islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Tasirin Laifuka A Rayuwar Dan Adam


7707
Surantawa
Haqiqa laifuka da xan Amda yake yi, da savon Allah, dare da rana, suna rugurguza rayuwar xan Adam, saboda tsayuwar rayuwa da ingancinta, ya dogara ne kacokam a kan biyayya ga Allah da daidaito a kan al’amarinsa, da kuma lazimtar shari’arsa. Duk wanda ya karkace wa addinin Allah, duk wanda ya bi Shaixan, to yana bin abin da ba shi da tabbas ne, yana bin abin da zai jawo masa takaici, musamman yayin da zai haxu da Ubangijinsa.

Manufofin huxubar

Bayanin haxarin da ke tattare da sovon Allah.

Jan-kunne game da savon Allah.

Dasa tsoron Allah a zukata.

Kwaxaitarwa a kan tuba.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Ku sani, laifuka da xan Amda yake yi, da savon Allah, dare da rana, suna rugurguza rayuwar xan Adam, saboda tsayuwar rayuwa da ingancinta, ya dogara ne kacokam a kan biyayya ga Allah da daidaito a kan al’amarinsa, da kuma lazimtar shari’arsa. Duk wanda ya karkace wa addinin Allah, duk wanda ya bi Shaixan, to yana bin abin da ba shi da tabbas ne, yana bin abin da zai jawo masa takaici, musamman yayin da zai haxu da Ubangijinsa. Allah yana cewa,

( فَبِمَا نَقْضِهِمْ مِيثَاقَهُمْ لَعَنَّاهُمْ وَجَعَلْنَا قُلُوبَهُمْ قَاسِيَةً يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَنْ مَوَاضِعِهِ وَنَسُوا حَظًّا مِمَّا ذُكِّرُوا بِهِ وَلَا تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَى خَائِنَةٍ مِنْهُمْ إِلَّا قَلِيلًا مِنْهُمْ فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاصْفَحْ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ 13 ) [المائدة: 13]

. (Saboda warware alqawarinsu da suka yi, sai muka tsine musu, muka sanya zukatansu suke qeqashe, suna sauya kalmomi daga gurabensu, kuma sun manta wani rabo daga cikin abin da aka yi musu wa’azi da shi. Ba za ka gushe ba kana tsinkaye a kan wani ha’inci daga gare su, sai kaxan daga cikinsu. Ka yafe musu, ka kuma kawar da kai, Allah yana son masu kyautatawa).

Kuma Allah ya ce,

( كَلَّا بَلْ رَانَ عَلَى قُلُوبِهِمْ مَا كَانُوا يَكْسِبُونَ 14 ) [المطففين: 14].

“Bari dai, abin da suka kasance suna aikatawa, ya yi tsatsa a cikin zuciyarsu.”

Kuma Allah yana cewa,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا إِنْ تَتَّقُوا اللَّهَ يَجْعَلْ لَكُمْ فُرْقَانًا وَيُكَفِّرْ عَنْكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ 29 ) [الأنفال: 29]

(Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka ji tsoron Allah, zai sanya muku mararraba, kuma ya kankare muku daga zunubanku, kuma ya gafarta muku. Lalle Allah ma’abocin falala ne mai girma).

Lallai savon Allah yana gadar wa xan Adam qunci da rashin jin daxin rayuwa, kamar yadda Allah yake cewa,

( وَمَنْ أَعْرَضَ عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنْكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى 124 قَالَ رَبِّ لِمَ حَشَرْتَنِي أَعْمَى وَقَدْ كُنْتُ بَصِيرًا125قَالَ كَذَلِكَ أَتَتْكَ آَيَاتُنَا فَنَسِيتَهَا وَكَذَلِكَ الْيَوْمَ تُنْسَى 126 وَكَذَلِكَ نَجْزِي مَنْ أَسْرَفَ وَلَمْ يُؤْمِنْ بِآَيَاتِ رَبِّهِ وَلَعَذَابُ الْآَخِرَةِ أَشَدُّ وَأَبْقَى 127 ) [طه:124 - 127]

.

(Duk wanda ya bijirewa ambato na, to rayuwar qunci ta tabbata gare shi, kuma za mu tashe shi ranar alqiyama, makaho. Sai ya ce, “Ya Ubangiji! Mai ya sa ka tashe ni makaho, alhali na kasance mai idanu” Sai ya ce, “Haka nan ne ayoyinmu suka zo maka, sai ka qyale su, kai ma yau haka za a qyale ka. Kamar haka ne muke saka wa wanda ya wuce gona da iri, bai ba da gaskiya ga ayoyin Ubangijinsa ba. Azabar lahira ta fi tsanani da wanzuwa).

