islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Nasiha da amana


21431
Surantawa
Nasiha itace kashin-bayan addini, domin addinin gaba dayan shi nasiha ne, kuma nasiha tana kasancewa ne ga Allah, da manzonsa, da shuwagabannin musulmi, da gama-garinsu. Dukkan sanda mutum yayi nasiha game da wadannan abubuwa, ta addini ya cika, kuma duk wanda yayi sakaci wajaen nasiha ga wani cikin wadannan abubuwa, to haqiqa addininsa ya samu tawaya gwargwadon sakacinsa. Don haka wajibi ne musulmi ya lura da amana wajen nasihar da ze gabatar, da bayanin gaskiya ba tare da yin kara ba ga kowaye, domin shi yana cikin kariyar Allah.

Manufofin huxubar

Bayyana cewa addini nasiha ne.

Bayanin me ake nufi da nasiha.

Bayanin ma’anar amana da yadda ake kiyayeta.

Bayanin falalar nasiha da yadda ake yin ta.

Tsoratarwa akan sakaci da amana da yin nasiha.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

‘Yan uwana musulmi a yau huxubarmu tana magana ne akan wata matashiya mai girma, wadda dukkan musulmi da musulma suke da buqatar ta, kuma Manzon Allah (ﷺ) ya siffata ta da cewa itace addini gaba xaya, sannan wannan matashiya ita ce aikin annabawa gabaxayansu, wannan matashiya kuwa ita ce Nasiha.

Abin da ake kira nasiha shi ne nufin mutum da alheri kamar yadda Imamul Khaxxabi da waninsa suka faxa. Nasiha ita ce tushen wannan addini, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : “Addini nasiha ne, addini nasiha ne, addini nasiha ne, sai muka ce “ga wa?” Sai ya ce, “Ga Allah, ga littafinsa, ga Manzonsa, ga shugabannin musulmi, da sauran da gama - garinsu”. A duk lokacin da bawa ya yi nasiha ga waxannan abubuwa to ya cika addini, wanda duk kuwa ya gaza nasiha ga wani abu daga cikin waxannan abubuwa, haqiqa ya rasa wani abu na addininsa gwargwadon abin da ya gaza a cikinsa.

Nasiha ga Allah ita ce imani da shi, tsarkake zuciya yayin bautarsa, da gaskiyar nufi wajen neman yardarsa, ta yadda mutum zai zama haqiqanin bawa ga Allah, mai yarda da abin da ya hukunta, mai wadatuwa da abin da ya bayar, mai kamanta umarninsa, mai nisantar son zuciyarsa, mai tsarkake gaba xayan addini gare shi, ba ya nufin riya ko son a ji.

Nasiha ga littafin Allah ita ce, karanta shi, da kamanta umarninsa, da nisantar abubuwan da ya hana, da gasgata labaransa, da ba shi kariya daga canzawar masu canzawa da karkacewar karkatattu, da qudurce wa shi zancen Allah ne, ya jefa shi ga Jibrilu, shi kuma ya sauka da shi ga Manzon Allah (ﷺ).

Nasiha ga Manzon Allah (ﷺ) tana nufin qauna da so gare shi, biyayya gare shi a fili da voye, taimakonsa yana rai ko bayan ya bar duniya, gabatar da maganganunsa da shiriyarsa a kan magana da shiriyar kowane mutum.

Nasiha ga shugabannin musulmi kuwa ita ce, yin biyayya da gaskiya gare su, da shriyar da su zuwa ga abin da yake alheri ne ga al'umma cikin addininta da duniyarta, da taimakonsu wajen yin aiki da haka, yi musu xa’a da biyayya akan duk abin da suka umarta, matuqar ba su umarni da savon Allah ba. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, :

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ59) [النساء: ٥٩ ].

Ma’ana : «Yaku waxanda kuka yi imani, ku bi Allah, ku bi Manzo da ma’abota al’amari a cikinku».

