islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Alamomin Tashin Qiyama


21975
Surantawa
Imani da ranar lahira rukuni ne cikin rukunnan imani, kuma imanin mutum baya cika har sai yayi imani da alamomin tashin qiyama, domin qiyamar ba zata auku ba sai sun faru. Haqiqa da dama daga cikin alamomin qiyama da manzon Allah s.a.w ya bada labarinsu sun bayyana, wanda hakan na nuni ne da kusantowarta. Don haka ya zama wajibi ga mutane su dawowa addininsu, kuma su fuskanci ubangijinu, domin idan ta zo, lallai imanin wata rai bazai amfane ta ba matuqar batayi imanin ba kafin wannan lokaci.

Manufofin huxubar

Cusa imani da Allah da ranar lahira a zukata.

Umarni a kan ayyukan qwarai da ribatar lokaci

Faxakar da mutane dangane da kusantowar alqiyama.

Jan-kunne game da fitintinu da kuma hanyoyin kauce musu.

Bayanin wasu daga cikin alamomin tashin qiyama.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka:

Ya ku musulmai! Matashiyar maganarmu a yau, tana da girma, magana ce da ta shafi gaibu, wato maganna a kan alamomin tashin qiyama. Allah yana cewa,

( فَهَلْ يَنْظُرُونَ إِلَّا السَّاعَةَ أَنْ تَأْتِيَهُمْ بَغْتَةً فَقَدْ جَاءَ أَشْرَاطُهَا فَأَنَّى لَهُمْ إِذَا جَاءَتْهُمْ ذِكْرَاهُمْ 18 ) [محمد: 18]

(Ba komai suke suke jira ba, face sa’a ta zo musu babu zato, babu tsammani. Haqiqa alamominta sun riga sun zo, to yaya za su yi idan wa’azinta ya zo musu?).

A cikin hadisin Jibril, sananne, wanda Imam Muslim ya rawaito, yana cewa, “Ka ba ni labari a kan imani.” Sai ya ce, “Imani shi ne, ka bayar da gaskiya ga Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa da ranar qarshe, kuma ka ba da gaskiya da qaddara, mai daxi da mara daxi.”

An karvo daga Huzaifa bin Usaid, ya ce, “Wata rana mun kasance muna zaune, muna hira a inuwar wani xaki na Manzon Allah (ﷺ), sai muka ambaci sa’a, sai muryoyinmu suka xaukaka, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Alqiyama ba za ta kasance ba, ko ba za ta tsaya ba, har sai alamomi guda goma sun kasance gabaninta….” har zuwa qarshen hadisin. [Abu Dawud ya ruwaito].

Sanin lokacin tashin qiyama na daga cikin abin da Allah ya bar wa kansa sani. Allah yana cewa,

( يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِنْدَ رَبِّي لَا يُجَلِّيهَا لِوَقْتِهَا إِلَّا هُوَ ثَقُلَتْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَا تَأْتِيكُمْ إِلَّا بَغْتَةً يَسْأَلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِيٌّ عَنْهَا قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِنْدَ اللَّهِ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ 187 ) [الأعراف: 187]

(Suna tambayar ka game game lokacin tashin qiyama. Yaushe ne za ta tsaya? Ka ce, “Iliminta na wurin Ubangijina, babu wanda yake bayyana da lokacinta, sai shi. Ta nauyaya a sama da qasa, ba za ta zo muku ba, face babu zato, babu tsammani. Suna tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce, “Kaxai dai, saninta na wurin Allah, sai dai da yawa mutane ba su sani ba).

Kuma ya ce,

( يَسْأَلُكَ النَّاسُ عَنِ السَّاعَةِ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِنْدَ اللَّهِ وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّ السَّاعَةَ تَكُونُ قَرِيبًا 63 ) [الأحزاب: 63]

(Mutane suna tambayar ka game da alqiyama. Ka ce, “Saninta na wajen Allah. Me ya sanar da kai, wata qila sa’a za ta zama kusa?) .

Kuma ya ce,

( يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا 42 فِيمَ أَنْتَ مِنْ ذِكْرَاهَا 43 ِلَى رَبِّكَ مُنْتَهَاهَا 44 ) [النازعات: 44]

(Suna tambayar ka game da sa’a, yaushe ne za ta tsaya? Me ya haxa ka da zmbaton ta? Zuwa ga Ubangijinka matuqarta take).

Kuma yayin da mala’ika Jibrilu ya tambayi Manzon Allah (ﷺ) lokacin tashin qiyama, sai ya ce, “Wanda ake tambaya a kanta, bai fi mai tambayar sani ba.” [Muslim ya rawaito shi].

Ibni Rajab, Allah ya ji qan sa yana cewa, "Abin da yake nufi, ilimin halitta baki xaya kan lokacin sa’a xaya yake, abin da yake nuna Allah ne ya kevanta da sanin lokacinta".

