islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Son Allah Da Manzonsa, Da Qaddamar Da Su Akan Waninsu


9209
Surantawa
Yana daga cikin abinda ya zama lazimin imani, kuma bawa baya zama cikakken musulmi mumini har sai ya gabatar da son Allah da manzonsa akan dukkan abinda ya mallaka na dukiya da ‘ya’ya da dukkan mutane gaba ‘daya, kamar yadda manzon Allah s.a.w ya bada labari, kuma gwargwadon qaunar mutum ga Allah da manzonsa, gwargwadon ayyukan biyayyansa da kuma amsa ma kiran Allah da manzonsa.

Manufofin huxubar

Bayanin wajabcin son Allah da Manzonsa. Da fifita su a kan komai

Dasa son Allah da Manozonsa a cikin zukata.

Bayanin alamomin son Allah da Manzonsa.

Abubuwan da suke haifar da son Allah da Manzonsa.

Jan-Kunne a kan gabatar da son mata ko dukiya ko ‘ya’ya a kan son Allah da Manzonsa.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka:

Ya ‘yan uwa musulmai! Maganarmu a yau, magana ce mai girma, kowane xaya daga cikinmu yana buqatar ta. Imaninmu ba zai cika ba, sai mun tabbatar da ita: Abin nufi, son Allah da Manzonsa, da kuma gabatar da su a kan duk wani abu da ba su ba. Lallai imani ba zai cika ba, ba tare da qaunar Allah, da son Manzon Allah (ﷺ) ba. Babu yadda za a yi mutum ya zama cikakken mai imani, ba tare da ya gabatar da son Allah da Manzonsa a kan duk wani abu da ya mallaka na dukiya, ko xa, ko mahaifa, ko ma sauran mutane baki xaya ba, kamar yadda Manzon Allah (ﷺ) ya yi bayanin haka cikin ingantaccen hadisi.

Ya ‘yan uwa musulmi! Haqiqa Allah ya umarci muminai, da su qaunaci Manzon Allah (ﷺ) a wuri daban-daban a cikin littafinsa. Kaxan daga ciki, Allah yana cewa,

( قُلْ إِنْ كَانَ آَبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ وَإِخْوَانُكُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ وَعَشِيرَتُكُمْ وَأَمْوَالٌ اقْتَرَفْتُمُوهَا وَتِجَارَةٌ تَخْشَوْنَ كَسَادَهَا وَمَسَاكِنُ تَرْضَوْنَهَا أَحَبَّ إِلَيْكُمْ مِنَ اللَّهِ وَرَسُولِهِ وَجِهَادٍ فِي سَبِيلِهِ فَتَرَبَّصُوا حَتَّى يَأْتِيَ اللَّهُ بِأَمْرِهِ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ 24 ) [التوبة: 24]

(Idan dai iyayenku, da ‘ya’yanku, da ‘yan uwanku, da matanku, da danginku, da dukiyoyinku da kuka tara, da kasuwancin da kuke tsoron durqushewarsa, da gidajen da kuke son su, sun fi soyuwa gare ku, sama da Allah da Manzonsa da jihadi a cikin tafarkinsa, to ku dakata har Allah ya zo da al’amarinsa. Allah ba ya shiryar da mutanen da suke fasiqai ne).

Alqadhi Iyad, mai littafin Ashafa, yana cewa, a cikin littafinsa: «Wannan aya ta isa wajen tabbatar da wajabcin qaunar Manzon Allah (ﷺ), da tabbatar da cancantarsa da soyayyar muminai, don Allah ya qwanqwanshi wanda ya zama dukiyarsa da matansa da ‘ya’yansa sun fi soyuwa zuwa gare shi, sama da Allah da Manzonsa. Sannan ya yi narko da faxinsa, “….ku dakata har Allah ya zo da al’amarinsa.” Sannan ya rataya musu fasiqanci a qarshen ayar, ya kuma sanar da su cewa suna daga cikin waxanda suka vata, kuma Allah ba zai shiryar da su ba.