Nasiha ga sauran gama – garin musulmi ita ce, ka so musu irin abin da kake so wa kanka, ka vuxe musu qofofin alheri ka kwaxaitar da su a kanta, ka rufe musu qofofin sharri tare da tsoratar da su daga barinsu, ka yi soyayya da ‘yan uwantaka tsakaninka da muminai, ka yaxa kyawawan ayyukansu, ka suturta munanan ayyukansu, ka taimaki wanda aka zalunta a cikinsu, da wanda yake zaluncin, ka taimaki wanda aka zalunta ta hanyar kare shi daga zalunci, shi kuma wanda yake zaluncin da taimake shi ta hanyar hana shi zaluncin.

A duk lokacin da al’umma suka tsaya a kan waxannan abubuwa, nasiha ga Allah, ga littafinsa, ga Manzonsa, ga shugabannin musulmi da sauran musulmin, to zasu rayu rayuwa mai kyau abar yabo.

Bayin Allah : Daga abin da ya gabata zai bayyana garemu cewa nasiha ta haxa addini gaba xayansa, tushensa da reshensa, haqqoqin Allah da Manzonsa, da haqqoqin bayin Allah. Sai dai abin tambaya a nan shi ne :

Ina nasiha ga wanda ya tozarta haqqoqin Allah, ya kutsa cikin abubuwan da ya haramta, ina nasiha ga ma’abota ha’inci da algush a cikin mu’amala!? Ina nasiha ga wanda yake so varna ta yaxu a cikin musulmi, ko kuma yake bibiyar al’aurarsu don ya gano abin da suke aikata wa a voye?. Babu ko shakka waxannan babu su babu nasiha, sun yi nisa daga gareta. Madallah ga masu nasiha, Tir da tavewa ga masu algush. Ku ji tsoron Allah – Yaku bayin Allah – ku kamanta abubuwan da ya umarta a yi.

Yaku ‘yan uwana masu sauraro : Ku sani cewa wajibi ne akan duk wanda zai yi nasiha ya lura da waxannan abubuwa masu zuwa :

Nasiharshi ta zama don Allah, kada ya yi don a ji, ko don a gani, saboda duk aikin da aka yi ba don Allah ba, Allah baya karvar shi, baya bada lada a kanshi. Allah yana cewa,

(وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ5) [البينة: ٥].

Ma’ana : «Ba a umarce su sai dai su bautawa Allah suna masu tsarkake addini gare shi».

Ya zama ya san abin da zai yi nasiha a kai, saboda ba a hukunci a kan abu har sai an san shi.

Ya zama amintacce ne, domin babu nasiha ga wanda yake maha’inci.

Nasihar ta zama a voye, mai mulki za a yi wa ko kuma talaka, don gudun tozartawa. Amma Idan nasihar a voye ba ta yi amfani ba, to babu laifi a bayyanata, musamman ma idan ta shafi savawa abubuwan shari’a waxanda aka haxu a kansu.

Ba sharaxi ba ne wanda zai yi nasiha ya zama ya fi kowa ilimi, ko ya fi kowa daraja, ko adalci. Imam Ishaq xan Ahmad yana cewa : “Da a ce wanda yake da ilimi kaxan ba zai hana mai ilimi da yawa mummunan aiki ba, to da umarni da kyakkyawan aiki ya ruguje, da mun zama kamar Bani – Isra’ila waxanda Allah ya ce a kansu “Sun kasance ba sa hana mummunan aiki idan su aikata shi” don haka wanda aka fi falala zai iya yin inkari ga wanda ya fi shi falala, fajiri zai iya hana mutumin qwarai mummunan aiki”.

