islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Ka yi wa masu haquri albishir


11723
Surantawa
Haqiqa haquri ga mumini tamkar wata madogara ce da babu yadda ya iya sai ya dogara da shi. Babu imani cikakke ga wanda ba shi da haquri. Duk sanda imani ya yi qaranci kuwa to sai ka ga ko da bautar Allahn ma ta zama rabi darabi.

Manufofin huxubar

Koyar da haquri.

Haquri halayyar mumini ce.

Sanin kashe-kashen haquri.

Haquri dole ne ga mai son ya rayu a tsaka

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka! Ya bayin Allah! Ku sani Allah ya sanya haquri tamkar ingarman dokin da ba ya tuntuve, tamkar takobin da ba ya dakushewa, tamkar rundunar da ba a tava karya ta ba, tamkar ganuwar da ba ta rusuwa. Haquri da nasara ‘yan’uwan juna ne, kuma duk mutumin da bai riqi haquri a matsayin makaminsa a addininsa da duniyarsa ba to ya san da sanin cewa, maqiyansa sai sun fatattake shi. Maqiyi ne na zuciya ko na shaixan ne. Kuma babu wani qarfi ga bawan da bai da haquri. Kamar yadda babu shi babu cin nasara matuqar dai ba shi da haquri a yaqinsa da yin gaba da abokin gabansa. Allah yana cewa,

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اصْبِرُوا وَصَابِرُوا وَرَابِطُوا وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ200) [آل عمران: 200]

(Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi haquri, kuma ku jure, kuma ku zama a cikin shiri, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta).

Ya bayin Allah, haqiqa haquri igiyar talala ce ta mumini, duk inda ya je zai komo gare shi. Kuma shi dai haquri ga mumini tamkar wata madogara ce da babu yadda ya iya sai ya dogara da shi. Babu imani cikakke ga wanda ba shi da haquri. Duk sanda imani ya yi qaranci kuwa to sai ka ga ko da bautar Allahn ma ta zama rabi darabi. Ranar da gari ya yi daxi a yi, ranar da kuma abubuwa suka cave a yi biris da ita. Allah ya ce:

(وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَعْبُدُ اللَّهَ عَلَى حَرْفٍ فَإِنْ أَصَابَهُ خَيْرٌ اطْمَأَنَّ بِهِ وَإِنْ أَصَابَتْهُ فِتْنَةٌ انْقَلَبَ عَلَى وَجْهِهِ خَسِرَ الدُّنْيَا وَالْآَخِرَةَ ذَلِكَ هُوَ الْخُسْرَانُ الْمُبِينُ11) [الحج: 11]

(Daga cikin mutane akwai wanda yake bauta wa Allah a kan gava, idan alheri ya same shi sai ya gamsu da shi, idan kuma wata musiba ta same shi sai ya juya baya, to ya tave duniya da lahira, wannan ita ce hasara mabayyaniya).

Wannan bai samu komai a kasuwancinsa ba sai hasara mai girma da ya yi. Waxanda suka dace da kyakkyawar rayuwa sun same ta ne a dalilin haqurinsu. Don haka sun sami manya-manyan matsayi a dalilin godiyarsu ga Allah. Sun ta shi sama da fikafikin haquri da na godiya ga Allah zuwa ga aljannatai na ni’ima. Saboda faxar Allah da yake cewa,

(ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ) [الحديد: 21]

(Wannan falala ce daga Allah, yana bayar da ita ga wanda ya so, Allah kuwa Ma’abocin falala ne mai girma(.

Ya bayin Allah! Haquri halayyar cikakkun bayin Allah muminai ce, babu mai jure masa sai wanda Allah ya qarfafe shi. Annabawa da manzanni su ne abin koyi a dukkan nau’o’in haquri, Imam Ahmad Allah ya rahamshe shi ya ce: “Allah Mai tsarki ya ambaci haquri sau casa’in a cikin Alqur’ani». Sannan kuma Allah Mai girma da buwaya ya yabi masu haquri a cikin littafinsa. Kuma Ya ba da labarin cewa ladan da zai ba masu haquri, ya fi gaban lissafi, a inda yake cewa:

(إِنَّمَا يُوَفَّى الصَّابِرُونَ أَجْرَهُمْ بِغَيْرِ حِسَابٍ10) [الزمر: 10]

(Haqiqa masu haquri ne kawai ake cika wa ladansu ba da lissafi ba).