Allah yana cewa,

( قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ 31 ) [آل عمران: 31]

(In kun kasance kuna son Allah, to ku yi mini biyayya, sai Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku laifukanku. Kuma Allah mai yawan gafara ne mai jin qai).

Kuma Allah ya ce,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا لَا تُقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيِ اللَّهِ وَرَسُولِهِ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ 1 ) [الحجرات: 1]

(Ya ku waxanda suka yi imani! Kada ku sha gaban Allah da Manzonsa. Ku ji tsoron Allah, lallai Allah mai ji ne, kuma masani).

Ya zo a cikin sunnar, Manzon Allah (ﷺ), kamar yadda Anas ibn Malik ya rawaito cewa, “Xayanku ba zai yi imani ba, har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi, sama da mahaifansa da xansa da sauran mutane baki xaya.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Haka nan, Anas ibn Malik ya rawaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Abubuwa guda uku, duk wanda ya same su, ya sami zaqin imani: Allah da Manzonsa su zamo su ne mafi soyuwa gare shi daga abin da ba su ba; kuma ya so mutum, ba don komai ba, sai don Allah; kum ya dinga qyamar ya koma cikin kafirci, kamar yadda yake qyamar a jefa shi a cikin wuta.”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Lallai qaunar Allah da Manzonsa, tana da alamomi, wanda malamai suka yi bayaninta dalla-dalla, suka tsamo daga cikin littafin Allah, da sunnar Manzon Allah (ﷺ). Alqali Iyadh yana cewa, "Mai gaskiya a cikin da’awar qaunar Manzon Allah (ﷺ), shi ne wanda aka ga alamomin qauna tare da shi. Abu na farko, koyi da shi, da aiki da sunnarsa, bin maganganunsa da ayyukansa, kwatanta umarninsa da nesantar abin da ya hana, da kamanta ladabi irin nasa, a cikin kowane irin yanayi mai daxi ko marar daxi. Duk wannan yana qunshe a cikin faxin Allah cewa,

( قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ 31 ) [آل عمران: 31]

(In kun kasance kuna son Allah, to ku yi mini biyayya, sai Allah ya so ku…).

Haka da fifita abin da ya shar’anta, kuma ya kwaxaitar a kai, a kan bin son zuciya, da bin sha’awa. Allah yana cewa,

( وَالَّذِينَ تَبَوَّءُوا الدَّارَ وَالْإِيمَانَ مِنْ قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمْ حَاجَةً مِمَّا أُوتُوا وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ وَمَنْ يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ 9 ) [الحشر: 9]

(Waxanda suka zauni gida, suka yi imani tun ganinsu, suna son waxanda suka yi hijira zuwa gare su. Ba sa jin takuruwa a zuciyarsa daga a ka ba su. Su na fifita ‘yan uwansu akansu ko da kuwa sun kasance suna da buqata. Waxannan su ne masu samun babbar nasara).

Yana daga ciki, taimakon addininsa, ta hanyar magana ko aiki, da kare sunnarsa; yana daga ciki, yawan begen haxuwa da shi; yana daga ciki, son karatun Alqur’ani, da qin duk wanda ba ya son Allah da Manzonsa.

Amma abubuwan da suke jawo soyayyar Allah da Manzonsa ga bayi, su ne; yin imani da Allah Ta’ala, ayyuka na qwarai, haquri, kyautata wa bayi, tsarki, tuba. Allah yana cewa,

( وَاللَّهُ يُحِبُّ الصَّابِرِينَ 146 ) [آل عمران: 146]

(Allah yana son masu haquri).

Haka kuma, Allah yana cewa,

( إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ 195 ) [البقرة: 195]

(Lalle Allah yana son masu kyautayi).

Haka kuma, Allah yana cewa,

( إِنَّ الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَيَجْعَلُ لَهُمُ الرَّحْمَنُ وُدًّا 96 ) [مريم: 96]

(Lallai waxanda suka ba da gaskiya, kuma suka yi ayyuka na qwarai, da sannu Allah zai sanya musu qauna).