Bayin Allah : Haqiqa duk wanda yake bin tarihin magabatanmu na qwarai zai ga yadda suka buga kyakkyawan misalai wajen yi wa juna nasiha da karvar nasihar in an yi musu, an rawaito cewa babban tabi’in nan Imam Alhasan Al-Basriy ya ga wani mutum yana dawowa daga wurin jana’iza, sai ya ce masa, “Kana ganin wannan mamacin da zai dawo duniya zai yi aiki na qwarai kuwa?” sai mutum nan ya ce, “Qwarai kuwa” Sai Alhasul Basri ya ce da shi, “To in shi bai dawo ya yi ba, kai ka yi” wato in shi bai da ikon dawo wa duniya ya yi aiki na qwarai, saboda ya mutu, qasa ta binne shi, ya zama a cikinta, to kai ka yi tun gabanin ka zama a matsayinsa, ya zama babu damar qara aiki na qwarai.

Khalifofin nan shiryayyu sun kasance suna yi wa junansu nasiha a voye, suna farin ciki da ita in an yi musu, ba sa girman kai wajen karvarta. Sayyidin Abubakar – Allah ya yarda da shi – yana cewa : “Babu alheri a tare da mu idan bamu karvi nasiha ba, ku kuma mutane babu alheri a tare da ku idan baku yi mana nasiha ba”.

Sayyidina Umar xan Khaxxab – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Allah ya jiqan mutumin da faxa min kura – kuraina”. Akan wannan tsari shugabannin musulmi daga cikin magabata suka tafi.

Allah ya yi mana albarka cikin abin da muka ji, daga Alqur’ani da Sunnah, ya yi mana gafara, haqiqa shi mai iko ne akan komai.

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (ﷺ) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

‘Yan uwana musulmi : yana daga cikin abin da ya kamata a ambata a wannan wuri amana, domin kuwa amana nauyi ne mai girma, wanda Allah ya bijirar da shi ga sammai da qassai da duwatsu amma suka qi xauka. Allah yana cewa :

(إِنَّا عَرَضْنَا الْأَمَانَةَ عَلَى السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَالْجِبَالِ فَأَبَيْنَ أَنْ يَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الْإِنْسَانُ إِنَّهُ كَانَ ظَلُومًا جَهُولًا72) [الأحزاب: 72]

Ma’ana : “Haqiqa mu mun bijirar da amana ga sammai da qassai da duwatsu amma sai suka qi xaukarta, suka ji tsoronta, sai xan adam ya xauke ta, lallai shi mai yawan zalunci ne da jahilci” (Al-Ahzab : 72).

Amana tana nufin mutum ya lazimci haqqoqin da Allah ya xora masa, ya bauta masa kamar yadda ya shar’anta, hakanan ya lazimci kiyaye haqqin bayin Allah ba tare da sakaci ba, kamar yadda kake so mutane su kiyaye maka haqqoqinqa ba tare da sakaci ba, saboda mu ‘yan adam mun xauki nauyin kiyaye amana a wuyanmu, mun lazimci ta, za a kuma tambaye mu a kanta ranar alqiyama, kaico, wace amsa zamu bayar in an tambaye mu a wannan rana mai girma.

Yaku Musulmi : Allah Maxaukakin sarki ya umarce mu mayar da amana ga ma’abotanta, idan kuma zamu yi hukunci tsakanin mutane to mu yi hukunci da adalci, waxannan abubuwa guda biyu amana ba ta tsayuwa sai da su, mayar da amana ga masu ita, da hukunci tsakanin mutane da adalci.

Sannan kowa da kowa ya sani amana tana shiga cikin dukkan komai, shugaba ko sarki mai kiwo ne a kan talakawansa, kuma za a tambaye shi a kansu. Magidanci mai kiwo ne a kan iyalanshi, kuma za a tambaye shi akan abin da yake kiwo. Mace mai kiwo ce a gidan mijinta, kuma za a tambaye ta akan wannan abin da aka ba ta kiwo. Kai! Dukkaninku masu kiwo ne, kuma dukkaninku sai an tambayeku a kan abin da aka baku kiwo, kamar yadda Manzon Allah (ﷺ) ya faxa.