Bayan haka, Allah ya faxi cewa, yana tare da masu haquri da shiryarwarsa, da babban taimakonsa, da kuma bayyanannen buxinsa, sai ya ce:

وَاصْبِرُوا إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ46) [الأنفال: 46]) (Ku yi haquri haqiqa Allah Yana tare da masu haquri).

Kasancewar masu haquri na tare da Allah, ya sa suka rabauta da ni’imomin Allah na fili da na voye.

Haka kuma, bayan duk waxannan bayanai, Allah mai girma da xaukaka, ya haxa shugabanci a addini da haquri da sakankancewa sai ya ce;

(وَجَعَلْنَا مِنْهُمْ أَئِمَّةً يَهْدُونَ بِأَمْرِنَا لَمَّا صَبَرُوا وَكَانُوا بِآَيَاتِنَا يُوقِنُونَ24) [السجدة: 24]

“Muka sanya shugabanni daga cikinsu (wato banu Isra’ila) suna shiryarwa da umarninmu lokacin da suka yi haquri, kuma sun kasance suna sakankancewa da ayoyinmu”.

Qari a kan haka Allah ya rantse a kan cewa haquri alheri ne ga masu yin sa a inda ya ce:

وَلَئِنْ صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْرٌ لِلصَّابِرِينَ126) [النحل: 126]) “Kuma lalle idan kuka yi haquri, to babu shakka shi ne mafi alheri ga masu haquri”.

Kuma komai qarfin abokin gaba babu yadda ya iya da bawa mai haquri da tsoron Allah. Allah maxaukaki ya ce:

(وَإِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا لَا يَضُرُّكُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا إِنَّ اللَّهَ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيطٌ120) [آل عمران: 120]

“Idan kuka yi haquri kuka ji tsoron Allah, to makircinsu ba zai cuce ku da komai ba. Haqiqa Allah mai kewaye ce da saninsa ga abin da suke aikatawa.”

Sannan kuma Allah Y a rataye rabautar bawa da haquri da kuma jin tsoron Allah. Sai Ya ce:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اصْبِرُوا وَصَابِرُوا وَرَابِطُوا وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ200) [آل عمران: 200]

(Ya ku waxanda suka yi imani ku yi haquri, kuma ku jure, kuma ku zama a cikin shiri, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta).

Bayan haka, Allah ya bayyana qaunarsa ga bayinsa masu haquri. Ya ce,

(وَاللَّهُ يُحِبُّ الصَّابِرِينَ146) [آل عمران: 146] (Allah yana son masu haquri).

Sannan ya yi wa masu haquri albishir da abubuwa uku masu daraja fiye da abubuwan da bayi suke hassada a kansu a duniya, Ya ce:

(وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ 155الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُمْ مُصِيبَةٌ قَالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ 156أُولَئِكَ عَلَيْهِمْ صَلَوَاتٌ مِنْ رَبِّهِمْ وَرَحْمَةٌ وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُهْتَدُونَ 157)[البقرة: ١٥٥ – ١٥٧].

(Kuma ka yi albishir ga masu haquri waxanda idan masifa ta same su sai su ce, mu na Allah ne, kuma mu wurinsa za mu koma. Waxancan (bayi) gafarar Allah ta tabbata a gare su da rahama, kuma waxancan su ne shiryayyu).

Sannan kuma babu mai tsira daga wuta, kuma ya rabauta da aljanna sai fa masu haquri. Allah mai girma da buwaya ya ce:

إِنِّي جَزَيْتُهُمُ الْيَوْمَ بِمَا صَبَرُوا أَنَّهُمْ هُمُ الْفَائِزُونَ [المؤمنون: 111]

(Haqiqa ni na saka musu a yau saboda haqurinsu, haqiqa kuma su ne marabauta).