Imamu Ahmad ya rawaito hadisi daga Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ranar da aka yi isra’i da ni, na haxu da Ibrahim da Musa da Isa, sai suka ambaci tashin qiyama, sai suka mayar da lamarinsu ga Ibrahim. Sai ya ce, “Ba ni da masaniya a kanta.” Sai suka mayar da lamari ga Musa. Sai ya ce, “Ba ni da sani a kanta.” Sai suka mayar da lamari ga Isa. Sai ya ce, “Amma lokacin aukuwarta, babu wanda ya san haka, sai Allah. Kuma yana cikin abin da Allah ya yi mini alqawari, cewa Dujal zai fito tare da ni, akwai sanduna guda biyu, idan ya gani, sai ya narke, kamar yadda dalma take narkewa.” Ya ce, “Sai Allah ya halakar da shi.”

Haqiqa ayoyin Alqur’ani da hadisan Ma’aiki sun yi nuni a kan qarantuwar sa’a da kusancinta. Allah yana cewa,

( اقْتَرَبَ لِلنَّاسِ حِسَابُهُمْ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ مُعْرِضُونَ 1 ) [الأنبياء: 1]

(Hisabin mutane ya kusa, su suna cikin gafala, suna ba da baya).

Kuma Ubangiji ya ce,

وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّ السَّاعَةَ تَكُونُ قَرِيبًا 63) [الأحزاب: 63]) (Me ya sanar da kai cewa wata qila sa’a ta kasance kusa?).

Kuma Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “An aiko ni, alhali ni da sa’a muna kamar haka.” Ya yi nuni da yatsunsa, yana miqe su. [Bukhari da Muslim suka rawaito shi]

Haqiqa alamomin tashin qiyama sun rabu guda biyu: Qanana da manya. Qanana su ne wanda za su zo tsawon lokaci, kafin tashin qiyama, kuma za su zamo cikin abin da aka saba da shi a rayuwa, yau da kullum. Wasu daga cikin qananan, za su iya bayyana tare da manyan alamomin, ko bayan bayyanarsu. Su kuwa manyan, su ne alamu, wanda za su bayyana dab da sa’a, kuma abubuwa ne da ba a saba da su ba a rayuwa: Kamar bayyanar Dujal, da makamancin haka. Amma ta fuskar bayyanarsu, iri uku ne: Na xaya, wanda sun bayyana, sun wuce; na biyu, sun bayyana, kuma suna ta havaka; na uku, wanda har yanzu ba su bayyana ba. Daga cikin qananan alamomin, akwai aiko Manzon Allah (ﷺ), saboda hadisin Sahl (RA) ya ce, “An aiko ni, ni da sa’a, muna kamar haka.” yana nuni da yatsunsa, yana miqe su. [Bukari da Muslim suka ruwaito].

Kuma haka mutuwarsa, saboda hadisin Auf bin Malik (RA), ya ce, “Ka lissafa abubuwa guda shida a gabanin sa’a: Na farko, mutuwata.” Sannan ya ambaci sauran. [Bukhari ya rawaito shi]. Da mutuwarsa ne wahayi ya yanke. Kamar yadda Ummu Aiman ta faxawa Abubakar da Umar cikin amsar da ta ba su lokacin da suka ziyarce ta a gidanta bayan mutuwar Annabi. (ﷺ) [Muslim ne ya ruwaito].

Daga ciki alamomin alqiyama, akwai bayyanar fitintinu masu girma, wanda qarya za ta cuxanya da gaskiya, imani ya riqa reto a cikin zukata, mutum ya wayi gari yana musulmi, kafin rana ta faxi, ya kafirta. Abu Musa ya rawaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Gabanin sa’a, akwai fitintinu, kamar yankin dare mai duhu. Mutum zai wayi gari a cikinsu, yana mumini, amma yamma ta yi, ya zama kafiri, ko kuma da yamma yana mumini, ya wayi gari ya zama kafiri.”. [Ahmad da Abu Dawud da Ibn Majah ne suka ruwaito].

Yana daga cikin alamomin, bayyanar wata wuta a yankin Hijaz (Makka da Madina). Abu Huraira ya rawaito, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Sa’a ba za ta tsaya ba, har sai wuta ta fito a yankin Hijaz wacce za ta haskaka wuyayukan raquma a Busra.” [Muslim ya rawaito shi]. Kuma wannan wuta ta bayyana a tsakiyar qarni na bakwai, a shekara ta 654. Wuta ce gagaruma, malamai da suka ga zamaninta, sun kawo labarinta, kamar yadda Ibn Kasir ya yi a cikin littafinsa Al-Bidaayah Wan-Nihaayah.

Yana daga cikin alamomin, tozarta amana. An karvo daga Abu Huraira, ya ce Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Idan aka tozarta amana, ka jira sa’a.” [Bukhari ya rawaito shi]

Allah ya albarkance mu, ni da ku, cikin Alqur’ani mai girma, kuma ya amfane mu, ni da ku, da abin da yake cikinsa na ayoyi da wa’azi mai azanci. Shi majivincin haka ne, kuma mai iko a kan haka.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangiji talikai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah (ﷺ).