Ya ‘yan uwa musulmi : Amana a fahimtar magabata bata tsaya a kan mayar da dukiya ba, ko kiyaye alqawari kaxai ba, a'a ta yalwaci komai da komai, gabas da yamma, ita ce bishiyar tauhidi, kuma xan itacen imani nunanne, sannan inuwa ce a tsananin zafin rana, guzuri ga matafiya.

Amana ce tsayar da shari'ar Allah a cikin rayuwar mutane, sallah amana ce, idan bawa ya tozarta ta, to zai tozarta abin da ba ita ba, Anas xan Malik ya fashe da kuka yayin da ya ga an tozarta sallah a zamanin mulkin Hajjaj kamar yadda imamul Bukhari ya rawaito a cikin ingantaccen littafinsa. Babin da yake magana a kan tozarta sallah ga barin lokacinta. An karvo daga Zuhuri – Allah ya yi masa rahama – ya ce, na shiga wurin Anas xan Malik a garin Dimashqa, yana kuka, sai na ce da shi, "Me ya saka kuka?, sai ya ce, "Babu wani abu da na sani wanda na riska sai sallah, to ita ma sallar ga shi an tozartata". Zakka amana ce, Sayyidina Abubakar Assidiq ya yaqi waxanda suka hanata, ya siffata su da waxanda suka yi ridda. Azumi amana ne, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa "idan ranar azumin xayanku ce, kada ya yi batsa, kada ya yi hayaniya, idan wani ya zage shi ko ya yi faxa da shi, ya ce masa, "Ni mutum ne da yake azumi". Hajji amana ne, Allah yana cewa : "Duk wanda ya shiga hajji to babu batsa, babu fasiqanci, babu jayayya a cikin hajji". Kira zuwa ga Allah amana ne.

Amana tabbata ce akan ambaton Allah, da cika alqawarin ga Manzon Allah (ﷺ), sannan kuma da dauwama akan addini har zuwa qarshen rayuwa. Sarki Hiraqla ya tambayi Abu Sufyan dangane da sahabban Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa, "Shin ana samun wani daga cikinsu yana yin ridda ga barin addininsa?" Sai Abu Sufyan ya ce, "A'a" Sai Sarki Hiraqla ya ce, "Haka imani yake idan ya cakuxu da zuciya". Bukhari ne ya rawaito.

Amana kiyaye haqqoqin bayin Allah ce, kamar yadda Annabi Yusuf (A.S) ya amsa wa sarki yayin da yace, "A yau kai wajenmu tabbatacce ne amintacce". Sai ya ce, "Ka sanya ni akan taskokin qasa haqiqa ni mai kiyayewa ne kuma masani".

Amana bin iyaye ce, da kiyaye dukiyoyin musulmi, da kare musu mutunci. Amana kula da kiyaye ji ce, da yi wa gani hisabi, da bibiyar zuciya. Allah yana cewa :

(إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا36) [الإسراء: 36]

Ma’ana : “Kada ka bibiyi abin da baka ilimi a kanshi, haqiqa ji da gani da zuciya dukkansu ababen tambaya ne”. (Al-isra’I : 36).

Amana kiyaye ilimi ne da riwaya, kamar yadda malamai suke cewa, «Wannan ilimi addini ne, don haka ku duba wurin wa zaku karvi addininku».

Amana tashi ne da kula da haqqoqin musulmi, xaukan nauyin buqatun talakawa ne da miskinai, hidima ce ga mabuqata, haka siffar Manzon Allah (ﷺ) take, kamar yadda Nana A’isha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “A’a wallahi Allah ba zai tozarta ka ba har abada, saboda kai kana sada zumunci, kana xaukar nauyin wanda bai da shi, ka bawa wanda ba ya da shi, ka taimako a kan abubuwan gaskiya”. Bukhari.