Kuma Allah ya kevanci masu haquri da godiya da amfanuwa da ayoyinsa inda don tantance su da wannan rabo mai girma, kuma gwaggwava, har sau huxu a gurare daban-daban. Allah Ya ce,

(إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآَيَاتٍ لِكُلِّ صَبَّارٍ شَكُور31)ٍ [لقمان: 31]

(Haqiqa game da wannan akwai ayoyi ga duk mai yawan haquri mai yawan godiya). Duba surorin Ibrahim da Saba’i da Luqman da kuma Shura, za ka ga hakan.

Ya bayin Allah! Ba wani abu ba ne haquri face hana kai raki, da hana harshe kokawa, da kuma hana gavvai make-make da kekketa sutura da makamantan haka.

Wani daga cikin nagartattun bayi ya ga wani mutum yana kai kukan matsalarsa ga xan uwansa, sai ya ce da shi “To ai kai ka kai qaran wanda zai tausaya maka gurin wanda ba zai tausaya maka ba”.

Wannan ya sa aka ce, Mai kai kukansa ga xan adam yana kai kukan mai jin qai ne (wato Allah) wajen wanda ba zai ji qansa ba.

Kai kuka iri biyu ne.

Na farko shi ne, kai kuka ga Allah. Wannan ba ya korewa bawa haquri. Kamar yadda Annabi Yaqub ya yi inda ya ce:

قَالَ إِنَّمَا أَشْكُو بَثِّي وَحُزْنِي إِلَى اللَّهِ وَأَعْلَمُ مِنَ اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ86) [يوسف: 86])

(Ni fa kawai ina bayyana takaicina ne da baqin cikina zuwa ga Allah. Kuma na san wani abu daga Allah wanda ku ba ku sani ba).

Duk da haka kuma ya ce:

(فَصَبْرٌ جَمِيلٌ18) [يوسف: ١٨].

(Na yi haquri kyakkyawa).

Na biyu shi ne, Wanda yake cikin wani bala’i ya riqa nuna damuwarsa da manganarsa ko da yanayinsa. Irin wannan salo ya savawa haquri, yana ma rushe shi.

Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wata kyauta mafi yalwa da alheri da aka bai wa wani bawa irin haquri”.

Shi haquri tamkar linzami ne ga zuciyar xan adam, da zarar aka rasa shi sai zuciya ta bazama.

Ya bayin Allah! Haquri kashi uku ne, duba da abubuwan da suka rataya da shi.

Haquri na farko shi ne, haquri a kan bin Allah, da aiwatar da umarninsa.

Haquri na biyu kuwa, shi ne haqurin barin abubuwan da ake hana na savo.

Haquri na uku kuma shi ne, haquri a kan abubuwan da Allah ya qaddara kuma ya hukuntawa bayi ta yadda bawa ba zai yi fushi da haka ba.

Sheikh Abdulqadir Jilani, Allah Ya yi masa rahama ya ce a cikin littafinsa Fathul Gaib: “Babu makawa ga bawa har sai ya zama mai aikata umarnin Allah, ya kuma nisanci haninsa, sannan ya yi haquri da hukuncin Allah”.

Da waxannan kashi uku na haquri, Luqman ya yi wa xansa wasicci ya ce:

(بُنَيَّ أَقِمِ الصَّلَاةَ وَأْمُرْ بِالْمَعْرُوفِ وَانْهَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَاصْبِرْ عَلَى مَا أَصَابَكَ إِنَّ ذَلِكَ مِنْ عَزْمِ الْأُمُورِ17) [لقمان: 17] (Ya xana ka tsayar da sallah, kuma ka yi umarni da kyakkyawan aiki, ko kuma hana mummunan aiki, kuma ka yi haquri bisa duk abin da ya same ka, lalle wannan yana daga cikin manyan abubuwa).

Wayayyen mumini ba ya fatan bala’i, sai dai yana haquri da shi idan ya afku. An karvo daga Abdullahi xan Abu Auf, Allah ya yarda da shi, ya ce: Haqiqa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku mutane kada ku yi fatan haxuwa da abokan gaba, ku roqi Allah zaman lafiya, sai dai idan kuka yi kicibis da abokan gaba to ku haquri, kuma ku sani haqiqa aljanna na qarqashin inuwar takubba”. (wato bayan wuya sai daxi).