Kuma Allah yana cewa,

إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ 222 ) [البقرة: 222] ( (Lallai Allah yana son masu tuba, kuma yana son masu tsarki).

Haka kuma, Allah yana cewa,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا مَنْ يَرْتَدَّ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ فَسَوْفَ يَأْتِي اللَّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ أَذِلَّةٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى الْكَافِرِينَ يُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَلَا يَخَافُونَ لَوْمَةَ لَائِمٍ ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ 54 ) [المائدة: 54]

(Ya ku waxanda suka yi imani! Duk wanda ya ba da baya ga barin addininsa daga cikinsu, da sannu Allah zai zo da wasu mutane, waxanda yake son su, kuma su ma suke son sa, masu qanqan da kai a kan muminai, masu nuna xaukaka a kan kafirai, suna yin jihadi a cikin tafarkin Allah, ba sa tsoron zargin mai zargi. Wannan wata falala ce daga Allah yana bayar da ita ga wanda ya so. Kuma lalle Allah mai yalwatawa ne, masani).

Huxuba Ta Biyu

Yabo da godiya da kira sun tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin rahma, Annabinmu Muhammad da alayensa da sahaabban da sauran masu qaunarsa har zuwa ranar qiyama. Bayan haka:

Ya ku ‘yan uwa! Ku sani, sahabban Manzon Allah (ﷺ) sun nuna rayuwa abar misali, wajen qaunar Manzon Allah (ﷺ), da girmama shi. Ba a tava samu wasu mutane a doron qasa ba waxanda suka so win bil-adama kamar yadda sahabban Manzon Allah (ﷺ) suka so shi. Daga wajensu ne za mu koyi yadda haqiqanin son Manzon Allah ya ke.

An karvo daga Amr bin Aas (RA) ya ce, “Babu wani da ya fi soyuwa zuwa zuciyata, sama da Manzon Allah (ﷺ); babu wanda ya fi qima a idanuna, sama da shi; amma duk da haka ba na iya cika idanuna wajen kallon sa, saboda girmamashi. Da za a tambaye ni, in siffanta shi, da ba zan iya ba, saboda ba na iya cika idanuna wajen kallon sa.” Muslim ne ya ruwaito shi.

Urwatu xan Mas'ud (R.A.) kafin ya shiga musulunci, ya ga irin yadda sahabban Manzon Allah (ﷺ) su ke girmama shi, suke nuna masa soyayya ta haqiqa, suke tabarraki da wasu abubuwa masu alaqa da shi. Ya kuma ga irin yadda suke gaggawar zartar da umarninsa. Lokacin da ya je sulhul Hudaibiyya, ya gane wa idonsa hakan. Ga yadda ruwayar ta zo:

"Sannan Urwa ya zurawa sahabban Annabi (ﷺ) ido yana kallon su. Ya ce: "Wallahi babu wani kaki da Manzon Allah (ﷺ) ya tofar face ya faxa a hannun xaya daga cikinsu, kuma ya shafe fuskarsa da jikinsa da shi. Idan ya umarce da wani abu, nan da nan sai su zartar da wannan abin. Idan kuma ya rage ruwan alwala, to fa kamar sa yi faxa a kan sauran wannan ruwan. Idan kuwa yana magana to kowa sai ya yi tsit yana sauraron shi. Ba sa iya qura masa ido, domin irin yadda suke ganin girmansa. Daga nan Urwatu ya koma ga kafirai 'yan uwansa ya ce musu: "Ya jama'ata! Wallahi na yi yawo na ga sarakuna daban-daban. Na ga sarki qaisara na rumawa, naga sarkin Farisawa Kisra, naga na Habasha Najashi, to amma wallahi ban ga sarkin da mutanensa suke girmama shi ba kamar yadda sahabban Manzon Allah (ﷺ) suke girmama shi. Wallahi bai yi kaki ya tofar ba face ya faxa a hannun xaya daga cikinsu, kuma ya shafe fuskarsa da jikinsa da shi. Idan ya umarce da wani abu, nan da nan sai su zartar da wannan abin. Idan kuma ya rage ruwan alwala, to fa kamar sa yi faxa a kan sauran wannan ruwan. Idan kuwa yana magana to kowa sai ya yi tsit yana sauraron shi. Ba sa iya qura masa ido, domin irin yadda suke ganin girmansa". Bukhari ne ya ruwaito shi.