Lallai ‘yan uwa, mu sani, yana daga cikin illar laifuka mafi haxari, kewa da suke sawa tsakanin bawa da Ubangijinsa. Sai ka ga, xa’a da biyayyar Allah suna yi masa nauyi, amma kuma yana jin daxin savon Allah, kuma ya saba da savon Allah, savo ba ya yi masa wahala. Wannan wace irin makanta ce? Allah ya kiyashe mu!

Ya ku ‘yan uwa musulmi! Ku sani, rayuwa ingantacciya, ita ce rayuwar da ake yi wa Allah biyayya a cikinta, rayuwar da za ta mayar da mutum bawa ga Allah shi kaxai, ta kuma mayar da shi xa ‘yantacce ga duk wani abu da ba Allah ba. Huzaifa ya ce, na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, “Za a bijiro da fitinu a kan zukata, kamar tabarma. Duk zuciyar da fitina ta ratsa cikinta, sai a yi xigo baqi a cikinta, duk zuciyar da ta yi inkarin sa, sai a yi xigo fari a cikinta, har sai sun koma zuciya iri biyu: Xaya fari fat, kamar wani falalen dutse, fitina ba za ta cutar da ita ba har abada. Xayar kuwa ta zamo baqa qirin, ba ta san ma’arufi ba, ba ta inkarin munkari ba, sai abin da son zuciya ya gaya mata.”

An karvo daga Abdullahi bn Umar ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ya ku gungun muhajirai! Abubuwa guda biyar, idan aka jarrabe ku da su, suka sauka a cikinku, ina neman tsari da Allah, ku riske su: Alfasha ba ta tava bayyana a cikin wasu mutane ba, suna aikata ta, face sai annoba ta bayyana a cikinsu, da cututtuka irin waxanda magabatansu ba su san su ba; kuma mutane ba su tava tauye mudu da sikeli ba, face sai an jarrabe su da fari, da tsananin rayuwa, da zaluncin shugabanni; babu mutanen da za su hana zakka, face sai an hana su ruwa daga sama, ba don saboda dabbobi ba, da ba za a yi musu ruwa ba; ba wanda za su warware alqawarin Allah, da alqawarin Manzonsa, face sai Allah ya xora abokin gabansu a kansu, su karve wani abu daga cikin abin da yake hannunsu; matuqar kuma shugabanninsu ba su amfani da littafin Allah ba, sai Allah ya jefa tsanani a tsakaninsu.” [Hakim ne ya rawaito shi]

Don wannan ita ce qa’idar Allah, kamar yadda yake cewa,

( وَاتَّقُوا فِتْنَةً لَا تُصِيبَنَّ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْكُمْ خَاصَّةً وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ 25 ) [الأنفال: 25]

(Ku ji tsoron fitina, wadda ba za ta shafi waxanda suka yi zalunci ba daga cikinku kawai. Ku sani, Allah mai tsananin uquba ne).

Haka ya zo a cikin hadisi, Zainab bint Jahsh ta ce, “Shin za a halaka mu, alhali akwai mutanen qwarai?” Sai ya ce, “Idan vata-gari suka yi yawa!” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

An karvo daga Huzaifa ibn Yaman, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Na rantse da wanda raina yake hannunsa, lallai ko ku yi umarni da kyakkyawa, ku yi hani kan mummuna, ko kuma lallai Allah ya kusa ya aiko muku da uquba daga gare shi, sannan ku yi ta roqon sa, ba zai amsa muku ba.” Tirmizi ne ya ruwaito shi.

Ya ku musulmai! Me ya nutsar da Fir’auna? Me ya halakar da adawa da samudawa da mutanen Annabi Luxu, da Qaruna da Hamana, da ma jama’a masu yawa? Abin da ya halakar da su shi ne savon Allah. Allah yana cewa,

( وَعَادًا وَثَمُودَ وَقَدْ تَبَيَّنَ لَكُمْ مِنْ مَسَاكِنِهِمْ وَزَيَّنَ لَهُمَ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَكَانُوا مُسْتَبْصِرِينَ38وَقَارُونَ وَفِرْعَوْنَ وَهَامَانَ وَلَقَدْ جَاءَهُمْ مُوسَى بِالْبَيِّنَاتِ فَاسْتَكْبَرُوا فِي الْأَرْضِ وَمَا كَانُوا سَابِقِينَ39 فَكُلًّا أَخَذْنَا بِذَنْبِهِ فَمِنْهُمْ مَنْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِ حَاصِبًا وَمِنْهُمْ مَنْ أَخَذَتْهُ الصَّيْحَةُ وَمِنْهُمْ مَنْ خَسَفْنَا بِهِ الْأَرْضَ وَمِنْهُمْ مَنْ أَغْرَقْنَا وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَكِنْ كَانُوا أَنْفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ 40 ) [العنكبوت:38 - 40].