Abubakar Siddiq, Allah ya yarda da shi ya ce: "Na fi son a qare ni da lafiya in gode fiye da a jarrabe ni da bala’i in yi haquri”.

Don haka fatan bala’i ba ya daga cikin koyarwar musulunci. Amma fa idan bala’in ya afku, haquri da shi ya zama dole. A kodayaushe al’amarin mumini alheri ne, ko daxi ko wuya, kamar yadda ya tabbata a cikin hadisi na Sahihi Muslim, daga Suhaibu xan Sinan ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mamakin al’amarin mumini, haqiqa duk al’amuransa alheri ne a gare shi, kuma babu wani wanda ya dace da haka sai dai muminin. Idan wani abin daxi ya same shi sai ya godewa Allah, hakan sai ya zamar masa alheri. Idan kuma wani abin qi ya same shi sai ya yi haquri, sai haqurin ya zama alheri gare shi".

Ya ‘yan uwa ku sani! Rayuwa dukkanta jarrabawa ce da gwaji. Allah Ya ce:

(وَنَبْلُوكُمْ بِالشَّرِّ وَالْخَيْرِ فِتْنَةً وَإِلَيْنَا تُرْجَعُونَ35) [الأنبياء: 35]

(Muna jarraba ku da fitinar sharri da ta alhri, kuma gare mu za a dawo da ku.)

Kuma ko da Allah yake jarrabar bayinsa yana jarrabarsu ne don sanin masu haqurinsu, da jarumansu, da kuma masu gaskiyarsu, daga waxanda ba haka ba. Allah ya ce:

(أَمْ حَسِبْتُمْ أَنْ تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَعْلَمِ اللَّهُ الَّذِينَ جَاهَدُوا مِنْكُمْ وَيَعْلَمَ الصَّابِرِينَ142) [آل عمران: 142]

(Ko kuna tsammanin za ku shiga aljanna ne tun gabanin Allah bai san waxanda suka yi jihadi a cikinku ba, kuma tun gabanin bai san masu haquri ba).

Kuma Allah ya ce:

(وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّى نَعْلَمَ الْمُجَاهِدِينَ مِنْكُمْ وَالصَّابِرِينَ وَنَبْلُوَ أَخْبَارَكُمْ31) [محمد: 31]

“Kuma haqiqa wallahi za mu jarrabe ku har sai mun san masu jihadi daga cikinku Mu kuma san masu haquri, kuma Mu jarraba ayyukanku a zantukanku”. Da dai sauran ayoyi masu kama da waxannan.

Har wa yau, yana daga ckin hikimar jarrabar bayi, sauqaqa musu hanyar samun shahada kamar yadda aya mai zuwa take sanar da haka:

(إِنْ يَمْسَسْكُمْ قَرْحٌ فَقَدْ مَسَّ الْقَوْمَ قَرْحٌ مِثْلُهُ وَتِلْكَ الْأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيْنَ النَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللَّهُ الَّذِينَ آَمَنُوا وَيَتَّخِذَ مِنْكُمْ شُهَدَاءَ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ140) [آل عمران: 140]

(Idan wani miki ya same ku, to haqiqa miki irinsa ya sami mutanen (a yaqin Badar), waxancan kwanaki muna jujjuya su ne a tsakanin mutane, don Allah ya san waxanda suka ba da gaskiya (daga cikinku) ya kuma sami shahidai daga gare ku. Allah kuwa ba ya son azzalumai. Kuma don Allah ya tsarkake waxanda suka ba da gaskiya, ya kuma hallakar da kafirai).

Kuma Allah maxaukakin sarki ya ce,

وَاعْلَمُوا أَنَّمَا أَمْوَالُكُمْ وَأَوْلَادُكُمْ فِتْنَةٌ وَأَنَّ اللَّهَ عِنْدَهُ أَجْرٌ عَظِيمٌ28) [الأنفال: 28]) (Haqiqa dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne, kuma a wurin Allah lada mai girma yake).