An tambayi Aliyu bin Abi Talib, “Yaya qaunarku ta kasance ga Manzon Allah (ﷺ)?” Sai ya ce, “Na rantse da Allah, ya kasance, ya fi soyuwa ga zukatanmu, sama da dukiyoyinmu, da ‘ya’yanmu, da iyayenmu. Kai sama ma da ruwan sanyi ga mai jin qishi”.

Kuma Alqali iyad ya rawaito cewa, Bilal da Huzaifatubn Yaman da Ammar bn Yasir, sun kasance lokacin da mutuwa ta zo musu, suna cewa, “Gobe za mu haxu da masoya, Muhammadu da rundunarsa.”

Ya ku 'yan uwana musulmi! Ku sani Allah yana cewa,

( قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ 31 ) [آل عمران: 31]

(Ka ce, idan har kuna son Allah, to ku bi ni Allah zai so ku ya gafarta muku zunubbanku. Kuma Allah mai yawan gafara ne, mai yawan jin qai).

Malam Ibni Kasir yana cewa, «Wannan aya mai girma, ta yanke hukunci a kan dukkan wanda ya yi da’awar qaunar Allah, amma kuma ba ya kan tafarkin Manzon Allah (ﷺ), da cewa lallai shi maqaryaci ne, har sai ya bi shari’ar Manzon Allah (ﷺ), da addinin da Annabi ya zo da shi, cikin gabaxayan maganganunsa da ayyukansa da yanayinsa, kamar yadda ya tabbata cikin hadisi, Manzo Allah (ﷺ) yana cewa, “Duk wanda ya aikata wani aiki, ba tare da umarninmu ba, za a mayar masa da aikinsa.” Wani daga cikin masu hikima yana cewa, Batun inda yake, shi ne a so ka, ba wai kai ka ce, kana so ba". Hasanul Basari yana cewa, "Wasu daga cikin mutane sun yi da'awar qaunar Allah, sai Allah ya jarrabe su da wannan aya". Kuma Manzon Allah yana cewa, "Na hore ku da bin sunnata da sunnar halifofi na shiryayyu. Ku cije su da fiqoqinku. Kuma ina jan-kunnenku game da fararrun al'amurra. Domin duk wani fararren abu bid'a ne, duk wata bid'a kuwa vata ce".

Ya ku ‘yan uwa! Ku sani, yana daga cikin haqqoqin Manzon Allah (ﷺ) a kan bayi, su dinga yin salati gare shi, kamar yadda Allah yake cewa,

( إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا 56 ) [الأحزاب: 56]

“Lallai Allah da mala’ikunsa suna salati ga Annabi. Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati gare shi, kuma ku yi masa taslimi.”

Haka yana daga cikin haqqoqinsa a kan wannan al’umma, girmamashi da kambama shi. Allah yana cewa,

( لَا تَجْعَلُوا دُعَاءَ الرَّسُولِ بَيْنَكُمْ كَدُعَاءِ بَعْضِكُمْ بَعْضًا ) [النور: 63].

(Kada ku sanya kiran Manzon Allah a tsakaninku, kamar kiran junanku).

Haka nana, yana daga cikin haqqoqinsa, kare martabarsa da martabar sahabbansa masu girma.

Ya Allah ka sanya cikin masu qaunar Annabinka qauna ta haqiqa. Ka tabbatar da digadiganmu akan sunnarsa, mu rayu akai mu mutu a kai, kuma a tashe mu tare da tawagar qwarai, ta Annabawa da siddiqai da salihai da shahidai.