(Da adawa da samudawa, wani abu daga cikin matsugunansu ya bayyana gare ku. Shaixan ya qawata musu ayyukansu, sai ya kare su daga bin tafarkin Allah, alhali suna gani, da Qaruna da Fir’auna da Hamana, haqiqa Annabi Musa ya zo musu da ayoyi bayyanannu, sai suka yi girman kai a doron qasa, kuma ba su zamo masu tsere mana ba. Kowanne mun damqe shi saboda laifinsa: Daga cikinsu akwai waxanda muka aika wa mahaukaciyar iska wadda take qunshe da tsakuwowi; daga cikinsu akwai wanda tsawa ta kama su; daga cikinsu akwai wanda muka shafe qasa da su; daga cikinsu akwai waxanda muka nutsar. Bai cancanta Allah ya zalunce su ba, sai dai kansu suka kasance suna zalunta).

Huxuba Ta Biyu

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, mai kowa mai komai, mai iko a kan dukkan komai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin tsira Annabin rahma Muhammad xan Abdullah da alyensa masu tsarki, da sahabbansa yardaddu a gurin Allah. Da duk wanda suka bi tafarkinsu na gaskiya har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:

Ya ku ‘yan uwa Musulmi! Duk wanda yake son tsira a duniya da lahira, to ya lazimci yin biyayya ga Allah da Manzonsa. Allah yana cewa,

( وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا 71 ) [الأحزاب: 71].

(Duk wanda ya yi biyayya ga Allah da Manzonsa, haqiqa ya rabauta, rabauta mai girma).

Ku sani ya ‘yan uwa, yana daga cikin abin da zai tseratar da ku daga azabar Allah, umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, kamar yadda hadisi ya nuna a baya.

Kuma wajibi ne a kan shugabanni su tsayar da haddi a kan duk wani wanda ya keta haddi, domin da yin haka ne za su sami yardar Allah.

Kuma ku yawaita tuba zuwa ga Allah. Allah yana cewa,

( وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَا الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ 31 ) [النور: 31]

.

(Ku tuba zuwa ga Allah gabaxayanku ya ku muminai. Lalle za ku samu rabuta).

Yana kuma cewa,

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا تُوبُوا إِلَى اللَّهِ تَوْبَةً نَصُوحًا ) [التحريم: 8]

(ya ku waxanda suka yi imani, ku yi tuba ta gaskiya zuwa ga Allah).

Anas ya rawaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) yana tuba sau saba’in a yini guda. [Bukhari].

Tuba ta gaskiya it ace wadda ta cika sharuxan da malamai suka faxa guda huxu. Sharuxan su ne: Yin nadama a kan abin da ya wuce, da quduri kan ba zai sake aikata laifin ba a sauran rayuwarsa, kuma ya daina savon, idan a lokacin yana yin sa. Idan kuwa laifin ya shafi bayi ne cikin haqqoqinsu, to sai ya biya su, ko ya nemi yafiyarsu. Sharaxi na qarshe, ya tuba a lokacin da lokacin tuba ne, kafin ya sharafa, ko kuwa rana ta fito daga yamma. Allah ya datar da mu!

Ya Allah kai ne mai jujjuya zukata, ka tabbatar da zuciyarmu a kan addininka. Allah ka shiryar da mu ga mafi kyan halaye, babu wanda yake shiryar wa ga ma fi kyan halaye sai kai. Kuma ka raba mu da miyagun halaye, babu mai raba mutum da miyagun halaye sai kai. Ya Allah ka taimaka mana bisa ga ambatonka, da gode maka da kyautata bauta gareka. Ya Ubangijinmu kada ka karkatar da zukatanmu bayan ka shiryar da mu, kuma ka ba mu wata rahama daga wajenka. Lalle kai mai yawan kyauta ne.