A nan nake cewa Allah ya gafarta min ni da ku da sauran musulmai, ku nemi gafarar Allah, lallai Shi mai yawan gafara ne mai yawan jinqai.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen manzanni Annabinmu Muhammad, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya, bayan haka:

Ya bayin Allah! Annabi (ﷺ) ya kasance yana rainon sahabbansa a kan yin haquri ta dukkan nau’o’insa. Kuma haka na bayyana a fili qarara, idan muka dubi irin zaman Annabi da sahabbansa a garin Makka. An karvo hadisi daga Khabbab Xan Aratt. Ya ce; Mun kaiwa Manzon Allah (ﷺ) kuka, yana mai ta da kansa da wani mayafinsa a inuwar Ka’aba. Sai muka ce masa, ba za ka nema mana taimakon Allah (a kan abokan gabarmu ba), ba ka yi mana addu’a ba. Sai ya ce tabbas cikin waxanda suka gabace ku a kan kama mutum a haqa rami a qasa a sa shi a ciki, sannan a zo da zarto a sa shi a kansa, a raba shi gida biyu, ko a riqa tsefe naman jikinsa da kum xin qarfe, amma duk da haka ba zai bar addininsa ba. Na rantse da Allah al’amarin wannan addini zai cika har matafiyi ya tafi zuwa Hadaramaut (cikin qasar Yaman), daga Sana’a' ba ya tsoron komai sai Allah. Sannan da fargabar kura ta far wa dabbobinsa. Sai dai ku kuna da gaggawa ne".

Abin nufi a nan, su yi haquri a kan addininsu, kamar yadda waxanda suka gabata suka yi haquri. Kuma da sannu azabar da kafirai suka yi musu za ta gushe.

Ya bayin Allah! Ta kowane hali mutum ba ya wadatuwa daga haquri, domin kuwa yana jujjuyawa ne tsaknin abin da ya wajaba ya yi, da wanda ya wajaba ya bari da kuma abin da aka qaddara masa mai gudanuwa a kansa kwatsam. Ga kuma ni’ima da ta zama dole ya godewa Allah a kanta. Idan kuma a kodayaushe bawa bai fita daga waxannan halaye haquri ya zamar masa dole har zuwa ranar mutuwa.

Hadisai da maganganun magabata a kan falalar haquri suna da yawa. Ga kaxan daga ciki:

An karvo daga Ummu salama ta ce na ji manzon Allah tsira da amincin Allah yana cewa: “Babu wani musulmi da wata masifa za ta same shi sai ya faxi abinda Allah ya umarce shi da shi: “Daga Allah muke, kuma ga Allah za mu koma, ya Allah ka ba ni ladan jarrabata kuma ka maye min da abin da ya fi ta. Face sai Allah ya maye masa da abin da ya fi ta.

Ummu salamah ta ce, yayin da Abu Salamah (mijinta) ya rasu sai na ce wane Musulmi ne ya fi Abu Salamah, gida na farko da suka yi qaura zuwa ga Manzon Allah, sannan duk da haka sai na faxa, sai Allah ya musanya mini da Manzon Allah.

An karvo daga Abu Huraira, ya ce; haqiqa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda Allah yake nufinsa da alheri, sai ya jarrabe shi.

An karvo daga A’isha Allah ya yarda da ita ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wata musiba da za ta sami mumini face sai Allah ya kankare masa laifukansa ta dallilinta hatta daidai da qaya idan ya taka".

Ya xan’uwa mulumi! Ka yi haquri da maqoci, ka yi masa alheri, kuma ka daurewa cutarwarsa. Bayan haka ka yi haquri da wanda yake qarqashinka. Sannan dole sa an yi haquri da iyali, don haka ka yi haquri da matarka a kan kurakuranta.

Ya ‘yar’uwa, ke ma sai kin yi haquri da mijinki. Shugaba ma sai ya yi haquri da waxanda yake shuganbata. A dunqule dai haquri ya zama dole ga dukkan mutane. Wanda ya yi haquri zai haxu da alheri mai xinbin yawa, wanda kuma ya rasa haquri to haqiqa ya rasa alheri mai tarin yawa.

Ina roqon Allah dacewa gare ni da ku gaba xaya, tare da neman taimakonsa a kan dukkan alheri, domin shi mai cikakken iko ne a kan kowane abu.