‘ya mace ta zama araha ana fito da ita tsirara gaban maza, a wuraren da suke taruwa, sun maida su masu hidima a cikin gidaje, ma’aikata a ofisoshi, masu jinyar marasa lafiya a asibitoci, masu tarban mutane a hotels da wuraren sayar da abinci, masu karantar da maza a makarantu, ‘yan wasan kwaikwayo a gidajen sinima. Haqiqa sun zalunci ‘ya mace, sun hanata haqqinta na tsayuwar xa namiji a kanka wajen ciyarwa da kula da ita, sun rabata da matsayinta a gida da tarbiyyar yara, da samar da iyali, haka suka yanke mata duk wani taimako da zai taimaka mata wajen aikinta da Allah ya halicceta da shi, har sai da suke takura mata ta fito don neman abin da zata ci, ta hanyar sayar da mutuncinta ga duk wani fajiri, suka xora mata aikin maza, suka rabata da sitira, suka bar ta tsirara tana bayyana wuraren kyau a jikinta, suka jefata cikin cakuxuwa da maza, har ta zama abin kwaxayin duk wani mai kwaxayi, sun haramta abin da Allah ya halatta, suka halatta abin da Allah ya haramta a cikin haqqin mace, sun hana auren mace fiye da xaya, wanda hakan shi ne haqiqanin maslaha ga mata, saboda namiji zai xauki nauyin wani adadi na mata, domin abu sananne cewa adadin mata ya fi na maza a yawa a wurare da dama, amma sai suka taqaita namiji akan mace xaya, sauran matan kuwa suka bar su ga mavarnata, suna cin abinci ta hanyar sayar da mutuncinsu, ko kuma suna aiki mai wahala, sun xaixaita su suna neman aikin da za su rayu da shi, koda kuwa a wasu garuruwa ne masu nisa da garinsu.

Haka maqiya Allah maqiya ‘yan adam suka raba ‘ya mace daga dukkan wani taimakon da zai sa ta rayu rayuwar arziqi, suka savuleta daga dukkan haqqinta na yau da kullum, don su mayar da ita hanyar varna da lalacewa.

Zaku mamaki – Yaku bayin Allah – idan ku sani cewa duk da waxannan laifuffukan da maqiya Allah suka yi wa mata, suna da’awar sune masu taimaka wa mata, masu kare musu haqqi, masu neman a basu haqqinsu, wani abin mamakin ma shi ne wai har a samu musulmi su zama bakunansu suna maimata abin da suke faxa, suna yaxa maganganunsu a jaridu da kafafen yaxa labarai, suna maimaita maganganun da aka faxa musu ba tare da sun san ma’anarsu ba.

Allah ya yi mana albarka cikin abin da muka ji, na alqur’ani da hadisi, haqiqa Allah mai iko ne akan dukkan komai.

huxuba ta biyu

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (ﷺ) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Yaku mutane : ku ji tsoron Allah dangane da matanku, haqiqa ku an baku kiwo ne, ku sani cewa duk wani abin da ya faru garesu, ku ne abin tambaya. Amma abin baqin ciki muna jin irin munanan yanayi da wasu mata suke ciki a gidajensu da unguwanninsu, daga cikin irin waxannan hali : akwai sakaci da hijabi, musammam ma ‘yan matan da suka saba fita, suna fita da kaya matsatstsu, waxanda suke siffata jikinsu, yin haka sava wa Allah ne, kuma cin amana ne!.

Ku sani – Yaku magidanta – cewa musulunci ya sanya lada mai yawa akan tarbiyyar ‘ya ‘ya mata. An karvo daga Uqbatu xan Amir – Allah ya yarda da shi – ya ce, naji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : “Duk wanda yake da ‘ya ‘ya mata guda uku, kuma ya yi haquri da su, ya tufatar da su daga samunsa, za su zamar masa kariya daga wuta”. Bukhari ne ya rawaito shi a cikin (Al’adab) Sheikh Albani ya inganta shi.

Haka ma An karvo daga Jabir xan Abdullahi – Allah ya yarda shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wanda yake da ‘ya ‘ya mata guda uku, ya zama yana mai tattaro su, yana isar musu abin da suke nema, yana tausayinsu, to ya wajaba ya shiga Aljannah” sai wani mutum ya ce, “ko guda biyu ne ya Rasulallahi? Sai ya ce, “Ko da biyu ne”. Bukhari ya rawaito shi a cikin littafinsa (Al-Adabul Mufrad).

Don haka ku ji tsoron Allah ya waxanda Allah ya xora wa nauyin kula da mata, ku kula da tarbiyyar ‘ya ‘yanku mata, zaku rabauta, ku azurta duniya da lahira. Ku kiyaye wasiyyar Allah da Manzon Allah (ﷺ) suka yi akan kula da lura da mata.

Sannan ina kira ga ‘yar uwa musulma da ki riqe addininki, addinin da Allah ya girmamaki da shi, ya xaukaka matsayinki da shi, ya tsamo ki da shi daga faxawa da gangarawa zuwa ga halaka, da faxawa gaban mutanen da suke dabbobi, ku tuna – yake baiwar Allah – a koyaushe meye matsayinki kafin zuwan musulunci, da matsayinki a yau a qasashen kafirai.

Ki sani da’awar ci gaba da ‘yancin mace ba zata kawo miki alheri ba, kaxai zata haifar miki da tavewa da shiga uku. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa : “Wanda duk ya yi aiki nagari daga namiji da mace yana mai imani to zamu raya shi kyakkyawar rayuwa, kuma zamu saka musu ladansu daga mafi kyan abin da suke aikatawa” (Annahal : 98).

Ki tuna – yake baiwar Allah – irin yadda Allah Maxaukakin Sarki ya fifita wasu mata saboda biyayyarsu ga Allah da Manzonsa (ﷺ) Ki duba Nana Khadija Allah Ta’ala yake aiko mata da gaisuwa.

An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Mala’ika Jibrilu ya zo wajen Annabi (ﷺ) ya ce, ya Manzon Allah, ga khadija nan ta zo, tana xauke da kwano da abinci a ciki ko abin sha, idan ta zo wajenka, ka isar mata gaisuwa daga Ubangijinta, da kuma daga gareni, ka yi mata bushara da gida a Aljanna na azurfa, wanda babu hayaniya da wahala a cikinsa”. Bukhari ne ya rawaito shi.

Yaku Musulmi : Daga abin da ya gabata zamu gane cewa musulunci addini ne mai girma kuma gamamme da ya haxa komai da komai, babu zalunci ko tawaya cikin abin da Allah ko Manzonsa suka saukar. Musulunci shi ne addinin kaxai ya girmama xan adam ya xaukaka martabarsa.

Don haka wajibi ne akan malamai su tashi su bayyyana wa mutane haqiqanin wannan addini mai girma, ba a vatar da wasu matan ba sai saboda jahilcinsu ga addininsu da abinda yake cikinsa na gyara da xaukaka. Allah ya datar damu.