Amana cika alqawari ne a kan abin da Alqur’ani da sunnah suka xora wa mutum, bin umarninsu da tsayuwa akan iyakarsu. Don haka yana cikin ha’intar Allah da Manzonsa a zagi sahabban Manzon Allah (ﷺ), a kafirta sahabban nan guda biyu masu girma Abubakar da Umar, alhali ayoyin Alqur’ani suna furuci da Allah ya yarda da su, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : “kada ku zagi sahabbaina”. Allah ya jiqan babarmu uwar muminai A’ishatu – Allah ya yarda da ita – yayin da take cewa Urwatu “Ya xan ‘yar uwata, an umarce su ne su yi sahabbai istigfari, amma sai suka zage su”. Muslim ne ya rawaito.

Amana adalci ce, da sanya mutane a matsayinsu, ba da tauye musu haqqi ba, kamar )yadda Allah ya ce, يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ لِلَّهِ شُهَدَاءَ بِالْقِسْطِ وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآَنُ قَوْمٍ عَلَى أَلَّا تَعْدِلُوا اعْدِلُوا هُوَ أَقْرَبُ لِلتَّقْوَى وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ8) [المائدة: 8]

Ma’ana : «Yaku waxanda kuka yi imani ku kasance masu tsayuwa saboda Allah, masu yin shaida da gaskiya, kada qin wasu mutane ya sanya ku qi adalci, ku yi adalci don shi ne mafi kusanci ga tsoron Allah».

Hakanan amana ce kada ku xaukaka wulaqantacce, kada kuma mu yabi qananan mutane, kada ba jivinta lamari ga waxanda ba ma’abotansa ba, kada mu girmama jahilai, mu hukunta su a cikin lamarin addininmu da duniyarmu, duk yin wannan yana cikin cin amana wanda yake tafiyar da jin daxin rayuwa da ginshiqinta.

Amana shaida ce don Allah, da nasiha ga musulmi, da bayyana gaskiya, wannan ya sa da aka tambayi Hafiz Aliyyu xan Madini dangane da babansa Abdullahi xan Ja’afar sai ya ce, «Babana yana da rauni (a haddarsa)».

Amana barin qarya ce da da’awar qarya, domin duk wanda zai siffatu da abin da ba na shi ba kamar wanda ya sanya rigar zur ce. Imam Azzabiy ya faxa a cikin littafinsa (Siyar) da Ibnu Kasir a cikin (Albidaya wan nihaya) suka ce, “Abu Abdullahil Hakim Annaisaburiy ya kasance yana karantar da mutane littafin da Alhafiz Abdulganiy xan Sa’id ya yi masa gyara cikin wasu kurakurai da ya faxa a cikinsu a cikin littafinsa (Almadkhal), kai! Bai ma tsaya nan ba, har sai da ya aika masa da godiya akan wannan nasiha da ya yi masa. Daga nan AbdulGaniy xan Sa’id ya ce, “Zai gane cewa lallai Hakim mutum ne mai hankali”.

Bayin Allah : Saboda girman amana da kyawunta Annabawan Allah suke siffata kansu da riqon amana. Annabi Hud (A.S) yana cewa mutanensa :

(أُبَلِّغُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَأَنَا لَكُمْ نَاصِحٌ أَمِينٌ68) [الأعراف: 68]

Ma’ana : (Ina isar muku da saqon Ubangijina kuma ni mai nasiha ne gareku amintacce) (Al-a’araf : 68).

Haka ma Annabi Lux, Salihu, da Nuhu, suka faxa wa mutanensu inda kowannensu yake cewa :

(إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ162) [الشعراء: 162]

Ma’ana : (Haqiqa ni Manzo ne gareku kuma amintacce). Manzon Allah (ﷺ) saboda amanarsa aka ce masa “Al-amin” a garin Makkah tun gabanin a aiko shi ya zama Manzo.

Ku ji tsoron Allah – bayin Allah – Shashenku ya yi wa sashe nasiha, saboda addinin gaba xaya nasiha ne, babu alheri ga al’aummar da ba nasiha a tsakaninta. Sannan ku mayar da amana ga masu ita, ku sani Allah zai tambayeku abin da ya baku kiwo, a ranar da dukiya da ‘ya’ya ba sa amfani sai wanda ya je wurin Allah da zuciya kuvutacciya.