Bayan haka, ya ‘yan uwa! Yana daga cikin alamomin sa’a qanana, yaxuwar neman mata da fitsara. Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, “Na rantse da wanda raina yake hannunsa (Allah), wannan al’umma ba za ta qare ba, har sai mutum ya shimfixe mace a kan hanya (zai yi lalata da ita), zavavvun cikinsu a wannan lokaci, shi ne wanda zai ce, “Ina ma ka sa ta a bayan katanga.” [Abu Ya’ala ya rawaito shi].

Yana daga cikin alamominta, kisfe qasa da rikixa halitta da jifa. Kuma yana daga ciki, baiwa ta haifi uwar gijiyarta; ka ga mutane marasa takalmi, talakawa, suna gasar gina gidaje masu tsawo. An karvo daga Sahl ibn Sa’ad cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “A qarshen zamani, za a samu kisfe qasa, da jifa, da rikixa halitta.” Sai aka ce, “Yaushe hakan zai faru, ya Ma’aikin Allah?” Sai ya ce, “Idan dai kaxa-kaxe suka bayyana, da 'yan mata masu waqe-waqe”. [Tabarani ya rawaito shi].

A cikin hadisin Jibril shahararren nan, ya ce, “Ka ba ni labarin alamominta.” Sai ya ce, “Baiwa ta haifi uwargidanta, ka ga marasa takalmi, masu tafiya tsirara, talakawa, masu kiwon awaki, suna gasar gina dogayen benaye” [Muslim ne ya rawaito shi].

Yana daga cikin alamomin, bayyanar qarya, da kusancin kasuwanni. An karvo daga Abu Huraira (RA) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Sa’a ba za ta tsaya ba, har sai fitintinu sun bayyana, qarya ta yawaita, kuma kasuwanni su yi kusanci da juna.” [Imam Ahmad ya rawaito shi]

Ya ku ‘yan uwa musulmai! Waxannan kaxan kenan daga alamomin tashin qiyama qanana. Amma manyan su ne, wanda bayansu za a yi tashin qiyama. Daga ciki, akwai fitowar Yajuju da Majuju. Allah yana cewa,

( حَتَّى إِذَا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ وَهُمْ مِنْ كُلِّ حَدَبٍ يَنْسِلُونَ 96 ) [الأنبياء: 96]

(Har sai sanda aka buxe Yajuju da Majuju, alhali suna ta gangarowa daga kowane tudu(.

Daga ciki kuma, akwai fitowar dabba daga qasa, wadda za ta riqa yi wa mutane magana. Allah ya ce,

( وَإِذَا وَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِمْ أَخْرَجْنَا لَهُمْ دَابَّةً مِنَ الْأَرْضِ تُكَلِّمُهُمْ أَنَّ النَّاسَ كَانُوا بِآَيَاتِنَا لَا يُوقِنُونَ 82 ) [النمل: 82]

(Idan zance ya tabbata a kansu, sai mu fito musu da wata dabba daga qasa, tana yi musu magana, “Lallai mutane sun kasance ba sa sakankancewa da ayoyinmu.”).

An karvo daga Huzaifa bn Usaid, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) wata rana, ya leqo daga xaki, alhali muna tattaunawa a kan tashin alqiyama. Sai ya ce, “Alqiyama ba za ta tsaya ba, har sai kun ga alamomi guda goma: Hudowar rana daga yamma, da Dujjal, da hayaqi, da dabba, da yajuju da majuju, da fitowar Annabi Isa (AS), da kifar da qasa guda uku: kifarwa ta gabas, kifarwa ta yamma, da kifarwa ta tsibirin larabawa. Da wuta da za ta fito daga tsakiyar birnin Adn, za ta kora mutane zuwa matattara, ta kwana da su, idan sun kwana, kuma ta yi qailula da su, idan sun yi qailula.” [Ibni Majah ya rawaito shi]

Ya ku bayin Allah! Waxannan wasu kenan daga cikin alamomin tashin alqiyama, qanana da manya. Shin mun shirya wa tashin alqiyama? Me muka aikata, don tunkarar wannan rana mai tsoratarwa? Shin yanzu, ba ma koma zuwa ga Allah ba, mu nemi gafararsa?

( أَلَمْ يَأْنِ لِلَّذِينَ آَمَنُوا أَنْ تَخْشَعَ قُلُوبُهُمْ لِذِكْرِ اللَّهِ وَمَا نَزَلَ مِنَ الْحَقِّ ) [الحديد: 16]

(Har yanzu lokaci bai yi ba ga wanda suka ba da gaskiya, zukatansu su risina ga ambaton Allah, da abin da ya saukar na gaskiya?).

Ku sani, ya bayin Allah! Lallai aukuwar mafi yawan alamomin tashin qiyama qanana, yana nuna kusancin aukuwar manya, wanda idan suka auku, tashin alqiyama ya zo. Don haka, ku ji tsoron Allah, ya bayin Allah, ku inganta ayyukanku, ku yi tanadi da ranar tashin alqiyama, ku sani lallai sa’a tana nan tafe, babu kokwanto a cikinta.

Ya Ubangiji! Ka xaukaka musulunci da musulmai, ka qasqantar da kafirci da kafirai, ka kuma rushe maqiya addininka.